KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

JAGUWA ya qarasa a hankali ya haye matattakala har lokacin basu shigo bangaren da kofar kasa take ba sannan basu daina harbe harbe ba , bangarensu jabir kuwa gabadayansu zama sukayi tare da rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafa ,
zuciyarsu tunanin jaguwa kawai take ,suna tsananin qaunarsa musamman ganin yadda shima yake matukar qaunarsu sun san da ana yiwa mutun numfashi tabbas da zai musu ,jaguwa ya samu nasarar fitowa cikin sauri ya maida kofar ya rufe kamar yadda take ya janyo table ya maida shi ya bar gurin da sauri zuwa wani bangaren .”

Alamarin polisawa da sojoji da dss kuwa sun shigo cikin gidan sun bincike gidan jaguwa sama da kasa amman babu su babu alamun su , suka sake bincikar me gadi shi kuma ya sake tabbatar masu da lallai suna cikin gidan alokacin daya sheida masu, kuma acikinsu babu mutun daya daya fita nan da nan hankalinsu ya tashi suka fara tunanin ta ina zasu fara Ib yafi kowa shiga rud’ani da tunanin ina suka yi “? to ko ‘bacewa sukayi “? ya tambayi kansa “Lallai hakan zata iya kasancewa tunda akwai tsari me karfi a tattare dasu duk wannan tunanin da yake yana yi ne yana tafiya yana dube dube bai ankara ba yaji yayi karo da mutun yana kokarin fitowa daga wata kwana .”Shiru yayi tun daga kafafunsa ya d’auki kallonsa har zuwa boyayyar fuskarsa sannan ya saita shi da bindigarsa yana kallonsa dafe da kafadar hannunsa daya, ga kuma jini na tsiyaya, zuiyarsa ce ta soma rawa ganin irin zane mutumin daya gani d’azu a office din tanwer , fuskarsa ce kawai ta bambata da wancan mutumin ,bai tsaya wata wata ba yace “you are under arrest “.

“Na nawa kuma sp bayan gani agabanka ka kama ni mana ya fada a dake yana sakar masa murmushin gefen baki wani sabon tashin hankali da mamaki ya mamaye zuciyar Ib “kana mamaki ko to ka daina mamaki naga damar ka kamani ne shiyasa ka ganni agabanka domin ina son mu buga wata yar qaramar wasa a tsakanina da kai.” sp T. Ibrhim ya sake saita kansa da bakin bindiga kamar yadda polisawa kan yi “ka d’auka zan kamu ne cikin sauki kamar yadda ka saba kama mutane ? jaguwa bazai kamu a hannun qaramin ma’akaci sirri irinka ba aikina kuma rayuwata ce babu wanda ya isa ya dakatar dani akanshi sai dai idan bana numfashi a duniya muje gani sai lokacin da waadina ya cika ka tafi dani duk inda zaka kai ni a madadin ma ka samu qarin girma fad’uwa zaka samu daga wannan lokacin zamu fara buga wasan sp .”

“shi wannan wasan baza’a kai ga bugasa ba zaka bakunci lahira , ya dauke bakin bindiga akansa ya saita daidai saitin zuciyarsa dake harbawa da sauri sauri sakamakon abu biyu da suka hade masa alokaci daya wannan tashin hankali dana tanwer dinsa,har Ib zai harbesa sai kuma ya tuna baa bashi umarnin harbinsa ba dan haka ransa amatukar’bace ya cigaba da magana “da’ace an bani umarnin harbeka da tun yanzu anan na cika aiki kaga wasan yazo karshe kenan .”
“jaguwa yayi wani murmushin gefe baki “ good job sp ka gwada harbina mana kaga me zai faru “?.yayi maganar yana matsosa cike da kwarin gwiwa da sauri Ib yaja baya cike da firgici mutun kamar aljani.”suna cikin wannan halin sai ga wasu daga cikin jami’an tsaro ganin ib yasa suka qaraso da sauri suna cewa ka samu nasarar gani ko gawar mutun daya ne acikinsu .”?

