KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48


Kwance tashi ba wuya agurin Allah kullum bikin shafiq da gali na Kara matsowa har yau sauran kwana bakwai Sadiq ne yayi rabon IV duk Inda ya dace ya Kai jaguwa kuwa tun satin Biki ya ajiye komai da za’a ci a Sha , yanuwa da abokan arziki na nesa dana kusa duk sun hallara Kowa ka gani farinciki  yake har  jaguwa sai dai Idan ya tuna shima ana daf da saka nashi ranar   da hasera hankalinsa sai ya   tashi shrye shirye yayi nisa har yau friday akayi kamu amarya anan unguwarsu bakaramin kudi jaguwa ya kashe ba, anyi biki na yar gata domin a hall akayi , mata kuwa Kamar zasu cinyesa duk inda yayi idanunsa na kanshi .
bayan an gama biki hakan nan zuciyarsa ta umarcesa ya sake gwada haseera dan haka ya aika karamar kanwarsa halima ta kira masa ita hasera na tare dasu baraka da suka zo biki suna hira hally  ta shigo tace “aunty hasera yaya Adnan na kiranki yana d’akin ya Sadiq ta fice abunta, haseera ta dubi baraka tace “Ina zuwa oga yayi kira ta figi mayafinta ta nufi dakin ta sameshi zaune da fuskarsa a d’aure sai da gabanta ya fadi muryarta a raunane tace “Ina wuni?” bai amsa ba illa idanunshi daya tsura mata yana qare mata kallo tsab “wai kana kirana gani ? ya mike yana cewa biyoni , jiki a sanyaye ta biyosa har gidin  motarsa ya bud’e ya shiga yayi kasa da glass din motar  shiru bai yi mgn ba Kuma bai wuce ba,dan hk ta fahimci shigowa yake son tayi .
ta bud’e ta shiga ta zauna yaja basu tsaya a koina Sai adiaraba daidai wani rubabben gida ginin kasa gbdy ginin babu cement da zallar kasa akayi , ya fito itama ta fito tana biye dashi suka shiga gidan suka tsaya a tsakar gidan , ya dubeta yace “kinga gidan nan “? Tace “na gani gidan waye”?
“Gidan da zakiyi rayuwar aure  dani Kenan .”

Ta d’ago ta sake dubansa tace “me zamuyi da wannan gidan da matsayinka da komai ka zabi rayuwa a irin wannan muhali gsky ni dai bazan iya zama anan area ba ma bare wannan gidan ka canza tunani ya numfasa yace “haka ne diyar professor kmrki tafi karfi zama anan amman karki manta kece kike bukatar aurena bani ba dan haka muddin zaki rayu dani to anan zaki zauna, Idan kin amince a saka rana a karshen watan kmr yadda kuka bukata idan baki amince ba kije ki sanar da iyayenki a fasa .”
  “Wallahi bazan zauna ba aure Kuma dole a daurashi babu fashi zan fad’awa mahaifina ya Siya mana gida a duk area da kake so amman nan wallahi bazan iya zama ba ai sai na mutu gbdy unguwar ma wari yake taya ma zan fara rayuwa anan  idanunta sun  rufe sai zuba maganganun take ya wuce ta ya shiga mota ta fito tana cika tana batsewa ta bud’e dayan bangaren ta shiga bata gama zama ba ya fige motar kamar sanda zasuzo babu Wanda yacewa danuwansa komai har suka karaso bakin kofar gidan ya tsaya batare daya fito ba sannan bai kashe motar ba tana fita ya ja motarsa da gudu .”


