KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

kai tsaye indoor cikin inda aka tanada domin yin shoping ya shiga bayan ya karbi bakar jaka a hannun daya daga cikin yaransa aciki gurin ya hadu da mutanen daya zo domin su, hannu ya mika masu daya byn daya suka gaisa  sannan ya dan waiga hagu da dama dan a d’an tsorace yake amman fahimtar  babu wanda idanunsa ke kansu ya saki jikinsa  sosai ya bude jakar hannunsa ya ciro leda daya ta  coken ya mikawa mutun daya, ya kar’ba tare da ciro qaramin wuka a gaban aljihunsa ya tsaga   ledar ya dibi coken din kadan ya kai bakinsa domin tabbatar da me kyau ne ko akasin haka .”jinjina kai yayi alamun tayi  dan haka ya mika masa ya mayar inda ya cirota shi kuma   ya mika masa jakar dake dauke da makudan kudade ,shima indoor ya bude ya tabbatar da kudaden ne a ciki ya sake mika masa hannu sannan suka fito  atare indoor  yayi hannunsa na hagu yayinda fararen fata sukayi na dama .”

daga cikin abun jin magana  su suka ji muryar jaguwa yana cewa “duk ku ankare fa gasu nan da alamar sun gama kasuwancisu kada kuyi harbi har sai idan nace kuyi jakar dake hannunsu kawai muke bukata sannan muyi kokari jami’an tsoro suyi gaba dasu idan sunki su bayar ne kawai zan iya cewa ayi wani abu akai .”Indoor na tafiya kawai yaga kamar ana binsa abaya ya waiga bai ga kowa ba ya sauke naunayen ajiyar zuciya ya sake rike jakar kudinsa da kyau  ya canza hanya, bangaren wadan can mutane suma anas ne da kamil har ma dasu jubi  ke biye dasu abaya duk inda suka bi suna biye dasu .”

tafiya kadan indoor yayi kawai yaga mutun ta gabansa tsaye yana kallonsa  jaguwa  bai tsaya wata wata ba   ya daura masa  bakin bindiga a goshinsa wata irin firgita yayi ya shiga zazzare idanunwa ya juya da niyyar guduwa nan ma yaga mutun biyu abayansa duk rike da bindiga ,nan take hankalin babban yaronsa wanda kuma ya kasance kani garesa ya tashi domin idanunshi na kan yayansa a bisa yadda suka tsara  atare ya waiga hagu da dama bai ga alamun polisawa ba hakan ya tabbatar masa da  ‘yan fashi ne aka musu cune.”
“Miko min jakar hannunka.”Idan kai jami’in tsaro ne gara kawai ka danganani da hukuma ko kuma mu sasanta anan dan zamu iya gyarota ,girgiza masa kai jaguwa yayi “ko daya mu masu amsar rabonmu né kawai mu qara gaba bamu da wata halaqa da polisawa hasalima abokan gabarmu né “gaskiya bazan baku wannan jakar ba gara ma ku daina wannan sana’ar kuzo ku hada kai dani ni nan zansa rayuwarku ta canza “.bazan iya aikinka ba domin aiki ne dake gurbata rayuwar yayan al’umma bazan zama silar bata zukata ta hanyar siyar da abinda zai saka bushewar zuciyar ga ya’yan alumma ba kai ma ina baka shawarar ka daina domin kuwa gara alqallata akan taka.” sam maganarsa bai sa farinciki ya mamaye zuciyarsa ba sai ma duhu daya gilma a qirjinsa “ka bani jakar kudin ya sake maimaita maganarsa yana miko masa hannunsa .”

Atare daga inda yake a maboyarsa ya saki harsashi guda biyu  nan take jaguwa  ya juyo a matukar firgice sauran mutun biyu din  dake tare dashi suka zagayesa suna duba ta inda harbin ya fito  kanin indoor  ya nuna kansa domin su san ko waye   mutun  biyu   suka biyosa kamar  iska yabi wata hanya  anan ma boyewa yayi yana kallonsu .
gurin ne ya hargitse da hayaniyar mutane kowa ya fara neman takansa wanda hakan ya bawa indoor  damar  kwasa da mugun gudu rike da jakar hannunsa, jaguwa ya biyosa aguje shi  jakar kudin yake bukata daya ajiyeta  sannan yaga sun shiga hannun polisawa shi kenan sun gama dashi  babu wani binsa da zai yi dashi .”
acan dayan bangaren ma anas biye yake da mutane guda biyu inda mutun daya yabi wata hanya nan kawunansu ya rabu gida biyu wasu suka bi mutun daya anas yabi me rike da jakar koken cikin haka jubi da kamil suka biyo hanyar da anas yabi tare da cire abun kunnensu “wannan dama ce kamil kar mu bari ta subuce mana cikin nida kai duk wanda ya samu damar kawar dashi kawai yayi.”

