KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Wani hadadden gidan sama ne da hawansa ya kai goma ,Maganar adadin daku nan dake cikin wannnan gidan ba azai lissafu ba ,daya daga cikin dakin mutane guda shida ne acikinsu sai dai mutun uku ne kawai a zaune sanye da bakaken kaya ,
yayinda mutun daya dake cikin wadan da suke tsaye ke yaga farar takarda yana cewa “wannnan takardar babu abinda zata mana bayanan wannna file din ne kawai zai mana amfani sun dauki lokaci suna tautaunawa akan gurbatacciyar kasuwancinsu kafin daga karshe nabel ya dubi alhj tajudenni “ya batun yaran nan kuwa sun nemeka sun baka hakuri ?ya girgiza kai alamun” a’a ! nabel ya gyada kai “amman sai da nayi masu gargadi kamar zasu yi aiki dashi ashe aikin banza nayi “ina fad’a maka taurin kansu ya wuce tunaninka “. Ina bukatar bayanan kowanne acikin wadan nan mutane guda biyar din inji wanda ya fara magana da farko wato Ahmed abba “.
“Idan muka bibiyesu hakan zai sa su qara suna a idanun duniya ,ba kuma zai yiwu ace kmarmu mun buga qasar mutuwa dasu ba inji cewar dahir “ai kuwa gara a tashesu aiki a share babinsu na daina jin duriyarsu acikin duniyar nan shine kawai kwanciyar hankalina kullum da tunanin wadan nan mutane nake kwana nake tashi most especially mutun biyu din nan jaguwa da amininsa lallai sai na daina jin bugun numfashinsu hankalina zai kwanta ruhina ya samu salama ya qarashe mgnr cikin tsananin tashin hankali ai kuwa hankalin kowa dake gurin ya tashi
“ai kuwa bazamu barsu ba lallai sai mun ga gazawarsu takowa ni hali nabel ya fada tare da daukar glss cup dake cike da tacaccen ruwan giya ya kai bakinsa .”

tunda suka fara maganarsu akan jaguwa tanko gote na zaune bai ce uffan ba sai yanzu “nifa ina ganin kamr aikin sirri suke wa gwanati , dan ban ta’ba ganin yan taadan da suka gagari kasa da kasa ba sai su ,ko a labari ban ta’ba jin masu irin sanarsu sun dauki shekaru me tsawo suna wannan aikin ba batare da anfarmakesu ba an musu kissan gilla ba , bugu da qari kafafunsu nada tsawo akwai asiri ajikinsu ,ai naso na jnyosu cikin mu amman sam yaran nan suka ki yarda, kunsan kuwa idan babu wata a kasa basuki amsar tayin alqalarmu ba ,gashi fashin su basayiwa masu adalci sai marasa adalci da azzalumai suke yiwa duk kuma inda masu laifi suke sai nemo sun masu hukunci sannna sun hadasu da jami’an tsaro,ku duba mutane guda biyar din daake zargi da kisan honorable ai sune silar shigarsu hannu nifa a nawa mu manta dasu muyi lamuran gabanmu kar muna zaman zamanmamu mu janyowa kanmu balai ba fadawa hannun hukuma bane matsalar zubewar mutunci idon duniya shine abinda zamu duba dan ta hukuma me sauki ne “.
Ya karashe maganr yana dubansu daya byn daya .”
“Abinda ya kamata muyi bincike akansu ba wai janye hukuncinmu ba ni nan zan yi bincike akansu ku bani kwana daya kacal inji nabel ya fada yana daga musu yatsansa daya “wallahi muddin nayi bincike banganosu cikin masu binciken sirri ba lallai ni nan zanyi ajalinsu daya bayan daya…””

????????????????????????
KUSKUREN BAYA
     ????????????????
????????????????????????

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

????️42

……a hankali kan jaguwa ya dinga sarawa da karfi tamkar ana buga masa guduma, zamewa yayi kasa sosai gumi na tsatsafo masa har akan karan hancinsa ,labbansa ya motsa magana ta fito cikin wani irin yanayi na tashin hankali “oh my goodness wai meke shirin faruwa dani né ?tanwer tana qoqarin juya min baya haka shima anas “why anas kai fa nawa ne na har abada ban cancaci kayi min haka ba ?.”
Gabadaya idanunshi sun kad’a sunyi jazur tamkar garwashin wuta , zuciyarsa na masa wani irin zafi ya dinga jin kamar ya fixgota daga qirjinsa ya fito daita waje ya huta , cikin tsananin damuwa ya zaro wayarsa daga cikin aljihunsa ya shiga app ya tsurawa cikin wayar kwayar idanunshi anas ya gani zaune kusa da hally hankalinsa kwance babu wani alamun damuwa atattare dashi .
“Shikenan bai damu dani ba ?”bai damu da kowani hali zan shiga ba rayuwarsa kawai yake ? yayiwa kansa tmbyr da bashi da me bashi amsarta,mikewa yayi cike da sanyin jiki ya bar d’akin ya wuce direct hanyar d’akin da suke ajiye kayan shaye shayensu bai qarasa ba eku dake zaune ya hangosa dan haka da sauri ya taso ya biyosa yana tambayarsa “boss akwai abinda kake bukata ne ?.”

