KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Dare  ya  raba bacci yaki  zama cikin  kwayar   idanun jaguwa  saboda zafi biyu  sun  had’e masa takura masa akan auren  hasera  da amminsa  take so ga Kuma takaicin kin zubar da cikin da tanwer tayi uwa uba tsakin data had’a mashi dashi har yanzu abun nayi masa zafi a zuciya  idan ya tuna kalamanta ya kanji kamar ya mutu wai shi ne zai haifi magajin fashi ?”
Idanunshi suka cika da hawaye amman ya danne .
haka ya wayi gari da rashin  bacci shiyasa da  gari ya waye yake ta  jin kasala ajikinsa.
Shigowar  Anas  yasa ya dan ji dama  ya  dan mike ya zauna rigingine dan yasan dole zai dawo dashi daidai “mutumina ina  fatan dai lafiya ba wata matsalar bace ?”
naunayyen ajiyar zuciya ya sauke yace “matsaloli ne ba matsala Kawai ba, sai dai fatan samun sauki daga Allah .
“ammi ta matsa lallai sai an saka ranar aurena da haseera  karshen watan  nan  da zara an gama bikin Shafik  kenan ,ga matsalar yarinyar nan wai  ni tanwer zata wa haka ina bata umarni tana wani butsarewa wai har da cewa bazata cire ciki ba zata haifa ko na kar’ba ko ta Kawo wa ammi,” ni ba kaiwa ammi  ne ma yafi damuna ba wai ta haifar min wanda zai gajeni a fashi ba sai nayi training yayan wasu ba ,wallahi wannan abu yayi min ciwo ko ance mata wannan sana’ar muna yinta ne dn  dadin rai ?”
“Kana ji ko muyi magana ta fahimtar juna  Allah  kuma  yasa ka saurarrni ,Jaguwa ya kara matsoshi sosai”me zai hana Anas ka fad’a komai zan saurara dan mafuta yake  nema tun kafin komai ya kwabe masa  .”

“Abinda kakewa yarinyar nan Sam bai da kyau , duk fa kai ka jawo abinda ta fad’a maka ba wai wulakanci tayi maka ba ,sai abu na gaba adnan Kana yiwa yarinyar nan wani so na dabam haka  itama  tana sonka sosai fiyye da komai irin son da zata iya rabuwa da Kowa nata dan ta rayu da kai  hasalima soyayyar da take  maka ne yasa ta kasa zubar da cikinka ba wai ina takura maka  akan  kana son yarinyar  nan bane ,sai dai   ina son ka sani  har abada bazaka daina sonta ba , itama  haka . zanyi farinciki idan ka sauke komai ka rungumeta ka aureta , nasan muddin  iyayenka sukaje  neman aurenta  zata yarda ta zubar da cikin duk da shima zubar da cikin babban laifi ne .
Jaguwa ya numfasa tausayin kansa dana tanwer ya rufesa tabbas shima ya fara jin wani abu akanta a yanzu ma babu abinda yake gani acikin kwayar idanunshi sai hotunanta , yayi saurin ya bud’e idanunshi da suka kada “kayi hakuri wannan shawarar taka ba abar d’auka bace yanzu agurina kasan komai nawa Koda zanyi aure bazan Iya aurar mace sama da daya ba ,” kaga Kenan bazan iya bin zabin Kowa ba sai na mahaifiyata dan haka maganar auren tanwer ma bata taso ba  ka bani wata shawarar yadda zanyi ta cire cikin nan dan ko bata samu hanyar kaiwa mahaifiyata ba ta cuceni muddin ta bari dana Ko y’ata sukazo duniya  ta wannan hanyar .”
“Komai fa muqaddari ne  daga Allah amman ka sake lallabata ka gani may be zata yarda  “babu irin abinda ban mata ba anas  babu irin  rarrashin da ban mata ba  ingaya maka yarinyar nan taki d’an Karan taurin kai gareta ,anas yayi murmshi yace “zanice ta tarar da muje kai daita duk abu daya kenan ” sun dade suna magana akan cikin tanweer a karshe ya tsaida shawarar zai nemota da kanshi ya kaita acire mata cikin ya huta da damuwar dake damun zuciyarsa.”


