KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“ kiyi hakuri banason ganin tanwer cikin wahala ne duk abinda zai sameta dole ya sameni nan hawaye ya soma gangaro mata ba kakkautawa murya kasa kasa tace “kayi musu fatan alkhairi babu abinda ya gagari allah wannan auren idan ba alkhairi bane allah ya dakatar dashi idan kuma alkhairi ne fa ?
”inshaallahu ma bazai tabbata ba kawai ni abinda nake so dake ki tsaya a bazaa yi ba, Kiyi min wannan alkwarin “gaskiya bazanyi ba tana gama fadar haka ta mike ta dauki wayarta ta fito ta bar masa dakin babu kowa a falon sai tv dake aiki da ac ta soma tafiya a hankali tana karewa falon kallo har ta isa kofar dakin dake kallon nata wanda suke saukar baki ciki ta soma neman layin uncle bashir kira daya ya dauka cike da girmamawa tace ya hau online haka ma uncle jamil shi daman soja kullum yana online da wahala ka hau baka sameshi ba conference ta hadasu a vedio call kowannensu yana kallon danuwansa “na kiraku ne akan matsalar tanwer da wannan yaron adnan ,bashir ina ganin lokaci yayi da zan dauki shawararka na amince tanwer ta aure shi amman kai jamil da Aliyu me kuka gani akai ?”nan take uncle jamil yace “minister ya yarda da hakan ne ? ta sauke numfashi da karfi “bai yarda ba gskiya.
Yayi min daidai gsky nima ban goyo baya ba kai yaya saboda me zaka bata wannan shawarar ?” Wannan ai abun kunya ne da torzarci gsky karki amince aunty sam sam wannan shawarar batay ba mu dai san yadda zamu nisanta tsakaninsu idan garin zaa mu bari daita zuwa wata kasar to adai san yadda zaayi.”
“Shikenan kai Aliyu fa me zaka ce ?
“Ni dai gsky na yarda ta auresa idan dai har adnan din dana sani ne lallai zai rike miki ita da gaskiya wallahi adnan din danasani me kirki ne dasanin yakamata…”kai dan allah malam ka rufewa mutane baki maganar riko akeyi ko sanin yakamata ?” ya katse shi ta hanyar fadar haka “ana magana ne akan sana’arsa duk kirkinsa tunda bashi da hali ai na banza ne “ni kaina banason auren nan jamil amman da ta dinga binsa suna aikata zina suna ciki ana cirewa me zai hana mu taimaka masa tunda muna da halin yin haka “ kayi hakuri kaji kanina nasani abun akwai ciwo amman ya zamuyi da qaddara?ta karasa maganar tana zubar da hawaye nan fa duk suka rude suka shiga rarrashinta “ban taba tsamanin rayuwarta zata dawo haka ba tanwer da kanta ke binsa kuma nasan da wahala su hadu wani abu bai shiga tsakaninsu ba ,nasan tanwer nasan yanayinta sai dai kawai na share dan yin maganar bashi da amfani sun dan dade suna tautaunawa a karshe dai dole jamil ya sadaukar ya hakura suka amince akan ta auresa wannan yasa mumy taji kwarin gwiwa suka sallama ta fito ta nufi dakin tnwer ta murda handle ta kusa cikin dakin alokacin tanwer tayi zurfi cikin tunani .”

