KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

  “hatsabibin boka ne ni  zan tabbatar da nayiwa kawarki   abinda take bukata , zan biya mata bukatarta ta duniya,   ya juya ya kalli zahra ” zakiyi  nasara akan rabashi da  yarinyar amman   shi da wahala ki mallakesa  kamar yadda kike so , domin kuwa  wannan  mutumi ya wuce da tunaninki yana  da hatsarin tunkara domin kuwa akwai  tsari mai karfi  ajikinsa , kafafunsa yafi naki tsawo ,Inda ya taka har ki mutu  kafafunki bazasu taka ba . “
“yanzu boka  ya za’a yi kenan   wallahi idan ban mallakesa ba zan iya  mutuwa sannan babban burina na rabashi da yarinyar nan koda diyar talaka ce bare diyar mai  kudi.
sai daya numfasa sannan yace ” na fada miki bazaki mallakesa ba sai dai ki rabashi da yarinyar ,Kuma  aikin da za’a rabasu  na  bukatar  budurwar wacce    bata taba aikata zina ba  Kuma an yi nasara domin kuwa  yarinyar budurwa ce wani nmj bai taba amfani daita ba ,Ina tabbatar miki  muddin ya kusancenta zaki iya rabasu  zai dai ya saurareki   amman  ba  zakiyi yadda kika ga dama dashi  ba  yana gama fad’ar haka yace  “me kika gani ayi  aikin ko abari? “

hankalinta a matukar tashe tace “yanzu boka babu wani mafuta sai wannan ?” wallahi Ina matukar kishin Adnan bazan so ya rabi wata mace ba byn ni “wannan ne  kawai hanya mafi sauki  Shima din   ba shine zai Kai Kansa gareta ba  itace zata Kai masa kanta  , Kinga wannan saurayin  naki akwai abubuwa da yawa akansa shiyasa ma ya  rufe ma Kansa  taurari dan kar mutane su san ko waye shi   yana kaiwa nan yace ku tashi ku wuce “kafin  sati biyu  da kanki zaki kirani  ki bani labarin cigaba da aka samu  ta bud’e jakarta  ta dibo kudi masu yawa zata ajiye a gabansa  ya nuna mata gurin gunkinsa , nan taga wata tukuyar tsafi  daskare da jini ta saka kudin ,jiki a sanyaye suka baro gurin boka zuciyar Zahra cike da matsanacin kishi “gsky banji dadin wannan aikin ba nifa banason ya kusance kowace mace byn ni , yanzu ance dole sai ya kusanci yarinyar nan Kuma gashi budurwa ce Kinsa amsar budurcin mace akwai tsayawa arai   .
“ki  kwantar da hankaliki  Zahra kibi maganar boka Inda akwai wata mafutar byn wannan  zai  miki  ,ke yanzu ma meye abun d’aga  hankali dan ya kusancenta  ke da zai dawo hannunki  “wani zai dawo hannuna ko baki ji abinda  bokan yace ba ? cewa fa yayi bazan mallakesa ba ni wallahi dama na hakura da aikin nan ta karasa maganar tana yastina fuska .”

“Dan Allah kawata ki cire kishin nan a ranki mude bukatarmu ta biya  ya rabu da yarinyar shine abinda muke so  ,  har suka k’araso tasha magana daya dai suke yi blessing na kokarin shawo kan Zahra , shiru  zahra tai taki cewa komai zuciyarta na tuttukin bakinciki Adnan zai kusanci tanweer Kuma shi zai amshi budurcinta.
bangaren tanweer kuwa   taki cin  abinci,  yadda ya   kawo mata abincin   jiya  haka ya  fitar dashi   bata ci ba ,ai ko shima   ya  hau  dokin zuciya  yaki bin ta kanta bare ya  rarrasheta .” duk yadda blessing ke Jan  zahra da hira  acikin mota ta kasa cewa komai har suka sauka a lagos   kowacce ta kama gabanta gbdy Zahra ta  kasa samun kwanciyar hankali sam bata ji zata iya wannan kasadar sai  tayi kmr ta kira boka  tace ta fasa  aikin sai Kuma  ta fasa   .”