Tunda yaran alhj Tahir suka Kawo masa labarin rashin nasarar da suka samu gurin kashe nazifi ya kasa samun sukuni, ranar a zaune ya kwana saboda tsananin tashin hankali addua yake Allah yasa ba hannun Jamin tsaro nazifi  ya shiga ba .
haka ya raya daren batare daya runtsa ba haka washegari tsumayi yake yaji ta inda za’a aiko masa da sammaci amman shiru kake ji ,haka yayi kwana biyu adaddafe duk ya zube Kamar wanda yayi shekara yana ciwo  baya Iya  zuwa  koina ganin har lokaci babu wani sammaci daga hukumar yansanda ya dan kwantar da hankalinsa .
Yau ta kama jumma’a   alhj Tahir yaje massalacin sallar jumma’a kai tsaye daga massalacin gidansa ya nufo shi direbansa Sai dai kafin ya karaso get din gidansa wata mota marcende tasha gaban motarsa take direbansa ya tsaya cak cikin tsananin tashin hankali .
wasu mutane masu siffar karfi da bai san ko suwaye ba fuskokinsu rufe da bakin face mark sukai attacking dinsu. duniya juyi juyi yau shi akayi attack shi da yake  turawa mutane fataken dare yau Shi aka turowa ,hankalinsa bai wani tashi ba a tunaninsa kudi sukazo nema sai dai yadda suka karaso tamkar zakuna suka hau bud’e kofar inda yake zaune a gidan baya suna cewa “fito muje shine yasa cikinsa ya turu ruwa “ya fito suje ina ?”yayiwa kanshi tmbyr a kasan ransa ,amman a zahiri cewa yayi “nasan kudi ne ya Kawo gani ga gidana can tafiyar mintuna kadan zai kai mu muje zan baku duk abinda kuke bukata ni dai ku barni da raina.”

“ba kudi ya kawomu gurinka ba cewa akayi muzo da kai Idan kaki biyo mu mu d’auki ranka” nan take jikin alhj Tahir ya d’auki kyarma kmr mazari yana zare Ido gaba da gabanta kenan, bai tsaya bata musu lokaci ba ya fito yana gyara babban rigarsa suka tasa keyarsa gaba har gurin matarsu suka saka shi a gidan baya mutun biyu suka sakashi a tsakiyar suka bar gurin aguje.. suna barin gurin direbansa ya fito tare da daura hannuwansa duka saman kanshi yana kururuwa neman d’auki ya bi bayansu sai dai akin banza yayi dan babu wanda ya fito ,daman kuma haka unguwar take duk abinda zai samu mutun da wuya ataimaka masa kuwarka banza barinsa ma haka .”


9:am daidai motar jaguwa ta karaso bakin get din  asibitin tanwer , yayi parking nesa kad’an da asibiti  yana zaune sai ga  direbanta yazo da wata  hadadiyar mota Kirar  land cruiser jeep sai sheki take .
tun daga nesa ya tsura mata Ido fuskarta a had’e tamkar bata ta’ba  murmushi ba sai dai yanayinta kamar zatayi kuka tayi masa kyau aini yaushe rabon ya sanyata akwayar idanunshi .
 driver ya sa kai zuwa cikin hospital din shima ya biyo bayansu , direba bai tsaya akoina ba sai a daidai hanyar da zata Kaita office dinta  yayi parking ya fito da sauri  ya bud’e mata gidan baya .
A hankali ta yunkura ta fito tana jin wani faduwar gaba ……”
ta tsaya shiru tana bin haraban gurin da kallo kafin daga bisani ta soma d’aga kafafunta zuwa ciki yayinda driver ya Shiga motar ya tayar ya soma k’okarin barin gurin .

Tana tafiya tana sake jin faduwar gaba tare da jin motsin tafiya a bayanta ta tsaya cak ta juyo bayanta a natse wayam babu Kowa sai ita kad’ai sai mutanen Dake kai Kawo ta gabanta ta cigaba da tafiya adaidai bakin corridor da zai Kaita office dinta suka hadu da doctor muyis cike da fara’a ta tsaya suka gaisa yana k’okarin janta da magana ta wuce ganin fara’a a fuskarta yau yasa shi jin sanyi aranshi dan haka yabiyota abaya  har ta karaso bakin kofar office dinta bata daina jin faduwar gaba ta tsaya tana k’okarin   bud’e  jakarta ta ciro key  Dr muyis ya amshi jakar hannunta dan ta Samu damar  bud’e kofar a tare suka  Shiga ya maida kofar ya rufe batare da yasa key ba .
Ya ajiye Jakarta akan makeken table din dake office din ta  zagaya ta zauna shima ya samu guri ya zauna suna fuskatar juna office din ya dauki shiru na minti goma sannan ya fara magana zuciyarsa na rawa dan fargaba. “jiya  dr Safina bata fad’a miki sakona bane ?” sai da tayi jim sannan tace “sakon me Kenan ?tayi mgnr batare da ta d’ago ba. ya gyara zama yana sakar mata murmushin sai lokacin ta d’ago ta dubeshi suka had’a Ido
“ya’akayi Dr muyis ?”yace “babu komai Kawai so nake muyi hira “ta sauke numfashi tana cewa “Ai yanzu ba lokacin hira bane lokaci ne na aiki zai fi kyau ka kama gabanka kaje kayi aikin gabanka” ta maida Kanta ta sunkuyar tare da numfasawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button