Ya tsaya cak batare daya juyo ba yace “wiwi nake so , okay boss an gama ,”kayi min babban nad’i kamar guda goma yayi maganar tamkar wanda ya sha ruwan barasa ,eku yayi shiru yana d’an dubansa sai dai bai ga alamun a buge yake ba ,koda yake shi daman baya shan ruwan barasa iyakarsa wine non alcohol ko wiwi da taba baya wuce wadan nan abubuwan “shikenan boss ka koma ciki zan kawo maka yanzu , kamata ma yayi ka kirani ba wai dan wannan bukatar ka fito da kanka ba .”
Jaguwa bai ce uffan ba ya juyo ya fuskancesa “shiga kayi abinda nake bukata ka bani kawai” babu musu eku ya shiga cikin d’akin ,cikin kankanin lokaci ya nad’o masa tabar wiwi babban nadi kamar yadda ya bukata “muje na kai maka boss wannan karon bai ce masa qala ba sai ma ya kai hannunsa ya d’auki guda d,aya ya kai bakinsa eku yayi saurin miko masa abun kunnawa .”

ya kunna cikin kwarewa ya soma zuka yana daga kafafunsa a hankali yana fitar da hayaki bai tsaya akoina ba sai falonsa dake had’e da bedroom dinsa ya zauna akan daya daga cikin kujerun dake falon tare da d’an zamowa yana fitar da hayaki ta hanci ta baki ,eku ya ajiye masa faratin wiwi akan table ya juya tare da rufo masa kofar.”
” ko cikakken minti biyar ba’ayi ba ya gama da guda hud’u nan da nan kwayar idanunshi suka sake rikidewa ya soma skiping na maye nan da nan idanunshi suka fara hango masa tanwer dinsa acikin idanunshi cikin shigar kananan kaya wondo iya cinyarta da wata yar karamar riga da tsayinta bata wuce kasan dukiyar fulataninta ba, yayinda cibiyarta ke bayyane a ganinsa , tana sakar masa tsadadden murmushi ,wata irin zabura yayi ya mike tsaye yana sake ware idanunshi da suke lumshe irin na masu zukar wiwi “.

“Tanwer kin had’u sosai gskiya qirarki ta had’u sosai ,ya za’ayi ki bar adnan ya samu kwanciyar hankali da sukuni? ai sam qirarki bazata bar zuciyata ta huta da tunaninki ba bare tarin qaunar da nake miki ta raqu ,komai naki yayi min sosai ,
haka nake son mace kamar yadda kike , zan iya ‘bata tsawon rayuwata kawai ina kallonki, tunanina babu wata halitta me kyawun halitta kamar naki ,hatta taurarin da suke sararin samaniya nasan suna jinjinawa halittar qirararki ,ina sonki tanwer lallai sai yanzu na fahimci sirrin dake tattare dake ina kewarki cike da soyayyarki dan allah karki barni haka bazan iya jura ba kamar yadda kika jurewa soyayyata.”

” kamanin surarta ne kawai ke yawo acikin tunaninsa, tsukakken kugunta wanda ke d’auke da faffad’an mazaunai masu rikitarwa da birkita lissafi yaga ta juya masa rikicewa yayi ya rungumo a iska amman shi gani yake kamar itace ajikinsa yana sarrafa sansar jikinta , ya sake kai sigari bakinsa ya zuka da iyakacin karfinsa” ina jin tsoro tanwer bazan iya jura ba ,bazan iya rayuwa babu ke ba ,kice soyayyata,kece haukana ,kece rayuwata dan allah karki barni “
kansa ne ya cigaba da sarawa amman bai daina zukar hayakin wiwi ba daman kuma haka yake yi a duk sanda ransa ya ‘baci idan yana son ya huce har ya samu bacci dole sai ya sha wiwi over amman wannan lokacin bai yi tasiri ba domin har 2 na dare bai samu barci ba sai tunanin da yake ta qaruwa a cikin kwakwaluwarsa da zuciyarsa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button