KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

A tare jaguwa da eku suka karaso gida gbdynsu babu wanda bai yi mamaki  ganin Scorpion dan basusa rai zai fito acikin kwana daya ba ,lokacin da jaguwa ya fad’a musu abinda yayi kafin scorpion ya dawo sunyi matukar jinjina masa,a daren ya  kira likitansa tazo tayi masa allura ta rubuta masa magani sannan eku ya taimaka masa ya shiga bayi yayi wanka dan jikinsa Kmr  gyenbo yake jinsa.
kwana daya kawai da yayi a hannun police yaji kamar kwanaki dubu yayi ya kalli jaguwa da idanunshi daya kunbura “police basu da Imani a gobe suke shirin min izaya ta karshe duk da bansan wacce irin izayya zasu min ba a fadar wani police naji tsoro ya kamani .”tausayinsa ya kama jaguwa  muddin ina raye bazaku tagayyara ba kwana sukayi suna hirar irin azabar da akayiwa scorpion.”

washegari Ana’s yazo  shima yayi matukar murna da dawowar scorpion “su jaguwa na jin dadin su a gida yayinda headquarter ta hargitse da gulmace gulmace na neman scorpion da akayi aka rasa “akwai wani abu guda daya dana rigada na  yarda dashi yanzu
Commissioner  da mataimakinsa suna da  saka hannu acikin abinda ya  faru “me yasa ka fadi haka ? Inji asp isa .Dcp yace “yaron  dan fashin guda aka kama amman dan an raina mana hankali aka nemi commissioner aka rasa bayan awa shida aka nemi scorpion tare da mataimakin commissioner aka rasa  sannan bayan wasu awanni aka sako commissioner wannan kawai ya tabbatar min dole akwai hadin bakinsu ,kowa fa yanzu su  yake tunhuma ,mu kasa kunne muji ne ig zai ce amman lallai nasan sai an tuhumesu.”


Bayan sati daya

Jaguwa na zaune a dakinsa sanye da wondo baki da Riga baki mai hula yana duba wasu takardu masu matukar mahimanci kawai yaga an turo kofar dakinsa an shigo ya dago kanshi  a hankali  ya kalli   Kofar tanwer ya gani tsaye  yana ganin itace ya dauke kansa  ta karaso ta zauna gefensa ya mike zai wuce ta riko hannunsa da sauri “please adnan ka tsaya kaji me ya kawo ni, banza yayi mata ya fixge hannunsa ya cigaba da tafiya ta biyosa tana nasa mgn “wai me yasa kake min haka ne ?
“Bansani ba amman  banason na tsaya dake bare nayi magana dake ,saboda ka tsaneni ko?duk ma yadda kika dauka haka ne kar kuma ki manta nace karki sake zuwa inda nake me ya kawoki yanzu ?
“Na kasa samun kwanciyar hankali ,wallahi ina cikin  wani hali  akan fushin da kake yi dani ,Idan kina cikin wani hali ina ruwana  me zan miki karki sake fad’a min cewar kina cikin wani hali akaina wannnan sakaran zaki fadawa bani ba  .”

Zagayowa tayi ta kwanta a gadon abanyasa ta daura hannuwanta a daidai qirjinsa dake bugawa a tun shigowarta dakin  ,kayi hakuri adnan dina nasan ban kyauta maka ba  tana magana tana shafa qirjinsa ,”
amman kai ma kasan daga ni har kai muke da laifi , da tsayuwar da kayi kana fad’a min mgn a gaban dr da daukata kayi ka tafi dani ka yanke min duk hukunci daya dace bazan damu ba amman a gaban dr ko wasu bazan ji …”
Riko hannunta yayi tare da fixgota ta dawo  gabansa suna fuskarta juna atare suka sauke numfashi  ta matso shi sosai ta zagaye wuyansa da hannunta daya yayinda dayan hannunta ke fama shafa fuskarsa zuwa faffadan qirjinsa tana kokarin kai bakinta kan nashi ya kawar da fuskarsa gefe ya rike hannuta dake qirjinsa da wanda ke wuyansa  ya soma tafiya daita har ya isa jikin bango ya mannata still kokarin matso shi take ta hade bakinsu domin tasan suna haduwa guri daya shikenan fushin da yake yi daita ya  kare amman yaki yarda .

