KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Da misalin karfe biyar na yamma ya fito daga d’akinsa cikin shirin fita riga da wando red and ash ne sanye ajikinsa ,
kafafunsa sanye cikin takalmi canvers Ash me ratsin red ta gefe da gefensa , hannunsa d’aure da agogon fata mai kyau da tsada yayinda kwantaccen sumar Kansa ya sha gyara ya kwanta luf luf Hakan ya karawa fuskarsa kyau da annuri sai dai fuskar a hade take babu alamun fara’a ko kad’an ,key din motarsa ferari ne rike a hannunsa Kai tsaye d’akin da tanweer take ya kutsa ya shiga bakinsa d’auke da sallama sai da aciki yayi ,kamshin turarensa daya saba amfanin dashi ne ya doki hancinta ta d’ago a natse ta tsura masa idanunta kamar Koda yaushe fuskar nan tashi babu wadataccen fara’a, muryarta a sanyaye ta motsa labbanta”Ina yini ?”bai amsa mata ba sai ma wani kallon banza daya bita dashi kafin ya d’auke kanshi daga kallonta ya nufi Inda bedside yake ya bude.
bata damu ba dan tasan dole zuciyarsa ta d’auki fushi daita sakamakon abinda tayi masa jiya wasu file ya ciro yana dubawa ya d’auki minti biyar yana tsaye yana dubawa sannan ya mayar ya ajiye ya juya ya fita ya nufi parlour yana taku a hankali kamar bai son taka kasa har sanda ya fito parlour’nsa .
Gbdy abokansa suna zaune kamil nacin abinci ,yayinda jubi ke k’okarin nada tabar wiwi , kunnen anas manne da waya yana ganinsa ya mike tsaye da sauri yana binsa da kallo .
Shima jaguwa Tsura masa Ido yayi yana karanta yanayin wayar da yake , anas ya karasa sosai kusa dashi ya rike masa hannu yana cewa “tanko gote ne wai yana da alqalla me kyau da yake son muyi masa ya kira layinka ba baka d’auka ba shine ya kirani kayi magana dashi ya mika masa wayar . “bazan yi magana dashi ba kaima karka sake d’aukar wayarsa sanin kanka ne anas bama Kulla alqalla da irinsu tanko gote mutumin da nake fatan a karshen rayuwarsa ya zamo mabaraci akan titi ya numfasa sannan ya cigaba da magana a sanyaye ” ka kula da kyau anas banason wani abu ya sameka idan wani abu ya sameka bazan yafe maka ba “.duk maganar jaguwa d’aya byn d’aya suke shiga kunnen tanko gote ya runtse idanunshi tare da disconnecting din kira.”

” Inshallahu zan kular maka da kaina Ina zuwa haka ga abinci anyi order da Kai ? numfashi ya fesar yana yamutsa fuska kafin yace “zanje ganin ahlina idan naje can zanci zan dan d’auki lokaci ban dawo ba dan zan fara da biyawa gidan marayu akwai sakon da zan Kai musu yana gama fad’ar haka ya zare hannunsa ya juya ya fice daga parlour’n dan yasan yanzu raunin anas zai bayyana .
ilai kuwa hakan ce ta kasance gbdy yanayin anas ya canza rauninsa ya bayyana kamar zai yi kuka ,ya danne hawayensa suka koma, a duk sanda yaga jaguwa za shi ga ahlinsa sai yaji zuciyarsa tayi rauni saboda rasa nashi ahlin da yayi bashi da kowa a halin yanzu sai jaguwa shine komai nashi zama yayi ya shiga duniyar tunani .Kai tsaye Inda motarsa ferari yake ya nufa ya danna keyn hannunsa ya bud’e ya shiga ya zauna yana me kunna motar tare da yin hon me gadi ya wangalemasa get din gidan ya fice.

tafiyar awa d’aya ce ta kawoshi gidan marayu babus’salam dake ikeja gra yayi hon aka bud’e masa get ya shiga, yasa guri ya
yi parking din motarsa ya fito ya bud’e bayan boot dinsa ya ciro bakar jaka dake shake da kudi ya kulle motar Kai tsaye office din shugaban makarantar ya nufa .malam yusif na ganinsa ya fad’ad’a fuskarsa da murmushin jin dadi dan yawon zuwan jaguwa yasa sabo me karfi ya shiga tsakaninsu ,ya nuna masa gurin zama byn jaguwa ya zauna ya mika masa hannunsa suka gaisa “yalla’bai barka da zuwa ya aiki da k’okari ? “alhamdulillah ya naku k’okarin da fama da yara ? malam yusif yayi murmushi kawai ,sun dan ta’ba hirar duniya sannan jaguwa ya mika masa jakar kudin daya zo dashi “ga wadan nan kudaden ayi wa marayu hidima dasu.
