KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48


Jaguwa ya gyara  tsayuwa   yana shafa  qirjinsa da hannu d’aya sannan  yana   jin  bayani  amminsa daki daki  akan matar data samo masa  ,”ammi ki bar maganar wata  hasera  a yanzu , zanyi k’okari na  kawo miki wacce zan aura “.ya fadi hakan ne ba dan zai Kai mata din ba sai dan ta rabashi da batun  wata hasera .
  a bangaren ammi ta katse shi da sauri  “lokaci ya kure maka bazan sake baka wata dama ba dan naga alamun zuciyarka bata shirya amsar soyayyar kowace mace ba ,gara ni na shirya maka  ga  hasera  nan ita  zuciyata ta zaba maka  Kuma ita zaka aura muddin Ina raye  idan Kuma bujirewa zabina   zakayi to sai ka sanar min ?   “. Shiru yayi
tare da lumshe idanunshi a tsayen da yake dan amminsa ta rigada ta gama d’aure shi da maganarta “kayi shiru ko bazaka bi zabina bane  nasani ? “
“Ban Isa ba ammi ,ban Isa naki bin zabinki ba amman ki canza min da wata ban da hasera”  ya fad’a yana Jin wani sabon tashin hankali ya kusanto rayuwarsa   “Amman  Kaine kace duk wacce  na zaba maka  baka da ja ?sun d’auki tsawon lokaci suna tautaunawa a karshe yace ta bar maganar idan ya shigo karshen sati zasu sake tautaunawa akai “.
Bayan ya gama waya da ammi ya  boye  number ya  kira mahaifin tanweer magana biyu yayi masa  ya katse Kiran  sannan ya kira  number baba yana sheida masa zai maida tanweer  gobe “bana ce maka karka kuskura ka  maida yarinyar nan ba ?
“wannan  yarinyar da kake  tare daita a gidanka  karka yarda ka rabu daita ko ka yarda  ta matsa a kusa da Kai kmr yadda na fad’a maka a watanni da suka gabata ,
abinda bakasani ba   ajikinta akwai taurari masu  haske da  karfin da zasuyi maka amfani  akan aikinka ka barta a karkashika  karka yarda ta bar karkashinka “.
“shiru  jaguwa yayi yana tunanin abinda yake ta fad’a masa kenan  kafin daga  baya ya soma magana a sanyaye “bazan iya cutar daita ba  sannan bazan iya amfani da taurarinta ba,  idan da hali na zauna a yadda nake.
na samu duk abinda nake nema batare danayi amfani da taurarin kowa ba..”.
“Wannan yarinyar dabam ce km  ko ba yanzu ba  dole zaka   bukaci me irin taurarinta sai dai ba lallai ka samu  ba   dan haka ka barta  kayi amfani da taurarinta  .” bazan iya cigaba da zama da…..”
“to ka aureta  domin ta kasance a karkashin ikonka abinda ake so dai ta zauna tare da Kai “.
“Aure  Kuma  baba ?”

Mmn sudais
Mmn sudais????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????

PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN domin sauraron littafaina a tuntubi channel dina ta hausa bakwai     .

????️ 21

“Eh  ! abinda  nake  nufi  Kenan  kuma  nake   bukata  ka  aikata,  muddin   wannan   yarinyar   bazata   kasance  karuwarka   ba  to  ya  zama   lallai  ka  aureta   Kuma  acikin tsakankanin wannan    lokacin  “.
Cikin   tsananin  firgici da  tsinkewar  zuciya  jaguwa  yace ”  me   yasa   baba ? “mai yasa   baza’a bar   wannan   maganar ba  dan  Allah ? ” ni  dai  gsky   a biyo  wata  hanyar   banda  wannan,  tanwer  tasan  koni  waye , tasan  sana’ata  fashi  ne , nayi   Imani   Koda na fada  mata  zan   aurenta  bazata  aureni  da   wannan  sana’ar ba ya k’arasa maganar tare da  yin shiru yana tunanin  zuci  “shi  dai  gaskiya  komai za’a yi  bazai  taba  auren  tanwer da wata manufar ba  ko cutar daita ba domin  yana  jinta  ajikinsa   tamkar   jininsa  .”

