KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Matsalar Kenan Duk kwanakin da zarar  ana magana zaka fara Kawo batun mutuwa ,zamu mutu amman ba yanzu ba anas ya bud’e baki zai yi mgn jaguwa yace “kaga malam karka ce komai  ga sauran kazar da nacan na rage  maka  kaci kaji dadinka ya juya zai shige bedroom dinsa   Anas ya rikoshi ya marairaice.
” dan Allah Adnan kayi hakuri  ka  lallaba yarinyar nan  ta zubar da cikin ta dadin rai  ,yadda  kake mata din nan  zai bugar mata da zuciya tana bukatar rarrashi da kulawa , jaguwa   yay masa wani irin kallo mai hargitsa kayan ciki  “dan Allah ba dan ita ba .”
Ya numfasa kana yace” naji zan kiranta “yauwa to  Ko kai fa dan Allah ka lallaba ta kaji abokina. Baice komai ba ya wuce zuwa uwar dakansa ya hau kan katifa ya kwanta ya janyo blanket ya rufe rabin jikinsa sannan ya lalubo  wayarsa ya  ya fara neman layinta kira d’aya ta d’auka qirjinta na buga da sauri sauri tsayawa tayi batare da tace komai ba shima shiru yayi na kusan minti goma yana sauke mata numfashinsa a kunne kafin daga bisani yace “hello ..!
Shiru tayi tare da kasa kunne tana jin zazzakar muryarya mai kashe jiki ,a hankali ta dinga jin wasu abubuwa na yawo ajikinta cikin zazzakar muryarsa yace “ya kike ?”a hankali ta bud’e bakinta “yanzu Adnan ka kyauta min Kenan ? lafiya muka rabu da kai fa,a tunanina kira d’aya idan kagani da kowacce number zaka biyo Kiran a tunaninka ko nice amman sai kayi watsi dani.
cikin murmushin yace “kiyi hakuri yanzu ya kike jin jikinki “.
gumin dake tsatsafo mata a bisa goshinta ta goge tana sauke numfashi hade da cewa “gani nan dai sai hankali wahala nake sha gashi kace a zubar da cikin saboda baka qaunata sai dai ni bazan zubar ba ina son abuna ..”

Naunayyen ajiyar zuciya ya sauke da karfi ya kamo lips dinsa na Kasa yana cizawa  a hankali yana yabi yatsun hannunsa da kallo dan tunanin Kalmar da zai mata amfani daita gurin lallabata “kace Baka bukatar cikin Ko”?
Shiru yayi na tsawon minti goma kana a hankali ya fesar da numfashi  ya kwantar da murya “ba wai bana son cikin bane matsala zai zame mana arayuwa bare ke da kike matsayin  mace  “ni dai gsky Ina son kayana “a hankali ya d’aura tafin hannunsa a goshinsa ya dafe tare da lumshe idanunshi cike da kulawa yace “nima Ina son abuna amman kiyi hakuri acire zamu samu wasu nan gaba.
“Da gaske kake ?”
Yayi shiru yana cigaba da cizan lips dinsa .
A hankali ta Kira sunansa “Adnan !”a hankali ya motsa lips dinsa “na’am tan .”ka tabbatar zamu samu wasu ? da kyar ya fixgo mgn “eh idan kika bi umarnina kika cire ba ya k’arasa maganar yana shafa sumar kanshi “tunda muka rabu ban kara samu sukuni ko walwala ba har mamakin kaina nake kullum cikin damuwar soyayyarka nake da zazzabin cikin nan bana wani cin abincin kirki gashi Kowa ya gane halin da nake ciki a gida “.
“oh my god tanwer me yasa kikayi haka me yasa kika bari suka sani ?
“saboda ina qaunarka ta k’arasa maganar kmr zatayi kuka ..
Qirjinsa yayi masa nauyi tausayinta ya lullubesa duk da bai son yawon surutu amman haka yayi shiru yana biye mata “gsky banso kika sanar dasu ba “to yazanyi da rayuwata dole ce . ya dunkule hannunsa sosai yaji ya Shiga damuwa” ina sonka Adnan Allah idan bakayi wani abu ba tunanika zai kasheni  “
ki daina yawon tunanina .
tace “bazai Yiwu ba yanzu ma Na fara idan kaga na rage tunaninka to ina gidanka ne “
“Ki rage yawon tunsni yana kisa ,dan Allah kiyi kokari kije asibiti gobe acire cikin nan sannan su rubuta miki magani. “nifa bazan zubar ba .
Ki yi abinda nace shine  kwanciyar hankalina  sun dade suna magana akan ciki duk yadda yayi daita  taki  amince masa   da zata  cire cikin,  wanda ita a zuciyarta   tuni ma  ta yarda  kuma ta amince ma zuciyarta zata  cire ta hutawa ranta tunda shima bai so amman bazata yarda ta bari yasan zata cire ba sai ta d’aga masa hankali.
“ki kwanta ki huta zan  Kiraki  zuwa  gobe amman ki tabbatar kin amincewa ranki zaki cire “
Tace “to !
“karkiyi tunani komai kinji “
  ta sake cewa ” to ! ta fad’a tana  jin zafi aranta  saboda gbdy ta gano rashin sonta da bai mata sai  tana jinshi  ya katse Kira .”

zuciyarta ta  kasa  samu natsuwar  tunanin daya gargade shi ta cigaba da yi, bata da burin da wuce ta mallakesa a matsayin mijin aurenta , tunani kala kala tayi ta saka wancan ta  kwance har ta shigo    tunanin rayuwar da sukayi  agidansa a farkon zuwanta  suna lullube dashi cikin bargo d’aya babu kaya ajikinsu tana makale a gefensa  yayinda hannunta d’aya Ke Saman faffadan qirjinsa shi kuma yana shafa  sansar jikinta tare da sarrafa albarkatun  qirjinta nan take  tsigar jikinta  suka tai  mikewa  ,ta dinga jinsa ajikinta a hankali  jikinta ya kama kyarma  ta kankame jikinta guri daya tana jin kamar jijiyarsa na shiga jikinta ,yayinda taji tafukan hannunsa na yawo sansar  jikinta da wannan tunanin bacci barawo ya dauketa .”

