KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

mahaifiyarta da mahaifinta ne suka shigo dakin cike da matsanancin tashin hankali ganinta zaune yasa dukkaninsu suka shiga sauke ajiyar zuciya haɗe da karasowa inda take zaune , suka sakata a tsakiyar su suna binta da kallo yayinda mahaifiyarta ke shafa fuskarta cike da soyayya .

“Tan……..
Tanweer! Meya faru are you alright? Garin yaya haka ta kasance ? I told you ki dinga driving da kula but you don’t want to heed me ,to ga irin ta nan yanzu me….”.
“Zainab!”. Ya Kira sunanta yana kallonta cike da kulawa. Jin yadda ya kira sunanta yasa ta koma ta gyara zamanta batare da ta kara cewa komai ba sai kallon Tanweer da take cike da damuwa .

“Baki ji me Doctor yace ba?”. Ya cigaba da magana, tabe bakinta tayi alamun bata ji dadin maganar tasa ba.

Tanweer na zaune tana saurarsu sai dai tunaninta na kan kyakyawan matashin da idannunta suka nuna mata a wanin da suka gabata , tayi nisa sosai cikin tunaninsa , runtse idannunta tayi inda take ganin abun kamar yanzu yake faruwa pink lips dinsa da sajen fuskarshi yafi komai burgeta, yadda yake motsasu lokacin da Motar ta nufesa.

“To Alhaji inban ji lafiyarta ba nawa zanji? Dan bakasan yadda naji bane yau walh , karka manta ita kadai Allah ya bamu we are bond to be worried when anything happens to her, what if we loose her?”. Ta tambayesa cike da damuwa kamar zatai kuka.
“No!”. Ya fada tare da jan numfashi Kallonsa take da dara-daran idannunta masu kyan gaske dan banda girma daya soma zuwa mata komai nasu iri d’aya ne da Tanweer, har taso tafi Tanweer din kyau.

“Nasha fada miki ki daina irin wannan maganganun dan basu da wani amfani, kibar ma Allah komai babu abunda zai faru da Babynmu Insha Allahu together we will take care of her”. Ya karasa maganar tare da murmushi kan fuskarsa ya riko  hannunta duka yana motsa su cikin nasa.
Lumshe idannunta tayi, hakan ya bashi damar shafar kumatunta ,Bud’e idannunta tayi da sauri tuna d’iyarsu nagun suka sakar ma juna murmushi me sauti.
Kallon Tanweer sukai wacce tayi nisa a duniyar tunani sosai kamar bata gun. ” Hye Tan!”. Momynta ta fad’a lokacin data riko yatsun hannunta cikin nata ?

A tsorace tanwer ta dawo daga duniyar tunanin nata ,saboda tsoro daya shigeta kar ace ta kad’e handsome din nan.

Hawayene suka soma sauka kan kuncinta wanda hakan yasa Dady saurin tashi tsaye daga kan kujerar da yake zaune. “What! Meyasa babyna take kuka? Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!”. Cike da damuwa yake maganar.
“Tanweer meyasa kike zubda da hawaye? Me kike rasa?”. Momy ta jero nata tambayoyin.

Sauka daga kan bed d’in Tanweer tayi da sauri tana share hawayenta taja takalminta data gani a gefe ta saka. Tana shirin fita Momynta ta sha gabanta.
“Momy please, dan Allah kibarni in duba wannan saurayin na kade’shi”. Abunda take fada tana nanatawa kenan, da kyar suka lallabata ta koma ta zauna. “But Momy Da…”.

“Salamu Alaikum”. Sallamar Dr.Mansur suka ji kamar daga sama, daga kai tayi da sauri ta kalleshi.
“Doctor ina mutumin dana kad’e?”. Ta tambaya tare da tsura mishi ido. Kallon ministet alhaji Abubakar dake zaune yana kallonsa yayi ya maida dubansa kan Tanweer wacce tayi narai-narai da idanu tana kallonshi, ya fada’d’a murmushinsa.
“Alhamdulillah Alhaji, yanzu zaku iya tafiya da Dr.Surayyah dan jikin nata da sauki sai magunguna da zaku kar….”.

“Doctor!”. Ta Kuma kiran sunansa wannan karon fuskarta ba walwala sam.