Shiru  ne  ya  biyo baya na wasu mintuna  kafin daga bisani baba ya  numfasa  kana ya soma magana  a dake “Hanya   daya   ce  zata  maye maka  wannan  gurbin , ka  nemi  mace   mai  irin  taurarinta  ka ajiyeta   akarkashin  ikonka  Koda  bazaka   aureta  ba ka dinga saduwa  daita  saduwa irin ta aure    idan   kayi  haka shikenan komai  zai cigaba da tafiyar  mana yadda   muke  so batare da wata matsala ba   .”
“shiru   jaguwa   yayi  yana kallon  zara  zaran  yatsun   kafafunsa  masu tsananin kyau da   sheki  yana  nazarin maganar  baba, nan  take  gumi ya  shiga  tsatsafo masa  a dukkanin   ilahirin  jikinsa, kwakwaluwarsa  ta  toshe  zuciyarsa  ta  cunkushe  guri daya , tunanin  da  yake ya tsaya cak  ya  Kasa  cigaba da tunanin  komai . sai  daya  dauki  minti  biyar   tsaye  batare da yasan madafar  dafawa  ba “amincewa  auren  tanwer  Ko  nemo  mai irin taurarinta ya ajiyeta akarkashin  ya dinga  aikata zina daita   “shi da yake neman yakice  zina  arayuwarsa sai ga baba  na kokarin  maidashi  ruwa tsundum.
“Ya amince  ne  ko kuma ya  fada masa a sake nemo wata mufutar ?  sautin  muryar  baba  ne ya dawo dashi cikin hankalinsa  ta Inda ya  cigaba  da  zayyano masa hujojinsa akan  bukatar auren tanwer da yake son yayi  Ko kuma  ya  shiga  gari ya nemo mace  me irin taurarinta  idan ba haka  ba  nan  gaba  kadan za’a  yi  galaba akansa  ” .

duk abinda baba ya  fada  yasan  yana  da  huja  akan hakan kuma yasan ya fada ne domin ingata rayuwarsa daga sana’ar fashin da yake  but  shi  baya jin  zai iya  ajiye  tanwer a  matsayin karuwarsa  Ko aurenta domin samun  wani  biyan bukata  daga gareta  “. ya runtse idanunshi yana  mai  sake  gyara tsayuwarsa  yana  jujuya  maganganun baba  yana sake fadadasu  yana masu filla filla , gbdy  komai  ya  tsaya masa.
ya sake  neman natsuwarsa  ya rasa , ji yake Kamar zuciyarsa zata  buga   tsabar  shiga rud’ani  tunanin  matsalar dcp ,tanwer ,
Amminsa  , yanzu  Kuma ga matsalar baba da me zai ji?
“me ya kamata yayi ya samar ma  zuciyarsa salama ? yana jin kamar yace   babu abinda zai yi acikin umarnin baba wanda wannan shine  Karo na farko da zai sabawa umarninsa a tun tsawon lokacin  da suka dauka tare  dan bai taba cewa ga abinda zaiyi ya mutsanta  masa ba sai dai ya aiwatar . “
“tun  yanzu ka fara tunanin  shiga  gari  domin  nemo me irin taurarin  yarinyar nan ka ajiyeyata  a matsayin karuwarka  dan nasan bazaka taba aurenta ba tunda baka amince da auren  yarinyar nan ba  .”
Juya  maganar  baba yaketa faman yi acikin kwa kwaluwarsa , zuciyarsa ta dunkule guri daya  yana jin Kamar ya daura hannu akanshi ya saka ihu ko yaji saukin zafin da zuciyarsa ke masa sai daya sanyawa jikinsa jarumta sannan yace “wacce irin alama ce  zatasa na gane me irin taurarin tanwer ?
“Kenan kafin bukatar wata akan wannan yarinyar ?
“bazan iya cutar daita bane ” ya fada yana furzar da iska mai zafi daga  bakinsa,  shiru baba yayi kafin daga bisani ya numfasa sannan  ya   cigaba da mgn “alamar da zaka gane me irin taurarinta , kana ganinta duk wata kafa ta gashi  dake kwance ajikinka zata mike, take wannan zoben dake hannunka zai yi baki, abu na gaba tsuntsun dake ajiye a gidanka zai bayyana akanta wannan shine alamar me irin taurarinta amman fa bai zama lallai ka samu ba.”
“zan samu …..”  ina samun nasara akan komai dana saka gaba wannan Karon  ma  nasan zanyi nasara  da yarda Allah   “Ina  maka   fatan  alkhairi da fatan samun nasara  yana  gama fadar haka  yayi  disconnecting din Kiran , jaguwa ya cigaba da tsayuwa  agurun tare da lulu duniyar tunanin .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button