“ban samu nasarar ganin gawa ba amman na samu nasarar kama mutun daya wanda nake kyautata zaton shine babbansu .”yayi mgnr alokacin da suka hallara “na dai yarda ka ganni zaka fad’a masu baka samu narasa kamani ba ”jaguwa ya fada. yana huci yana sake rike hannunsa dake tsiyayar jini yana masa zugi ”wata tazananniyar tsawa sojojin dake cikinsu suka buga masa da karfi “enough ka dade kana bawa jami’an tsaro wahala yau dubanka ya cika kwararre interligent police officer yayi nasarar kamaka daman kuma shi kadai ne zai iya da professional criminal like you .”

Gabadaya jami’an tsaro suka zagayesa suna huci tamkar mayunwata suna tamabayrsa sauran abokan aikinsu a tsawa ce, sun matukar firgitashi amman hakan bai sa ya nuna ajikinsa ba “ka sanar damu ina sauran abokan taadanceka suke ?“a yanzu ni kadai ne kowa yayi ta kanshi .”Ib ya dago kanshi yana kallonsa “tunda ka shigo hannu su kansu bazasu tsare ba muddin suna cikin kasar nan azabar dazaa gana maka kadai ta isa tasa ka nemosu a duk inda suke “na gwamaci mutuwa dana nemosu daya daga cikin sojojin dake tsaye agurin ya daga hannunsa zai wanka masa Mari jaguwa yayi saurin gocewa ai kuwa yasa bakin bindiga ya buga gwiwarsa kafin kace me gwiwarsa tayi kasa cikin tsananin azaba .”
Ib ya bada umarnin a shigo da yan jarida ya nufi ciki ya bar wasu jami’an tsaro tare da Jaguwa babu inda bai shiga acikin gidan ba yan jarida na biye dashi suna haskawa kai tsaye tare da haska fuskar jaguwa wanda zuwa lokacin an daba masa handcuff a duka hannuwansa har part din baya suka shiga suna dubawa “I thought bayan gidan nan na zagaye da jami’an tsaro?” haka ne sir !.”

“Ina mamakin inda sauran gang dinsa suka boye ,ku raba kwananku kuyi bincike me kyau lallai suna cikin gidan nan duk kuma wanda yayi kokarin tserewa ku harbe kansa da sauri wanda ib ya bawa umarni ya juya ya fice daga part din daidai gurin makeken table din dake part din baya ya tsaya komai na cikin falon ya hargitse sakamakon harsashin da suka sakarwa gidan ,yayiwa table din kuri da idanunshi yana dubansa yana qoqarin janye table din “qarar wayarsa ta dawo dashi dagawar da yake qoqarin yi ya dauki kiran “yes sir mun samu nasarar kama mutun daya Kmr yadda kake gani ana haskawa,yaki fadi inda sauran suke kuma an tabbatar mana suna cikin gidan gabadaya alokacin da muka shigo sir .”yana wa me gidansa bayani yana cigaba da jan table yayinda sauran inspectors ke bincika wasu bangaren.”

????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

????️46

lokaci daya me gidan IB yace “maza maza ka koma inda yake domin za’a iya nemansa a rasa dan takadirancinsa ya wuce da tunaninka ,rikeshi kawai zai sa sauran su fito d’aya bayan d’aya batare da mun sha wata wahala ba ” IB ya juya da mugun sauri ya soma d’aga kafafunsa yana cigaba da sauraron bayanan me gidansa “kana ganin dan harsashi ya samesa da wannan karfen da kuka da’ba masa a wuya da hannu kawai ya wadatar ? “ ka sani har yanzu da sauran qalubabi agareka muddin bai kai ga isowa headquarter ba “naji sir inshaallahu zanyi kokari.

Ib ya qaraso inda jaguwa da sauran jami’an tsaro suke tsaye zagaye da JAGUWA nan take ya shiga basu umarni a fito da JAGUWA zuwa waje , JAGUWA ya dubesa sama da kasa ransa a matukar dagule “wai mutumin da mahaifinsa ya fisa zama d’an ta’ada ne yake irin wannan d’agawar ?.”a halin yanzu babu mutumin da yake jin ya tsana a duniya kamar shi ji yake kamar ya kamo shi ya shake masa wuya ya kashesa ya huta ,a qalla JAGUWA ya kusan minti biyar yana duban ib cike da tsana sannan ya mike tsaye yana jan qaramin tsaki “ya fito yana daga kafafunsa da kyar dan bugun da’aka masa ya shigesa sosai kawai dai dauriya ce irin tasa .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button