“Kai masha Allah ,Allah yasa Saka da alkhairi ,Allah yasa maka ladan a mizani ,yadda kake faranta zukatan marayu Allah ya faranta naka , Allah ya kawo farinciki a rayuwarka data iyalinka, Allah ya tsareka”. “Ameen na gode sosai da addua ni zan wuce har ya juya malam yasif yace “yalla’bai har yau baka fad’a min sunanka ba gashi za’a Saka cikin sunayen masu tallafawa marayu “ya juyo a natse yana cewa”bana bukatar a Saka suna , sukayi sallama ya wuce ya d’auki hanya zuwa unguwarsu ko gama daidaita parking din motarsa bai yi ba Jamar’sa na unguwar suka zagaye motarsa tare da Kawo masa gaisuwa.
a natse ya fito yana ƙoƙarin kulle motar byn ya kulle ya mika musu hannunsa d’aya bayan suka gaisa ya Ciro kudi masu yawa ya shiga raba musu me dubu biyar me dubu goma cike da murna suka dinga masa addua shi km yana amsawa da Ameen sannan ya sa Kai zuwa cikin gidansu.

yana shiga gidan ya hargitse da murnar ganinsa ya samu guri ya zauna akan kujera me zaman mutun biyu idanunshi na kan fuskar amminsa dake zaune fuskarta d’auke da annurin ganinsa duk cikin ya’yanta tafi qaunarsa saboda tausayin dake garesa, yana qaunarta da qaunar kannensa ,yana tausaya musu, duk abinda suke so zai musu batare da bata lokaci ba shine komai nasu ita da yaranta.
kannensa suka durkusa har
suka gaishesa ,bayan sun gaishesa kowacce ta samu guri ta zauna akan hannun kujerar da yake zaune.
yayi murmushi kana ya dan zamo ya gaishe da mahaifiyarsa “ammi Ina yini ?Lafiya lau ya gida ya fama da aiki ?
“alhamdulillah ammina ya fad’a tare da juyowa ya Kalli hally “Ina sadiq ko ya fita aiki ne ?bai fita ba father yana gida yanzu nan ya fita raka ya marwan bata qarasa rufe bakinta ba sai gashi ya shigo fuskarsa da murmushi dan tun daya ga motarsa a kofar gida yasan yazo ya gaishesa yana tmbyr me jiki jaguwa ya waske tamkar ba dashi yake magana ba.
ammi taso ta tambayesa abinda ya faru dashi jiya amman ganin Babu damuwa atare dashi sai zallar farinciki yasa ta kame bakinta sadiq ya samu guri ya zauna a gefen ammi yana sake tmbyrsa tanweer , ammi ta gyara zamanta tana cewa wacece babu Lafiya ne ?”budurwarsa ce ammi “ya fad’a cikin tsigar zolaya Jin haka yasa jaguwa ya waigo ya watsa masa katuwar harara “Kai haba sadiq yanzu daman yayanka yana da budurwa baka ta’ba fad’a min ba ? lallai kayi min laifi me girma zaka fuskanci hukunci ? Tayi mgnr kmr Adnan ba dan farinta bane, ta rasa dalilin da soyayyar dan nata yake hana kunyarta tasiri idan tagansa neman kunyar take ta rasa “Allah ammi Nima ban dade da sani ba “oh nace dai ta Kalli jaguwa banda abunka ai sai kayi magana a tura gidansu ba sai a had’a dana shafiqa ba a wuce gurin” .

