KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

duk  suka  zuba  mata  idanunsu suna kallonta  kowa da abinda yake sakawa a cikin  ransa a hankali  jaguwa ya runtse  idanunshi tare da Kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da sauri sauri ,anas ne yayi karfin halin tambayarsa abinda ke faruwa daita “daman itace babu Lafiya me ya sameta ?”aikin wancan tsinanniyar yarinya ce ya fad’a a tsawace “wacce yarinya kenan ?anas ya tambayesa a rud’e “wace ce banda waccen yar iskan zahra din asiri tayiwa yarinyar mutane amman na rantse da Allah sai naci ubanta inga uban daya tsaya mata acikin garin nan”take it easy jaguwa Kai ya akayi kasan tayi mata asiri ? tsaki jaguwa yaja da karfi idanunshi na kan tanweer dan yasan daman haka zai ce tunda baya ganin laifinta  .
a tsanake jabir yace “Allah ya kyauta yanzu dai me ye solution dan  naga kmr yarinyar bata numfashi ?ga tan nan dai tana numfashin sai dai ba sosai ba da kyar na samu numfashinta ya dan dawo wallahi muddin wani abu ya ta’ba lafiyarta zan shayar da Zahra mamaki inji cewar jaguwa ,gyada kai suka yi  gbdy sannan jubi , jabir ,kamil suka juya suka fita daga d’akin dan babu me iyawa dashi idan yana cikin fushi sai anas .”

“kayi hakuri jaguwa ba lallai abinda kake zargi akan zahra  ta aikata ba anas yayi mgnr yana dafashi a fusace ya buge masa hanun yana cewa “Daman nasan haka zakace  tunda kafi qaunar dani “no !no !! jaguwa saboda qaunar da zahra take maka yasa nake kulata taya ma zaka had’a matsayinka daita gsky karka sake min hk banaso Kai fa jinin jikina ne  ita Kuwa fa ?  jaguwa yayi shiru tare da  tsurawa tanweer Idanunshi wasu kwalla masu zafi suka zubo akan kuncinsa cike  da  takaici da nadamar abinda ya aikata mata, nadama irin wacce bata da amfani .
anas yayi matukar mamaki ganin jaguwa ya tasa tanweer gaba yana kwalla “lallai haka rayuwa take tana cike da abun mamaki “jaguwa ne yau yake kuka akan mace ? “Jaguwa !
Anas ya kira sunansa “yana jinsa yayi masa banza tamkar ba dashi yake mgn ba ” kana mutuwar son yarinyar nan amman Kaki yarda da kana sonta , Kalli yadda kake zubar da hawaye akanta ,Kalli yadda tausayi mai hade da soyayya suke dawainiya da Kai ,ka yarda jaguwa kana sonta ka daina karyata zuciyarka , ka daina hasashen bazaka iya sonta ba, ita fa rayuwa kafi ni sanin rubutaccen alamari ne daga rabbi, hatta wannan Sana’ar tamu qaddara ce Killa da iyayenmu sun san zamu zo duniya mu kasance yan fashi wallahi da tuni sun kashemu da hannunsu “.yayi shiru yana dubansa “ka yarda Kuma ka amince kana sonta sai mu taru mu bar wannan rayuwar ,zamu tayaka inganta rayuwarka jaguwa domin sama maka farinciki ……….”
“ka daina fad’a min haka anas banaso ji wannan kalmar  daga bakinka sau nawa zan fada maka tausayi ne ba so ba ?”yayi saurin karyata amininsa taya ma zai sota byn tanweer tafi karfinsa a aure, waye shi ,? waye yan’uwansa a fad’in kasar nan ?
duk da a yanzu ya taka matsayin da kudi ba matsalarsa bane amman yasan aurenta zai masa wahala, ya sake fuskantarta sosai yana Jin kamar yayi mata numfashi ,sosai  ya  fad’a kogin tunani hankalinsa ya bar duniyar da yake ciki ya Lula wata duniyar dabam .”

“Bamu saba boyewa kanmu komai Daya shafi rayuwarmu ba ,jabir, jubi kamil ,duk tare suka ganmu kana fada min  gaskiyar dake cikin zuciyarka akan komai amman akan wannan yarinyar ne kawai ka kasa fad’a min matsayinta a zuciyarka ,kana tunanin zan hanaka soyayya ne da ita ko me?wallahi kamar yadda kaji na fada maka ni me rungumar komai ne akanka Koda kuwa mutuwa ce, Ina maka soyayyar da zan iya sadaukar da rayuwata akanka, karka manta mu din masoyan juna ne da muka yarda da juna Kuma muke son juna saboda Allah, zuciyata ta yarda ta amince kana son yarinyar nan so me tsanani ko dan tana diyar minister yasa kake gudun fallasa sirrin soyayyarka ?
“ko d’aya  bana  dai sonta ne ” kama saukakawa kanka nan kusa ma ammi zata min mata ka san kuwa zuciyata bata da wani zabi daya wuce nata dan haka ka cire wannan tunanin a ranka ya k’arasa maganar still idanunshi na kanta ” yana dasa Aya anas ya juya a hankali ransa a matukar bace.

