KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Washegari ta shigo d’akinsa bakinta d’auke da sallama yana kwance a akan doguwar kujera a falonsa dan tun bayan daya dawo sallah asuba yake kwance agurin ta ra’be gefe guda tana dubansa ,a hankali ta k’arasa ta tsugunna a gabansa tana kallon gefen fuskarsa Inda ta maresa ,saukar numfashinta akan fuskarsa yasa shi bude Ido eyes to eye’s suke kallon juna “sorry for my active kayi hakuri nasan har yanzu kana fushi dani “ya juya mata baya yana jan tsaki ta sake matsowa sosai ta Kai hannunta jikinsa ya buge mata hannu da karfi ta rike hannunta tana runtse idanunta dan taji zafi sosai har cikin ranta taji dukan .
take gumi ya shiga tsatsafo mata a goshi da karan hancinta muryarta a shagwa’ba tace “yanzu bazaka yafe min ba ?banza yayi mata kamar bai san da wani halitta agurin ba “ki tashi ki bar d’akin nan tun kafin na tashi nayi miki abinda banyi niyya ba . “ka yarda nayi nadama “dan ubanki karkiyi nadama maza ki tashi ki bar d’aki ya fad’a yana mikewa tsaye da sauri itama ta mike tsaye”oya out of this room “dan murmushi gefen baki tayi tare da matsoshi sosai ta rungumeshi tsam ajikinta kamar za’a kwace mata shi, jinta ajikinsa yasa shi Jin wani iri muguwar kasala ,tayi lif a faffadan qirjinsa tana shakar numfashinsa da kamshi turarensa me d’aga hankali.
a hankali kowannensu ke sauke ajiyar zuciya muryarta a matukar sanyaye tace “karka sake zagin ubana ko zan d’auki komai ban da zagin mahaifina ka kiyaye harshenka ” shiru tayi tana jiran abinda zai ce hannusa yasa ya zareta ajikinsa “tunda shine abinda kika fi tsana daga yau shi zan dinga fada miki “zan kuwa rama tunda uba bai fi ba “bar d’akin nan ya fada a fusace yana nuna mata kofa “karki sake shigo min daki “Kai ma haka karka sake zuwa Inda nake “wai ni sa’anki ne da ina fada kina fad’a?yayi mgnr a matukar hassale yana kokari damkota ta zame tayi baya da sauri tare da yi masa gwalo da karkad’a masa kunnuwanta.
tsura mata tsumammun idanunshi yayi kawai ya kasa cewa komai taku d’aya yayi ta kwasa da gudu ta bar d’akin ya ja dogon tsaki “zanyi maganinki ne .”Tun daga ranar bai sake shigowa Inda take ba hatta abinci ya daina kawo mata , lura da so yake yayi punishing dinta da yunwa yasa hankalinta ya tashi sosai ta shiga damuwar halin da zata shiga idan ta wuce kwana daya nan gaba batare data sakawa cikinta wani abu ba .

Sai da yayi kwana biyar yana fushi daita sannan ya sauko ya shigo domin kawo mata abinci ya ajiye mata farar leda zai fita tace “malam ka dawo ka d’auki abincinka bana ci duk kwanakin nan da baka kawo min abincin ba na mutu ne ?”ban mutu ba dan haka ka dauki kayanka ba zanci ba zan cigaba da zama haka har na bar gidan nan.
wani murmushin gefen baki yayi sannan ya juyo ya fuskanceta sosai yaga ta rame acikin kwanakin da yayi bata ci komai ba taku d’aya ya K’ara ya fara mgn cike da dakiyar zuciya “Kinga rashin cin abincinki ko rashin walwarki bazata dameni ba ,saboda bana sonki bakya cikin rayuwata bakya gabana ,kisan Allah ko nemanki na sake yi na rasa yanzu bazan damu ba saboda na lura baki da mutunci, bakida kirki ,baki da biyayya biki san komai ba sai zallar rashin kunya ,ada Ina matukar jin tausayinki da gudun abinda zai cutar dake amman a yanzu duk babu wannan , zan cigaba da rikeki ne dan na musguna miki dan fahimci kina qaunar komawa gida kamar yadda kike qaunar rayuwarki”. yana dasa aya ta fashe da kuka tana cewa “Allah ya Saka min wallahi sai hakina ya bibiyi rayuwarka ni wallahi dama kasheni kayi na huta .