Washegari da misalin karfe biyar da rabi ta farka had’e da yin mika , jiki a sanyaye ta sauko daga kan gadonta     tashiga bathroom tayi alwala  ta fito ta gabatar da Sallah byn ta Idar bata tashi  ba ta kwanta akan sallaya  tana azkar  tana  kuka har ta gama ta kama addua “rabbi Inni Lima Anzalta Ilaiya min khairin  faqeer ta dade kwance tana tunani da fargaban zafin cire ciki ahankali baci ya dauketa sai gurin karfe goma ta farka ta mike tare da nade dadduma Sallah ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta  shirya  ta  nufi d’akin mumy anan  ta samu  mumy har dasu uncle bashir   byn ta gaishesu ta gaishe da mumy sannan  ta roketa  tare  da bata hakurin damuwar da ta sakata jiya, sannan Kuma  ta  tabbatar mata Da ta amince  a cire cikin .
nan take mumy taji ta warke daga ciwonta ta ji jikinta ya dawo normal damuwa ta bar gangar jikinta sai faman saka mata albarka take “inshaallah sai Allah ya yaye Miki abinda kike ji akan dan iskan mutumin nan ,
Allah ya yaye miki gbdy suka amsa da” ameen”.
cike da farinciki suka dauketa zuwa babba asibitin kudi batare da bata lokaci ba suka Samu ganin likita suka fad’a masa taimakon da zai musu ,dake yasan minister bai tsaya  bata musu lokaci ba yayi mata gwaje gwaje dan ya gano cikin  Ko na wata Nawa ne dan yasan me za’a mata ganin karamin ne yace “za’a Iya bata kwaya tasha  amman fur dady yace a’a  ayi mata abortion Kawai zaifi samun natsuwa , dan haka batare da bata lokaci ba aka Shiga daita Wani d’aki .
ta sha wahala sosai Kamar zata mutu  har aka  gama kuka take tana Kiran “wayyo Allah zan mutu  nurse ta d’auki sama da minti talatin tana aikinta  bayan an gama nurse   ta fito ta barta ta dan huta .
byn kmr awa d’aya ta fito tana d’aga kafa da kyar tana jin jikinta kmr ba nata ba sai dai ta daina jin nauyin da jikinta yayi mata  amman   kallo  d’aya zaka mata ka tausaya mata dan  taji jiki sosai  , duk tayi wuri wuri Kamar wacce tayi shekara tana ciwo.
  sai dai ciwon bai kai zafin rashin son da jaguwa yake mata ba office din doctor  ta shiga inda ta iske su dady zaman jiranta doctor  ya  rubuta mata magugunan da zasu taimaka mata sannan suka dawo gida .
Kai tsaye d’akinta suka nufa daita suka kwantar daita akan gado suka zagayeta suna mata Sannu  “doctor yace abata ruwan zafi ta sha kafin ta sha magani inji cewar uncle Jamil.
  mumy najin haka  ta mike da sauri  ta fita ta shiga kitchen da Kanta ta dafa mata ruwan zafi ta juyo a cup ta dawo d’akin “Tashi ki sha kinji tanwer dina ,tan ta soma k’okarin mikewa uncle bashir ya taimaka mata  ta zauna  tana fidda zazzafan numfashi ya janyo pillow ya saka mata abayanta ya jinginata yana mata “Sannu!”
Mumy ta mika mata cup din ruwan zafi tana sake mata “Sannu”! tanweer ta gyada mata kai Kawai dan ita kad’ai tasan ciwon da zuciyarta ke mata .
a hankali ta dinga kurban ruwan zafin ,kadan ta sha tana k’okarin mikawa mumy cup, ta miko mata magani ta karba ta sha da kyar ta mika mata cup ta koma ta kwanta lamo had’e da kunna wayarta dan tun safe a kashe take ta tura karkashin pillow   .
Ko minti biyar batayi da kunna  wayar  ba,ta soma babriting alamun ana Kira  ta lalubo tana  duba screen din wayar  number jaguwa ne dan haka ta maida wayar inda ta dauko batare data dauka ba ta runtse idanunta sai ga hawaye masu zafin gaske wanda take jin zafinsu har cikin jikinta .
“ya kiranta yanzu saboda yana bukatar ta zubar da ciki amman ita kira nawa tayi masa bai d’auka ba ?”tana jin Kira na sake shigowa wayar amman taki d’auka “ciwon abun taji sosai bata san meye matsala arayuwarta ba sai da qaddara ta  hadasu ,wani Kiran ne ya shigo aranta tace “duk ka gama kiranka  bazan dauka ba   sai na ganar da kai kuskurenka .
Ahankali duk suka watse suka barta a d’aki ranar yini sukai cikin farinciki bini bini sun shigo dakin dubata har dady yayinda wuni jaguwa yayi yana Kiran number tanwer amman taki d’auka a karshe ma ta kashe wayar  gbdy.”
Haka yayita damunta da kira acikin kwanan biyu ya hanata sakat da batun zubar da ciki ita kuma taki yarda ta fad’a masa ta zubar tun su mumy basu fahimci mai Kiran ba har suka zo suka fahimta haushi kamar ya kashesu ganin tana sauraronsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button