Zaune jaguwa yake  cikin baban falonsa system ne a gabansa yana aiki   eku ya shigo tare da rusunawa ya gaishesa ya amsa batare daya d’ago ba eku ya  soma magana cike da ladabi “boss kamar ka manta da wancan mutumin ”  Jaguwa ya d’ago ya  kallesa  a tsanake yana bukatar qarin bayani “wancan mutumin dakace mu dauko a Rita Lori hotel mu  killace maka shi ” sai lokacin jaguwa ya tuna ya lumshe idanunshi  “Yana Ina ne ?”yana boys quarter ya gyada Kanshi kawai ya cigaba da abinda yake eku  bai  wuce  ba sai da jaguwa ya gama abinda yake ya mike yana tafiya kamar baya son taka kasa yayinda eku ke biye dashi har suka k’araso bakin kofar d’akin da alqali yake , eku yayi saurin  bude  masa kofar  d’akin , alqali najin motsin mutane ya shiga zare Ido jaguwa ya tsura masa Ido ya rame sosai  rama ta tashin hankali acikin kwana biyu  da yayi wanda idan ka kallesa bazaka sake marmarin kallonsa ba duk ya fita haiyacinsa, zaune yake jugun hannunwansa da kafafunsa duk kulle su da handcuff kamar wanda yake prison a hankali  jaguwa  ya shiga Taku a hankali  yana masa wani wulakantaccen kallo sannan ya tsaya a tsakiyar d’akin  yana cewa”waye Kai menene yasa kake bibiyata ?alqali da bakinsa ya bushe sosai ya fara magana cikin wahala “babu dalilin da yasa na  bibiyeka ya karasa maganar cikin tsananin tashin hankali .
“waye Kai ?”shiru alqali yayi ya kasa cewa komai jaguwa ya juya ya soma tafiya “Ina ganin azabar yunwar da’aka masa  bai ishesa  ba ka cigaba da barinsa babu ci babu sha har ya zamo sanadinsa ”  alqali wanda muryarsa ta fara dashewa babu karfi a tattare dashi yace “kayiwa Allah kayi hakuri na tuba  “jaguwa ya cigaba da tafiya batare da juyo ba  “idan na fada maka bazaka kasheni ba ?”yayi masa bmbyr a gigice cak jaguwa ya tsaya tare da goya hannuwansa duka  a baya ya juyo
ya tsura masa Ido alamun yana sauraronsa “ni ..ni  …sai Kuma yayi shiru yaji tsoron sheida masa cewar shi din jami’in sirri ne  ” kayi hakuri dan Allah ka tausaya min nayi kuskure bazan sake ba “runtse idanu  jaguwa yayi  ,ba dan baya son aikata kissa a rayuwarsa ba da babu shakka da sai  ya shake wuyan  wannan
mutumin da hanunsa har sai ya mutu
“kaga nayi  kama da wanda za’a bibiyi rayuwarsa for the  last time  ka fad’a min wanda yasa ka bibiyeni?  yayi masa tmbyr yana hade fuskarsa kmr hadari.  shiru  alqali yay ya kasa magana Dan Bai San abinda zai ce ba har kusan minti biyar Yana tsaye yana jiransa  ,eku ya Ciro karamar pestol  ya saita gefen brain dinsa “na baka minti biyu ka fadi Wanda ya sakaka  kafin na tarwatsa brain  dinka na aikaka lahira  “wa ..wallahi babu kowa Ina tafiya ne na gansa tare da yarinyar minister of health da ake nema  shine na dinga binsa a baya naga Inda zashi daita wallahi  byn wannan babu Wanda ya aikoni .
“ka cigaba da ajiyarsa anan har sanda zai fadi  gskiyar  wanda ya aikosa sannan ka ciyar dashi da  gari zalla da ruwa ,ruwan ma kwatan tea cup haka ma gari muddin yayi  wata bai fadi Wanda ya aikosa ba  ka tashesa aiki yana gama fad’ar haka ya fice daga daki  haka ma eku ya nufi kofar fita kmr wani  zautacce alqali ya rarrafa da gwiwawinsa   yana k’okarin riko ka’fafun  eku Amman Ina tuni ya fice ya maida kofar ya rufe cikin rashin tausayawa,   hawayen danasani suka silalowa alqali ya fara zubar da hawaye yana adduar Neman mafuta “me yasa ka biyosa gashi ka jefa rayuwarka cikin hatsari kuka yake sosai  kamar karamin yaro.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button