jaguwa ya sake watsawa sadiq harara yana cewa “Allah ammi karki amince da maganarsa ba budurwata bace taimako nayi “taimako! ?ta tmbyesa tana tsura masa idanunta domin gano gaskiyar dake zuciyarsa ,ya gyada mata Kai alamun “eh “.
to ai shikenan idan dai har ka bata lokaci Allah auren dole zan maka na huta da wannan shan kamshin da kakewa aure ta k’arasa maganar tana cewa shafiqa “jeki zubowa yayanki abinci da sauri ta mike ta fita ko cikakken minti biyu batayi ba ta shigo rike da plet ,hally ta mike ta janyo karamin stood gabansa shafiqa ta ajiye abinci tare da bude masa cike da farinciki suka dinga Ina na Saka Ina ajiye da yayansu kowannensu na kokarin faranta masa, cike da matsanacin farinciki da soyayya jaguwa ya kai loman shikafa da miya bakinsa ya ajiye spoon shima sadiq ya matso ya d’auki spoon din da jaguwa yayi amfani dashi ya Kai bakinsa ,ya ajiye spoon jaguwa ya sake d’auka Sadiq yace “gsky father ya dace yadda kayi kyau din nan na rakaka gurin yarinyar nan zance Allah Kun dace ban ta’ba ganin mutanen da suka dace da junansu ba kmar ku ba ……”jaguwa ya wani kallesa shekeke yana cewa menene Kuma zance ? yayi mgnr tare da ajiye spoon din hannunsa ya d’auki tissue yana goge bakinsa “haba father karka waske mana ni dai dan Allah ka auri yarinyar nan wallahi tayi min “na fika sanin tayi aurenta ne dai bazan yi ba kwarya tabi kwarya ya fad’a a zuciyarsa .
“kasan Allah Sadiq yayanka Adnan yafi karfin zuwa wani zance ko menene kace sunansa Allah dai ya tsareni da …”wani kallo da ammi tayi masa yasa shi katse abinda zai ce ya yamutsa fuska yana lumshewa ammi Idanunshi “duk kagama cika bakinka Muna nan zaka zo kayi auren ai duk dan sunan dole zai so aure “Allah ammi ko zanyi aure bazan je wani zance ba wannan zuwa zance fa kauyanci ne ” agurinka ba me ra’ayin rikau amman meye na kauyanci aciki ?”
Allah ammin bayan kauyanci har da lalata Yara yake shi yasa kikaga bana son yaran nan nayi zance “a’a ban yarda da mgnrka ba zance baya wani lalata yaro sai dai can yaron dan iska ne Amman irin zance da shafiq ke yi taya yaro zai lalace a parlour’n nan suke zama gashi mutane ma na Kai kawo Kai dai ka Maida hankali ka tsaida matar aure ,
ni jikina ma ya fara bani lokaci yayi “.sadiq yayi tsigil yace “sosai ma kuwa ammi sai ma Kinga yarinyar dana ganshi daita Allah cewa zakiyi ya aureta kawai “Nan fa hirar ta juye zuwa ta aure jaguwa ya wani shagwa’be fuska kamar karamin yaro yace “ni dan Allah ka rabani da zance aure nan ,nifa auren nan ban ta’ba Jin zanyisa nan kusa ba Kuma ma idan zanyi zanyi ne dan ya zama sunnah da faranta ran ammi Kuma ko zanyi sai na nemo wacce zatayi hakurin zama dani ba wacce zan dinga rage murya ba Ina kaskantar da kaina ba, kasan fa mata idan suka ga ka damu dasu sai salo da iskanci ya tashi babu ma abinda ke bani takaici kmr kaga katon nmj a gaban karamar yarinya yana rage murya da kaskantar da Kai wai duk akan a amsa masa soyayyarsa Kai Allah bazan iya ba ni kawai idan ma ya zama dole Allah umarni kawai zan bata tunda ya fara mgn sadiq da kannensa mata har ma da ammi suke dariya.
Shi kuwa jaguwa yayi dip kmr anyi ruwa an d’auke ,duk yadda sadiq ya so acigaba da mgnr tanweer jaguwa yaki sai ma ya kawar da hirar ya shiga tmbyrsu abinda basu dashi a gida anan yayi sallahr magrib da isha’i
Hira sukayi sosai har lokaci yaja ya duba agogon hannuna karfe shadaya saura ya mike yayiwa ammi sallama byn ya ajiye mata bandir din kudi yan dari biyu biyu suka fita tare da sadiq domin yi masa rakiya ya shiga motarsa ya kunnata ya bata wuta sai da sadiq yaga tashinsa sannan ya koma gida ya rufe .
Koda ya koma gida bai bi ta kan kowa ba har ma tanweer ya shareta ,ita Kuwa idanunta shi suke son gani ta sake neman afuwansa amman yaki shigowa Inda take ranar da kyar ta runtsa kwana tayi juyi da kuka .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button