ta zauna kusa daita tana shafa sumar kanta a dan firgice ta waigo suka hada ido daita mumy ta sakar mata murmushi itama tanwer murmushi ta sakar mata mai hade da kuka “na amince da zabinki tanweer ,na amince ki auri adnan kice masa ya turo iyayensa ..”tanweer tayi tsuru tana duban mumy tana jin mgnrta kmr a mafarki  kafin daga baya ta mintsini fatan jikinta  domin ta tabbatar da mafarki take ko kuwa gaske ne abinda taji mumy ta  fada .
“tunda kin amince kina son Adnan kice masa ya turo magabantansa suyi magana da mahaifinki karasa mgnr hawaye na zubawa daga kwarnin idanunta .”allah yasa yayi miki adalci tanwer amman kiyi min alkawari zaki yaki sanarsa kafin aurenku “nayi miki alkwari mumy .”
zuciyarta  tanweer sol da jin abinda mumy tace nan take ta sauko ta durkusa kasa gabanta  tana kwalla tace “na gode mumy Kuma Ina Kara baku hakuri dan Allah ku yafe min  Mumy ta share hawaye tana cewa  “ai ya wuce tanweer amman kibi a hankali banason ki Kara zuwa inda  yake  kice masa ya dinga zuwa , hawayen farinciki ta dinga zubawa muryarta a sanyaye tace “mumy dady ya amince ne ?
Naunayen ajiyar zuciya mumy ta sauke tare da cewa “eh yanzu nayi masa magana ya kuma amince tana gama fadar haka ta mike ta fita  .”
Tana fita tanweer ta soma neman layin jaguwa amman wayarsa bata shiga ,  dole ta hakura ta fito da gudu ta  nufi d’akin rukayya tana shiga ta kamo hannunwata duka cikin nata ta  fara juyi daita acikin d’akin tana cewa”yau dai naga amfani addua ruky mumy da dady sun amince na auri Adnan rukayya ta kamota ta zaunar  daita  “Kai amman na tayaki  murna Allah ya tabbatar da alkhairi rukayya tasan tanweer nason adnan sosai amman batasan dan fashi bane daga mahaifinta sai mahaifiyarta da kannenata da alhj Usman ne suka san da wannan maganar washegari da farinciki ta tashi ta tafi aiki hatta maaikatanta sun fahimci halin da take ciki na samun sukuni sai dai babu wanda yasan abinda ya jefata cikin farinciki a office dinta ma a qalla ta kusan minti talatin tana neman layinsa ko dan tayi masa albishiri amman bata samu ba haka har washegari numbersa kawai take kira but no answer a lokacin shi jaguwa yana kan wani aiki daman kuma idan yana kan aiki bai kunna wayoyinsa har  sai ya kammala abinda dake gabansa sannan ya kunna waya .”


Karfe goma na safiya anas bai yi shirin fita ba kamar yadda ya saba sai kallon dayasa gaba yanayi sosai hankalinsa yana kan film din dan ko motsin kirki bayayi hally wacce ta fito ta zauna kusa dashi more than 30 minutes ta rasa mai yake gani aciki har ya dauki hankalinsa ta dai kara arawa kanta lokaci ta cigaba da zama tana bin katuwar flazma din da kallo tana karanta translation din tana fuskantar film din amman sam bata gano wata maana da zata saka mutun ya dauke hankalinsa kacokan akan film din ba .”
Ya dan gyara zamansa lokacin da yarinyar cikin film din ta fito daga cikin ruwa kayan jikinta sun manne ajikinta surarta ta bayyana sosai ta dan saci kallonsa cikin kunyar data shigeta na ganin wannan yarinyar wani murmushi tagani a fuskarshi ji tayi zuciyarta ta buga nan take ta hade rai “wai meye amfanin wannan kallon da kake ina ganin gara kayi abinda ya dace ?” .ya waigo ya kalleta ya kawar da kanshi yana karantar abinda ya bata mata rai ya dauki remut yayi rewarning ya dawo baya kadan daidai inda yarinyar ta fito daga ruwa ya tsaya ya cigaba da kalla har aka dauke gurin sannan ya dawo da idanunshi kanta bai damu da cikar da take tana batsewa ba dan daman da biyu ya sako film din ya cigaba da kallonsa ganin haka ta tashi tsam ta koma dakinta ta kwanta wani takaici ya ziyarceta damuwar da batayi zato akan anas ba ta dabaibayeta wannan shine kishi itama ta fuskanci hakan amman bata san hanyar da zata kawar da kishin nashi ba .”

Bata jima da kwanciya ba ta tashi da niyyar ta leka domin ganin ko har lokaci yana zaune a hankali ta bude kofar ta turo da kanta waje nan ta fara jiyo tahowarsa sosai suka hada ido dashi kuma tasan ya ganta da sauri ta koma cikin dakin shiru bai shigo ba kunya kuma sai ta hanata sake yunkurin fitowa amman a yanzu kunyarsa da take ji bazata kaita ga hanata kawo abinda zai kawo masa farincikiba .
Dan haka ta daure ta fito parlour alokacin ya gama kallon ya mike akan doguwar kujera da “alamun yau dai babu inda zashi domin ko wanka baiyi ba ta zauna kusa da kujerar da yake kwance ta dube shi anatse “amman dai yau babu inda zaka ?ta fada tana kallonsa kamar ba zai yi magana ba daga bisani ya dago kai “me kikagani? Ya dawo mata da tmbyr ta dan dauke kanta daga kallonsa saboda kasa jure hada ido dashi tace” aa kawai dai na ganka ne kwance baka da alamun fita “mai zai hanani fita tunda zaman gidan ba wani abu zai amfanar min dashi ba kiran yayanki kawai nake jira na kama gabana “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button