“bazan kasheki ba zaki zauna ki cigaba da ganin rayuwa a gidan nan , sannan babu abinda zai bibiye rayuwata bakinki bazai kamani ba danke ba uwata bace
yana gama fad’ar haka ya fice daga dakin ya barta tana kuka yana fita ta hau share hawayenta da hannuwanta duka ta Isa Inda ledar takeway yake ta bud’e ta fito da takeway jikinta har rawa yake ta soma cin abincin tana zubar da hawaye .”

jaguwa na fita daga d’akin gidan ya bari gbdy zuwa asibiti Kai ziyara sai dai tafiya kad’an yayi ya fahimci ana binsa abaya , ilai kuwa yana duba mirrow din motarsa dcp lawan numan ya gani zaune yana biye dashi nan take ya qara gudu shima ya biyosa a guje sunyi tafiya me nesa dcp na biye dashi daf da zai sha gaban jaguwa ya ciro bindigar ya harbi tayar motar dcp cak motar ta tsaya daga mugun gudun da take Allah ya taimakesa motar bata hantsila ba , yaja tsaki yana cewa zaku rasa ranku akaina idan baku daina bibiyata ba ya canza hanya ya cigaba da tafiya yana sauke numfashi .”
Cike da rashin kuzari dcp ya dawo office ya tara yaransa gbdy ya Kalli Inda babban yaronsa yake zaune “meye nazarinka akan wannan lamarin na kwamushe diyar minister da danfashin nan yayi yaki dawo daita sannan yaki bukatar komai daga hannun iyayenta ?”ni fa bansan abinda zance ba wannan lamari yafi karfin tunanina” kana ganin shigowar yan fashi gidan minister hakan bashi da halaka dana jikin minister ?
“Nima na fara tunanin akwai saka hannun wani dake tare da minister dan mutun abun tsoro ne zasu iya aikata komai amman Kuma bai zama lallai zarginka ya zamo gaskiya ba dan idan da saka hannun wasu zuwa yanzu zamuga alama” “haka ne Kuma nan suka shiga nazari akan abubuwan dake faruwa suna nan zaune har karfe shida kira ya shigo wayar dcp ya d’auka “Yana d’auka sautin jaguwa ya karad’e gurin dake a handsfree ya Saka wayar “barka da yammaci masoyina “masoyinka Kuma ?eh mana masoyina dake bbiyata a duk Inda na Saka kafa kaga dole na kiraka da masoyi yakamata ace kasan Koni wanene shiyasa ma na kiraka na sanar da Kai wani Abu da baka sani ba .

cike da zakuwa dcp yace “Ina jinka a she dai kana bukatar mu tautauna kenan ? ya mike cike da hanzari yana cewa “Ina saurareka me yasa kake aikata abinda kake aikatawa ?”so kake kasan dalilin da yasa nake aikata hakan? dcp ya gyada masa kai kmr yana gabansa ” amman Kuma sanin dalilin ba fa shine me mahimmam ba sanin mahimmam aikina yafi .”
“yanzu har aikin fashi da garkuwar da mutane yana da wani mahimmanci ? Sannan Kai fa masheki ne “kwarai kuwa mahimmancinsa ne ma yasa nake aikata shi da kwarin gwaiwa ,kace masheki a karshen maganarka waye na sheke ?
“ban sani ba amman Kai ai kasan me laifi ne ? “Kenan har yanzu ana kan kirana da me laifi ? Idan ni an kirani da mai laifi su tanko gote da tawagarsa fa me za’a kirasu dashi ? gskiya Kai din mai baseera ne ya kamata na tayaka murna sosai amman meye laifina akan abinda nake aikatawa ?”