atare suka gyada kai tare da maida abun kunnensu suka cigaba da tafiya cikin sauri cikin haka suka hango anas yayi nasarar hard’e kafafun mutumin tare da saita kanshi da bakin bindiga ,da kai kamil yayiwa jubi alamar ya harbesa ai kuwa babu wani bata lokaci ya saita kanshi da bindiga zai harbi keyarsa yayinda shi kuma kamil ya kalli bayansa saboda tsaro dan kar wani daga cikin yaransu su
ya gansu ,adaidai lokacin sky ya sanyo kai ganinsa yasa kamil ya rike hannun jubi yayi kasa dashi ya harbin kafafun mutumin anas ya juyo da sauri cikin tsananin firgici sai dai ganinsu sune a bayansa yasa ya samu natsuwar zuciya ya maida hankalinsa ga
kafafun mutumin dake gabansa jini ne ke zuba kamar an yanka qaramar dabba “oga ya kuka tsaya anan kuzo mu qarasa mana “ya fad’a tare da wucesu ya qarasa inda anas yake wanda yayi nasarar kar’bar jakar hannun mutumin ya kallesu daya bayan daya yana cewa “waye yayi harbin acikinku ?”a dan rikice suka kalli junansu jubi ne yayi karfin hali cewa “kamil ne “ dan haka ya fuskanci kamil “gsky da bakayi harbin ba tunda gbdynmu ance kar muyi ya kamata mu dinga kiyayewa ya qarasa maganar yana cewa muje ko.”

  Gudu sosai indoor yake har ya kusan fita daga cikin gurin siyayya jaguwa na biye dashi yayinda kanin indoor ke  harbi kan jaguwa dake bin bayan  yayansa amman sai  ya goce harbin karshe da yayi ne adaidai lokacin tanwer ta sawo kai a rude domin neman gurin buya sauran kad’an harbin ya samu kanta cikin tsananin tashin hankali ta saki wata razananniyar qara tayi wurgi da ledar hannunta ta rufe idanunta da hannuwanta duka jaguwa   ya rungumota jikinsa yayi kasa daita harbin ya samu wani guri kusan mutuwar zaune tayi aguri nan ya barta ta dawo tamkar mutun mutumi ya mike da sauri ya cigaba da bin indoor.”
ganin da  jaguwa yayi bashi da niyyar sakin jakar yasa alokaci daya ya harbi  hannunsa da kafarsa daya dole tasa ya  duka kasa rike da kafarsa jaguwa ya qaraso ya tsaya akansa  yana sauke numfashi “kanka naso na harba  ka godewa allah ,kuna ina wani cikinku ya samu nasarar kar’ba dayan jakar ?”okay mu hadu a inda muka tsara kafin kace me sun hadu ta bayan layin shopright ya mika masu jakar hannunsa yana cewa “kuje kawai zanzo daga baya amman ku bar min wacan motar ya fad’a yana
canza wata fuskar ya bar ainihin fuskarsa ya cire safar hannunsa tare da sauya takalmi zuwa silifas
ya cire yar saman rigarsa white t shirt ya bayyana
sai daya ga wucewarsu sannan ya shiga mota ya
nufi cikin shopright yayi parking .”

kai tsaye ciki ya shiga cikin tsananin damuwa inda ya bar tanwer zaune ya nufa a lokacin ta mike tsaye tana zazzare idanuwa gbdy mutane dake cikin gurin suna cikin tashin hankali kowannensu hanyar guduwa yake Nema dan da kyar ma ya samu ya shigo saboda turereniyar fita daga gurin bai tsaya wata wata ba ya riko tsintsiyar hannunta “kin shiga rudani ko tunaninki zaa harbeke ?firgigib ta dawo haiyacinta sakamakon jin maganarsa da saukar hannunsa nata ,ba yanzu zaki mutu ba sai kin cika min gida da baby’s .”
Bata damu da maganarsa ba dan alokacin burinta bai wuce taganta a gida ba ,tayi da tasani da bata bi maganarsa ba da yanzu ta mutu ,wasu hawaye masu zafi suka gangaro mata akan kuncinta a natse ya soma tafiya daita alokacin team din sojoji dana polisawa sun qaraso inda suka iske kanin atare na kokarin dagasa domin su gudu suka cafkesu dan daman an dade ana neman su “kamata yayi su hada da kai “kina da wannan damar ai kice masu wani abu mana tsaki taja tare da fixge hannunta cikin nashi ta nufi wani bangaren a haraban gurin sai dai sama ko kasa ta nemi direbanta ta rasa aranta tace “shima ya gudu kenan ? naunayen ajiyar zuciya ta sauke ta ciro waya ta kira layinsa yana ringing amman baa dauka wata mota ta gani a gabanta bata tsaya tantancewa ba ta bude ta shiga ,kawai taga jaguwa zaune ta yunkura zata fito daga cikin motar taji yayi locking din koina dole ta koma ta zauna ranta a matukar bace.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button