KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48


Alhj tahir dake zaune yana jiran  zuwn nazifi yace “ya’akayi son  Kai nake jira anyi nasarar samun alluran kuwa da kwayoyin ?”kayi hakuri karka ga kamar Ina cutar da abokinka wallahi rashin tashinsa shine zaman Lafiya da kwanciyar hankalina sai da nazifi ya zauna akan kujera sannan yace “karka ji komai dady an samu da yarda Allah Kuma zai yi aiki ajikinsa sosai  fiyye dana baya dan wannan maganin  bincike ya nuna idan anyiwa mutun sau goma zai iya mutuwa dady ya matso gabansa “kar dai ya mutu amman Kuma idan mutuwar zata zame min hutu Allah ya bada ikon tafiya  “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun nazifi ya furta a ransa  qirjinsa na bugawa da matsanacin karfi a sukwane nazifi ya jingina bayansa da abun kujera “dady nifa Ina ganin daga wannan maganin da zan kaiwa mumy bazan sake kawo komai ba nagaji da wannan aiki zuciyata ta kasa samun natsuwa kullum zuciyata na fad’a min Ina cutar da aminina, ruhina yaki samun salama wallahi bana iya runtsawa  dama nasan dalilin da yasa kake son kassara rayuwar Ib Kuma nasan cewar ba cutarwa bace a rayuwarsa wallahi zan tsaya sai Inda karfina ya kare sannan  zan tsaya naga komai ya tafi daidai .”
“kai dan Allah gafara can Sha Sha  dady yayi hanzarin katseshi ta hanyar fad’ar haka “Ashe baka da hankali Taya kake tunanin zan fada maka dalilina  ?  karfi da  matsayin  da  Ibrahim yake dashi acikin garin nan  ne farkon jegon komai ,  muddin na bari ya tashi bisa kafafunsa  komai zai iya faruwa  dani, kasani Kai ma  ko ka manta matsayinsa ne?bama haka ba Ibrahim nada karfin da zai iya komai akan cikar nawa burin  dan haka 
nazifi bazan barshi ya tashi ba Kuma bazan   fada maka dalilina ba dan ko na fad’a maka bazaka  fahimta ba ka dai qara min lokaci ka cigaba da aikin nan  karshensa ma yazo “.
nazifi ya furza da wani huci Yana tsinewa alhj Tahir a zuciyarsa ya mike tare da yi masa sallama har ya kusan Kaiwa bakin kofa yaji muryar alhj Tahir “karka kuskura ka fadawa kowa wannan shiri dan bazan fad’a maka abinda zai biyo baya ba sai dai kawai ka tsinci kanka cikin tsaka me wuya abinda bazan so faruwarsa ba kenan  dan har yanzu kana nan a matsayin d’ana” . gyada Kai kawai nazifi yayi ya fice .

Hajiya baseera zaune akan kujera me zaman mutun uku sai ga nazifi ya shigo hannunsa rike da leda wanda da gani kasan na asibiti ne  dan a zahiri ake iya ganin abinda ke ciki  ,hjy baseera  na ganinsa ta saki  fuska duk da zuciyarta cunkushe take da damuwar rashina lfyr Ibrahim ,
sosai  tayi farincikin ganinsa tana qaunarsa tamkar yadda take qaunar Ib .ya dan rusuna  cike da girmamawa ya gaisheta “Ina yi mumy ?”lafiya lau son ya fama da jama’a da  kokari Kuma ?
“alhamdulillah mun godewa Allah ya  Ib da jiki ? alhamdulillah Lafiya na ta samuwa  ta nuna masa gurin zama da hannunta “ka zauna son “ya samu guri ya zauna yana cewa daga bangaren dady nake gbdy lamarinsa babu sauki a yadda yake kokarin son kassara rayuwar Ib,wallahi mumy abun na matukar bani mamaki haka nan sai na zauna Ina tunanin Anya kuwa mahaifinsa ne da yayi  silar zuwansa duniya ?”mahaifinsa ne nazifi kama daina tantama shi mutun da son abun duniya ke sama da farincikin iyalinsa “.
runtse idanuwanshi yayi “dady na bukatar rayuwar Ib domin kuwa wadan nan  magungunan da yake bukata a dinga bashi da allurai daidai suke da mutuwarsa dan  watan wata rana za’a wayi gari babu shi .”
“Da naji wannan mummunar labari zanfi bukatar  na bar gidan nan dashi sai dai ban san yadda zan bar gidan dashi ba  batare da sanin mahaifinsa ba”. ta k’arasa maganar cike da damuwa .
  shiru suka yi na second biyar  sannan  nazifi  ya cigaba da  magana a tsanake “karki  damu mumy daga yau  kisa a  ranki Ibrahim zai dawo rayuwa kamar yadda  sauran mutanen suke yi “zan d’auki nauyin ib bama garin nan  ba kasar ma  zan bari dashi gabad’aya Cikin dakiyar zuciya hjy baseera tace “wannan hukuncin naka yayi daidai Kuma na gamsu dari bisa dari dashi  wallahi , dan haka babu abinda zance maka  sai godiya ,yadda kake son ka nisanta tsakanin Ibrahim da mahaifinsa ta k’arasa maganar tana Kuka sosai  tmkr wacce aka Aiko mata da sakon mutuwar ta ko akace  mutuwa Ibrahim zaiyi “.
“lamarin alhj Tahir akwai ban tsoro da rashin tausayi da Imani “sosai kuwa  yanzu dai a sirrance zamuyi komai ta yadda bazai fargaba  “Allah ya d’aura mu akansa Allah ya kawar da tunaninsa akanmu “Ameen mumy ni zan wuce  duk abinda ake ciki zan kiraki a waya. “To na gode na gode sosai Allah yayiwa rayuwa  albarka ya mike ya fice .”yana jinina girman alamrin dady ,gbdy ya gama ganosa  Kuma yana tare da kwararrun  hujojin da zai sa jami’an tsaro su tunhumeshi   dashi idan bukatar haka ya taso , idan ta kama ya tsaya gaban alqali zai tsaya ya bada sheida domin kuwa mutumi kirki  ake karewa  da rufawa asiri irinsu dady kuwa sai dai a fallasasu duniya tayi Allah wadai dashi .”