“shikenan na yarda baka da laifi amman Ina son na had’u da Kai mu tautaunawa abu me mahimmanci nima yanzu zan goyi banyanka dan nasan akwai jami’an tsaro da dama da suke aiki karkashin ikonka masu kawo maka rahoto akanmu’ “dakata dcp har yanzu ba’a haifi uwar d’an da zai min wayo ba” dcp ya runtse idanunshi yana shafa goshinsa ” ni nan da wayona aka haifeni idan kaga na bar mutun to naga dama ne , dcp ya furzar da iska sannan yace “Kai karka dauka wannan takamar da kake samun sauki ne ko mafuta ,karka manta har yanzu Kai din me laifi ne a kasar nan “na dauka yalla’bai dan ka kirani da me laifi amman kasani masu aikata laifin irin nawa basa ta’ba shiga hannun yansanda domin a idon alumma ba masu laifi bane idan da naso da Kai kanka bazaka iya bincike akaina ba sannan da na kawar da Kai a dazu dan ba tayar motarka zan harba kwakwaluwarka zan fasa .
“ya kamata ka taimaki rayuwarka data iyalinka ka hutar da kanka da tunaninka akaina dan bazaka iya komai ba.”
“ka min shiru barawon banza kawai Kuma me garkuwa da mutane ” yalla’bai ka dai kirani da kwararren d’an fashi wannan nasan Ina yi amman garkuwa da mutane wannan ba aikina bane gurinsu tanko gote zaku samu cikakken bayanai masu yi ,ku daina bibiyata dan ga dukkanin alamun Kuna sa Ina Kara yin suna a duniya kunsa koina acikin garin nan sunan jaguwa kawai ake kira .
“idan aiki kuke bukata karku manta akwai yaran da kullum ake musu fayde sannan akwai yaran da kullum ake maidasu marayu saboda basu da gata arayuwaarsu da talakawan da basu ji ba basu gani ba aka sakasu shiga tashin hankali ,
aikin ne da yakamata Kuna tsaye akansu amman duk kun kasa daukar mataki Kuna zaune a office sanye da uniform din sharri ?”bari Kuji Ina kan zuwa kan aikinsu domin na hukuntasu bisa laifinsu tunda ku cin hanci ya hanaku bawa kasarku tsaron daya dace “.
“Ina ruwanka da wannan bangaren ?baka da hurumin hukunta ko ma wanene dan Kai ba kowa bane tamkar matacce dan kana shigowa hannu mutuwa ce zata tarbeka .
“nasani yalla’bai ni ba kowa bane Kuma duk daren dadewa zan mutu ko baka fad’a ba,Amman kasan da cewa Ina kishin kasata ni d’an kasa ne me kishin Kai Kuma na zabi farinciki al’uma akan mutuwa da komai Kuma zan hukunta azzaluman sannan na kawo karshen rayuwarsu.
“wallahi Kai sheidan ne “kwarai kuwa ka kirani da abinda yafi haka indai akan gaskiyata ne na yarda .”me ! dcp ya fad’a a razane shine dansanda Amman yafi shi shiga tashin hankali.
“Eh tamkar mota haka zamu cigaba da karawa da Kai Amman kasani a koda yaushe Ina gabanka daga nan har izuwa lokacin da zaka gane ba kuskure nake aikatawa ba domin kuwa ko za’a fito da gaskiyar a yanzu bazai shafe KUSKUREN BAYA BA shiru dcp yayi da sauran mutane suna sauraronsa “da zaku gane da Kun daina bincike akaina Ina fatan ka fahimta masoyi “tur da Hali irin naka yanzu yaushe zaka dawo da diyar minis ….”ai kafin ya karasa mgnr yaji kit wayar ta mutu tsaki dcp yaja yace “yanzu kenan bazamu iya kamashi ba ?da alama kam inji cewar daya daga ciki police din dake gurin “aikin banza kama wannan dan fashin dole ne Koda zan rasa rayuwata dole mu cigaba da bibiyarsa tunda da alamun har yanzu bai fahimci mun tura masa jami’n sirri ba dole zai shigo hannunmu a lokacin zai gane kuskuren da yake aikatawa sai yayi dayasani mara amfani wai shi me hukunta masu laifi , nida Kai ba masoya bane makiyan juna ne yadda kake bibiyar komai namu muma hk muna bibiyar  komai naka .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button