“ta yaya gashi yana kallon tsagwaron qaunar yarinyar a idanunshi amman yake ja inja dashi ? ranar ce rana ta farko da jaguwa yayi masa abinda   har yaji ya tsaya masa arai , Jin motsin Bude  kofar d’akin ya sa jaguwa ya waigo da Kansa anas ya gani zai fita daga d’akin shima kmr ya bar d’akin sai ya tsinci Kansa da kasa aiwatar da hakan yaji bazai iya barinta ita kad’ai ba dan haka ya hau gadon ya janyota ya d’aurata a saman  faffadan qirjinsa, a hankali  yana shafa bayanta, ajiyar zuciya ta fara jerawa tamkar wacce ta sha gudu tsira  ,qara   makaleta jaguwa  yayi   tamkar  wani zai kwaceta a hannunsa “Anya   kuwa adnan  baka  fara  son yarinyar nan ba ?” ya  tambayi kanshi yana shinshina wuyanta” ka fara sonta mana tunda kana tsananin qaunar kasancewa daita zuciyarsa ta bashi amsa da hakan  “Ina  ba  haka bane tausayi ne kawai babu wannan a tsakanina daita ,gyara mata kwanciya yayi sosai ta yadda bazata takura ba ya sauko daga kan gadon zai fita yaji ta riko hannunsa waiwayota yayi zuciyarsa na dokawa da matsanacin karfi ya kalleta sosai bacci take da alamun ma bata san ta aikata hakan ba , ya fito daga d’akin zuwa bedroom dinsa kana ganinsa kasan baya cikin haiyacinsa zama yayi yana neman layin sadiq ya kira sakamakon ganin missed calls  dinsa ya d’auka yana d’auka yace “father komai normal dai ko ka Isa gida lfy ? “Normal sadiq komai  daidai na gode da kulawarka dan uwana , sukai sallama kmr ya nemi layin zahra dan yasan adaidai wannan lokacin idanunta biyu Killa ma tana can yawon ta zubar amman ya share yana zaune  zata zo ta samesa ..”

Can  bangaren  IPO  kuwa  yana ganin dawowar jaguwa yasan sun yi missing dinsa wayarsa ya ciro ya shiga neman number dcp baba abare  yana d’auka yace “sir Kuna Ina ne  ? daga can bangaren dcp yace muna kan titi har yanzu bamu ga dawowarsa  ba “gsky kunyi missing dinsa dan ya dawo gida “shit ….” dcp ya furta a fusace sannan ya cigaba da magana “amman a juri zuwa rafi wata rana tulun zai fashe “wannan haka ne sir idan kere na yawo zabo na yawo  wata rana zasu  had’u ne “,ai kuwa haduwarmu bazata yi kyau ba dan bazan Kai shi ga office din  hukuma ba bare a samu damar bada belinsa tarwatsa masa Kai zanyi kowa ya huta yana gama fad’ar haka ya katse Kiran a fusace  yana bawa yaransa umarni .”


Washegari da misalin karfe takwas ya fito zuwa falonsa sanye cikin gajeren trouser  baki da riga fara mai hula da ratsin baki ,sanye da takalmi fari mai azaban kyau yayi kyau sosai sai dai fuskar nan tashi a murtuke tamkar jinin sarauta sannan kallo d’aya zaka masa kasan zuciyarsa a dagule take jira kawai yake a tabashi ya hau mutun , ya d’auki remut ya kunna tv ya Kai  chennel  zuwa na labarai  yana ƙoƙarin  zama friends dinsa suka shigo suka zagayesa har kamil Suma cikin shiga ta alfarma atare suka had’a baki gurin cewa”ya lafiyar yarinyar nan ?Kamar bazai ce Komai ba har sun fidda rai da zai Yi mgn suka ji yace “alhamdulillah har yanzu dai tana bacci  “.Shiru sukayi dukkaninsu babu wanda ya sake yin magana sai numfashi da suke fitarwa idanunsu na kan tv yayinda  anas ke son yi magana akan zahra zata zo dan tun safe ya kirata ya sheida mata abinda ke faruwa  sosai ta daga hankalinta  ,amman yadda yaga jaguwa ya had’e rai yasa ya kama Kansa ya ciro kwandala  a cikin aljihunsa ya murza akan center table din dake gabansa  take ta fara juyi a karshe ta kife ya tsurawa kwadalar Ido kawai yana kallonta  .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button