” Tan Baby, why not you forget about all this things bakiyi hiting kowa ba, ke kadai aka kawo hospital and you are the only one that got injured so kiyi hakuri calm down my baby”. Momy tafada tana dan matsa hannunta cike da kulawa.
“But Mo…”.
“No But Tanweer, maman ki gaskiya ta fada miki ba wanda kika buge and karki manta kece mai wannan asibiti din a matsayinki karkiyi spoiling dinshi da irin wadan nan abubuwan kinji”. Mahaifinta ya k’arasa yana mata murmushi.

Yatsina face dinta tayi nan ta soma tunanin ko gamo tayi dan ita da gaske taga lokacin da tayi hitting dinsa, sai dai Kuma su duka bazasu mata karyaba.
“Oh my first day is terrible”. Ta fada lokacin data koma da baya ta kwanta kan bed din tare da rike kanta.
“But you did well, dan hospital d’in nan sai maganar ki ake kinyi matuk’ar bamu mamaki you know so much about your work gaskiya Allah dai ya taimaka ya k’aro mana irin ku a wannan k’asar tamu”. Dr. Mansur ya fada cike da fara’a.

“Wow that’s good! Dole muje gida ayi celebrating d’in wannan ranar”. Alh.Abubakar ya fada cike da jin dad’in kalaman dr.Mansur.
“But Dady nayi accident fa”.
“So what? We will still celebrate this day tunda you are safe Alhamdulillah.

Nan Dr.Mansur yayi rubuce-rubucensa ya basu sukai sallama, kiran Nurse yayi ta karba dan karbo musu drugs din kafin su shirya. Cikin kankanin lokaci suka bar hospital suka nufi gidansu.

Duk yadda minister yaso ayi celebrating tanweer taki hasalima zamanta tayi a daki akan stool tana kallon window batare da tasan me take tunani ba ji tayi an tabata a firgice ta juyo ta kalli bayanta Ibrahim ta gani tsaye ……

DARLING’S????????????????????????
KUSKUREN BAYA
     ????????????????
????????????????????????

    WRITING BY
BAGUDO& MIMI’S QUEEN
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

????️02

A firgice ta juyo  Ibrahim ta  gani tsaye a bayanta yana sakar  mata  murmushi, ta yatsina  face d’inta  tana kauda  kanta gefe ,tsaye yayi yana kallonta gabansa na wani irin  fad’uwa, musamman daya tuna shine  dalilin accident din da tayi.
     Cike da sanyin jiki ya k’ara matsowa daf da ita ya rage tsawonsa har tana iya jin karar bugun zuciyarsa da hucin numfashinsa  a gefenta, runtse idannunta tayi ta juyo zata mishi magana karaf idanunsu  ya tsarke cikin juna  har saida hancinsu ya  da’n gogi  juna.

Tsura ma juna idanu sukai kafin daga baya  tayi ko’karin da’uke kanta shima yaso yin hakan sai dai ya kasa aiwatarwa,  sake juyo daita yayi akayi rashin saa hancinsu ya goge juna kanta ya bugi goshinsa  . “Ouch!”. Ta furta a hankali cikin Jin zafi ta kai hannunta kan bandage din dake zagaye a kanta.

“So…sor…sorry!”. Ya fada a rikice , ta  tsura masa Ido  tare da lumshe masa Ido tana radadi  , idannunsa ya runtse Shima  kamar ciwon a kanshi yake , ware idannunta tayi a hankali tana kallon yadda duk yabi ya rud’e yake bata hakuri a natse ta samu guri ta zauna  tuni  Shima gwiwowinsa suka   mazauni a gabanta  Yana kallonta kmr ranar ya fara ganinta .

          “I.B!”. Ta Kira sunansa cikin sassanyar  muryarta  kamar yadda ta saba kiransa, lokaci guda ya d’ago rinannun idannunsa ya zuba mata Yana  kallonta itama shi take kallo cike da tsananin tausayawa.”Tan I am really really sorry for causing you so much troubles on your special  day”. Ya fada yana kallonta cike da kulawa da nuna lallai yana nufin abunda yake furta mata har cikin  ransa.

Lumshe idannunta tayi ta bud’e a hankali  ” Hey is not your fault kawai haka Allah ya tsara karka yi blaming d’in kanka akan accident din Dana samu “. Ta fad’a tare da kauda kanta gefe  dan ko kada’n batason ganin irin wannan yanayin nasa , dan yana karya mata zuciya .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button