***””
Da misalin karfe goma   na daren ranar litini  jaguwa   ya shigo d’akin jikinsa sanye da kayan shan iska farare sol  yayinda hannunsa ke  rike  da farar leda dake d’auke da roban takeway guda biyu  wayam ya ga d’akin babu ita babu alamun ta  jiki a sanyaye  ya ajiye ledar hannunsa ya karasa ya zauna abakin gado a tunaninsa wanka take  shiru har minti biyar ta wuce bata fito ba ya kira sunanta yana duba agogon dake d’aure da tsintsiyar hannunsa still shiru ya Kara five  minute  bai ji motsin saukar ruwa ba ya mike tsam  ya Isa  bakin kofar bayi yayi knowking still babu respond Kara knowking yayi no answer a hankali yaji zuciyarsa ta buga da sauri ya  d’aura hannunsa kan handle din kofar  ya murd’a   yaji murfin a bud’e  ya sanya kanshi cikin  ya leka wayam ya gani nan  ma  babu ita yayi mamaki Inda  taje ya fito a rud’e yana duba sauran dakunan gidan nan ma shiru babu ita ..
Wata  uwar ashar ya saki ya wuce su anas ya  fito zuwa haraban gidan da sauri da mugun sauri yanzu kam jikinsa ya fara bashi akwai matsala yana tafiya anas ,jubi,jabir ,har ma da kamil dake dingisa  kafarsa suka biyosa suna Kiran sunansa amman bai juyo ba sai faman dube dube yake yana Kiran me gadinsa da sauri ya k’araso ya rusuna cike da girmamawa “ka budewa  yarinyar nan  kofa ne ?me gadi ya girgiza masa Kai alamun a’a , cikin fushi ya  d’auke shi da mari “ka bud’e baki kamin magana zaka wani girgiza min Kai kamar kadangare “a’a sir ban budewa kowa get ba tun safe ma babu wanda ya fita daga gidan nan bayan Kai  “.
ya Salam ya furta yana rike kugunsa da hannu d’aya ya shiga sintiri a haraban gidan  ya bar me gadi dafe
da quncinsa “gidan ubanwa ta shiga ?wallahi idan banganta ba sai naci ubanka ya fad’a a fusace yana juyowa tare da  nuna me gadi da yatsansa gbdy abokansa suka k’araso garesa alokacin d’aya anas ya dafa shi “wai meke damunka ne “ban sani ba duk banga amfaninku  ba ace Kuna zaune tanweer ta fito baku sheida min ba “
“ta fito taje Ina ?”tun byn sallahr isha’i  muke zaune a falo  bana tunanin ta fito zo muje mu sake dubata tana ciki  may be ko tana bathroom ne ya kamo hannun jaguwa ,ya fixge a fusace “bata nan na duba koina  bata nan bata cikin gidan nan  wallahi idan banganta ba duk sai na kasheku d’aya bayan d’aya cikin kankanin lokaci gabad’ayansu suka shiga tashin hankali anas ya basu umarnin nemota   duk suka raba kansu suna nemanta shi kuwa  jaguwa tuni ya dawo tamkar wani zarare   shi kad’ai yasan irin tashin hankali dayake ciki “Ina tabi tunda me gadi yace bai bud’ewa kowa get ba ?ya d’aga Idanunsa da suka rikid’e suka canza kala zuwa katangar gidan da sauri ya girgiza Kanshi “muddin ta tsallaka katangar nan  lallai zata mutu idan Bata mutu ba zata  nakkasa gashi  bayan gidan  babu wasu gidaje sai kango .
ya fito a gigice anas da jubi suka biyosa suna cewa “Ina zaka ? “dan Allah ka natsu  bazata iya tsallaka katangar nan ba , bai tsaya sauraronsu ba dan kwata kwata hankalinsa bai jikinsa  Kai tsaye bayan  gidan ya nufa yana haska gurin da wayarsa yana Kiran sunanta babu  ita babu alamunta ya  juyo
a harzuke yana masu wani irin kallo mai d’auke da rashin mutunci suna kallo ya dungule hannunsa, gbdynsu suka yi matukar tsorata shi kuwa anas byn tsoro har da kallon mamaki yake masa sai dai ya kasa ce masa komai wani irin kallo jaguwa ya cigaba da yi musu da  jajayen idanunshi ..”
????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button