“wannan bakin yafi karfinki yanzu sai dai wata .” yana gama fadar haka ya sakar mata hannu ya nufi kofar fita tabi bayansa da kallo qirjinta na dokawa da karfi har ya fice daga dakin idanunta na kallon kofa taji kamar tasa kuka ta runtse idanunta tana kokarin danne damuwarta amman sai da kwalla ta zubo mata, a qalla ta dauki sama da minti goma tsaye idanunta a runtse suna tsiyayar hawaye sannan ta budesu suka sauka akan gadonsa inda takardu da yake aiki akansu suke zube  .”
Jikinta a sanyaye ta karasa inda takardun suke zube ta soma dubawa a irin haka ta san alhji tahir ne ya aikosu  gidansu domin fashi wa mahaifinta dukkanin ayyukansa suna rubuce kuma tare da hotunan mutanen da yayi wa aiki a hankali ta soma dubawa cikin haka ya dawo dakin tana ganinsa tayi saurin ture takardun ta mike tsaye yaja tsaki sannan ya nuna mata kofa da babban yatsansa “out !.”
Ta mike tsaye ta dauki jakarta ta rataya  tana jan tsaki  “aikin banza kawai dan kaga na damu da kai shine kake wulakantani daga yau bazan sake zuwa inda kake ba kaje ka auri duk wacce kake so bazan damu ba “daidai kenan na kuma ji dadi da kika yankewa kanki shawara me kyau nima kuma na huta da naci .”

“Allah ya saka min cutar da kayi min bazan taba yafe maka ba mayaudari kuma makaryaci kawai , me muguwar zuciya har ta juya tana kuka ya riko hannunta ya dawo daita jikinsa yana kallon fuskarta da hawayen dake tsiyaya a idanunta “ni ne mayaudari tanwe ? Me yasa kika kirani da wannan kalmar ?tayi masa banza tana kokarin zare jikinta ya rike kugunta sosai “me lie tanwer ?kiyi bude baki ki min magana dont think am play with you ,”Who is playing with you too? bai yi mamaki dan yasan zata iya fiyye da haka .”

“You also call me makaryaci karya me nayi miki ? “bansani ba ka sakeni na kama gabanaba ,sai ka qara gani na arayuwarka sannan zaka cigaba da wulakantani “All these you can’t happy if they call you that and you are calling me mayaudari makaryaci why ?dan ban amincewa soyayyarki ba shine na zama makaryaci mayaudari me muguwar zuciya “?tsaki taja ta fixge jikinta ta fita da sauri murmushin gefe baki yayi yana cewa “tanwer kenan bazaki gane ba allah ya tsareki ,kamar wasa gbdy cikin kwanacinki tanwer bata kira shi ba sai kuma yaji ya kasa samu natsuwa a qalla sai da yayi kwana goma bai ga kiranta ba ko kiransa akayi yana allah ya duba ya gani ko itace sai yaga ba ita bace ya shiga damuwa sosai sai dai ya danne .”


Sannu a hankali scorpion ya samu sauki ya dawo tamkar yadda yake babu inda baya zuwa Adaidai wannan lokacin suka  samu sakon gayyata daga nabel  saboda suyi aiki dashi  ,nabel jami’in tsaro ne da kasa take alfahari dashi  kuma rikakken dan ta’adan  ne da yan taada ke ji dashi ,shi kansa dila ne na safarar miyagun kwayoyi uniform dinsa ne kawai ke rufe da asirinsa , akarkashinsa akwai jami’an tsoron da suke attare dashi ciki har da shugaba efcc gashi mugu ne na karshe bashi da Imani abu kadan idan kayi masa zai aikaka lahira baya yafiya .”sai byn da jaguwa da Ana’s suka zo suka fahimci bikin cikar shekararsa ake yi dan haka suka samu guri suka zauna suna kallon manya masu kudi na garin lagos ,da kusoshin gwanati dake shigowa  sai dai har lokacin nabel bai samu damar shigowa ba .”

tsaye nabel  yake cikin fararen suit yayinda gbdy yaransa ke tsaye cikin suit bakake , wani mutun tsaye a gefensa yana kuka yana bashi hakuri amman ko kallonsa bai yi ba ya kai Karan sigari bakinsa ya kunna ciki muryar kuka wannan mutumin yace “ranka ya dade dan allah ka taimakeni nasan nayi maka alkwarin bazan sake fita da sirrinka ba wannan ma Kuskuren né ka taimakeni ka gafarceni ya fada yana goge hawayensa “duk mutumin da bai yi Kuskuren ba bazai taba yin kuka ba .”
nan take mutumin ya fara dariya “ranka ya dade ai ba kuka nake yi ba  gashi ina dariya ” duk mutumin da bai yi Kuskuren ba tô bazai tabayin dariya da wuri haka ba, yana gama fadar haka ya soma tafiya wasu daga cikin yaransa suka biyosa ciki har da mutumin dake kuka ,cikin sauri mutun daya acikinsu ya bude masa kofa mutumin ya biyosa yana kuka ” ni yanzu ranka ya dade ka fada min me zan maka ka huce abinda nayi maka lokaci “ni a yanzu babu abinda zan ka iya min nima kuma babu abinda zan maka yayi mgnr yana turesa  da hannunsa “kar ka sake bina rayuwarka tazo karshe ya wucewarsa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button