Da sassafe  Ko abinci ɓata tsaya ci ba karfe bakwai daidai ta fice daga gidan babu wanda ya sani ta nufi gurin  aiki  ,dan zaman gidan ya isheita  sai data gama ayyukanta karfe biyu ta soma Kiran layin jaguwa kmr koda yaushe bai d’auka ba, dan haka ta yanke shawarar zuwa gidansa  yana kwnace yana sharar bacci daga shi sai boxes , ta tashesa ta hanyar shafa qirjinsa ya d’ago ya kalleta sannan ya sake maida  kansa ya dan juyo ya kalleta “me Kuma kikazo  nema ya fad’a kmr bai ji dadin zuwanta ba ,nan kuwa jin zuciyarsa yayi fesss “kai me yasa idan na Kira wayarka baka d’auka ?” idan muna tare ka dinga  nuna kmr duk duniya kafi sona akan kowa amman da zarar mun rabu shikenan baka da lokacina .
“me yasa  zan d’auki wayarki?
“idan na d’auka  nace miki me saboda Allah ?ta tsura masa Ido kamar zatayi kuka dan idanunta sun cika da kwalla muryarta na rawa tace “haba adnan laifi ne dan na kiraka Ko muryarka naji banganka ba zanji sanyi araina ,
yanzu dana zo naga lafiyarka shima haushi Kaji, me kake son dani ?”  ni kaina banajin dadin wannan rayuwar da nake ,baka sona haka iyayena basa sona da kai zaku taru Ku kasheni ….”ta k’arasa maganar idanunta na cikowa da kwalla .
ya sauke numfashi yana kallonta ta goge kwallan shima ya tsura mata Ido”meye Kuma abun kuka ba wai ban damu dake bane duk abinda bazai yiwu agareni ba Kuma na Lura zai  janyo min matsala arayuwata gudunsa nake tarayyarmu bazata Yiwu ba yanzu da bakinki kince iyanyenki basa sona amman ni ban damu su soni ba tunda bani da abinda zaa so  agurina ki hakura Kawai .”
tanweer ta sake Shiga tashin hankali”To ni dai ina sonka kuma ka dinga d’aukar wayata dan shine dalilin zuwa na  ” yanzu Kawai dan ban d’auki wayarki ba Kawai kikazo ?”
“ba Kawai bane Adnan daidai da second daya idan ban ji muryarka ba  zuciyata babu zaman lafiya yayi murmushi daga zuciyarsa yana tausaya mata sosai . “Allah Ko to shikenan zan tattara na dawo gidanku dan gara na dawo gbdy ki daina  wahalar da kanki ta
kwanto jikinsa tana sakar masa tsadadden murmu shinta “kasan Allah  da ka kyauta min shikenan kullum sai na dinga ganinka. “uhmm lalle kuruciya yana janki dayawa  tanwer ,ya mike tsaye ya fita ya barta kan katifarsa kusan minti talatin  sannan ya dawo  hannunsa rike da farar Leda dake dauke da soyayyar kaza da Kwai had’e doya ya sata ta hada masa shayi suka ci tare taci sosai dan yunwa take ji.
ranar ma anan ta k’arasa yinta suna makale da juna Sai dai bai yi  kuskuren yin romancing dinta ba bare ta kai su ga having sex , ita kuwa taso yayi mata  abubuwan daya saba mata koda kuwa bazai kusanceta ba .”

A gida kuwa tunda suka Lura bata gidan hankalinsu yayi kololuwar tashi bakinciki Kamar ya kashesu har karfe goma na safe  basu Karya ba ,dady ya shirya ya tafi hospital da kanshi da doctor muyis yaci Karo yake tambayarsa yace ” tazo hospital amman bata  jima ba ta wuce  yayi jim yana tunaninta dan yasan tana gurin dan fashi , zuciyarsa sai rawa take ya fad’a yayansa zai sanar da hukuma amman yace ya dakata ,duk yadda doctor muyis Ke masa bayanin akan yana son tanwer da aure  idan ya bashi dama zai turo ayi magana, Bata Shiga jikinsa i bai  cigaba da sauraronsa ba yasa kai ya wuce inda motarsa take ya fad’a direbansa yaja suka d’auki hanyar komawa gida .”

Bangaren tanwer kuwa a hankali take  jan jaguwa  da hira da yadda take so shi “dan girman Allah ki kwantar da hankalinki
ki cireni aranki wannan aure namu ba mai yiwu bane Ko na amince iyanyenki bai Zama lallia su amince ba “me yasa kake min kora da hali ne da wannan hujjar ni Kawai ka canza sana’an zanyi confused dinsu “.
“ki daina fad’a min wannan maganar banza iya ba idan na canza wani sanar zanyi ?
” Zan nemomaka Sana’a “ki min shiru wannan ne Karo na karshe da zaki kwaso jiki kizo ta narke ajikinsa tana masa kukan shagwaba muryarta na rawa tace ” dan Allah karka min haka mana  ina tabbatar maka muddin baka bar wannan sanar ka aureni ba zan kashe kaina ya cire hannunta ajikinsa “ni ban aikeki ba ya dai kamata ki gane ba dole Sai na aureki ba kinga dan Allah daga yau Karki kara zuwa inda nake da fari  na  d’aukoki ne sabod wulakantani da kikayi,na biyu Kuma domin tabbatar da ciki  da kikace  kina da, kinga ina da kanne Mata bazanso suyi irin wannan rayuwar ba ,dole idan mun hadu sai na tabaki kinga haka ba daidai bane .
ta marairaice masa Kamar ranta xai fita “ni dai ina sonka  Kuma zan cigaba da zuwa tunda kai baxaka zo ba ,ya had’e rai sosai Kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa “dan girman Allah ki kyaleni bana son surutu tashi muje na saukeki Karki manta Kar na sake ganin kafafunki ta cigaba da share hawaye ,wallahi Shi kansa yana son kasancewarsu tare amman bazai biyewa zuciyarsa ba Idan an ciza a dinga hutawa .
ya d’ago ya dubeta tana zubar da hawaye cike da tashin hankali yake kallonta yana jin zafin digarsu “,kayi hakuri dan Allah karka rabani da kai “yana jinta yayi mata banza “, please kayi hakuri dan Allah ta fad’a tare da rike tafin hannunsa wani irin zirrrrrr yaji a gbdy ilahirin jikinsa bai san lokacin daya ce “nayi hakuri amman ki Tashi muje na rakaki ki koma gida inshaallahu zanyi tunani akanki “zakazo gidanmu yace “eh zanzo  ki share hawayenki ya fada dan ya raba kansa da matsalarta .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button