KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

jamaa dake hall sai dubawa sukayi suka nemi ango da amarya da abokansa sukayi suka rasa dan haka a hankali mutane suka dinga watsewa “.
Ranar jumaa ya kama daurin aure a wani masalaci jaguwa ya kai daurin auren wanda tsirarrun mutane sukaje aka daura sannan aka dun guma zuwa na sadiq kiri kiri jaguwa ya hana duk wani dan team dinsa zuwa duk da bada fuskarsu ta ainihi suka je ba fuskar anas datashi ne kawai a bayyana daga daurin auren anas ya sallamesu daga shi sai anas suka je byn an daura suka shiga gaisawa da mutane sam bai yarda sunyi hoto da kowa ba daman wannan kai da ne da asalin fuskarsu basa hoto.
Qarfe biyar daidai mutane suka hallara a radisin hall domin gabatar da walima hally din ya kasance daga iyayenta kawayenta da abokan arziki amman banda ango ,jaguwa ne ya hanashi zuwa yace suyi dinner dinsu su kadai
A daren byn sun dawo daga dinner aka canzawa hally wasu kaya, sosai tayi kyau cikin wata hadaddiyar shadda madam gezner baki touch of milk colour Riga da zani ce dinki bakaramin kyau yayi mata ba sosai kuruciyarta ta fito ga wani makeken sarkar gwal dake makale a wuyanta da dan kunne da abun hannu da zobe wanda jaguwa ne ya siya mata sai wani haske ta kara na amarci tana zaune tsakiyar kawayenta sai kamshi turare take zubawa shafiq ta shigo da dan saurinta “taso muje yaya na kiranki ta yafa mayafi lifaya fari touch of gold ta nade mata jiki ta riko hannunta ta sauko daga kan gado tare suka fito tana rike da tsintsiyar hannunta bata tsaya akoina ba sai dakin ammi inda ta iske anas zaune akan dadduma yayinda jaguwa ke tsaye rungume da hannunwansa a kirji shafiq ta kamota ta zaunar daita kusa da anas dake zaune cikin wata dakakiyar shadda fara sol sai maiko take kana ganin kasan mai tsada ne kamshin turaren dio ne ke tashi ajikinsa yayi matukar kyau kana ganinsa kasan yana cikin farinciki .

a hankali jaguwa ya motsa bakinsa “ammi kiyi mata abinda ya dace zamu wuce daita , shafiq ta kallesa a dan rude “yaya da kanka alhalin ga masu rakiyar amarya nan cike da gida ? “duk su waste baa bukata ni haka nayi raayi kuma babu me binta kema daga baya zaki san gidan kuma bance ki kai kowa ba ko ki fadawa wani ,ke kawai na lamucewa ke hatta mijinki ban yarda ba idan dole sai dashi zaki kiyi zamanki baa so shiru tayi cike da matsanancin mamakin yayanta , ta juya ta kalli ammi taga sam bata nuna damuwarta ba hally ta matso gaban ammi tana neman yafiyarta cikin muryar kuka “ammi ki yafe min,baki min komai ba auta ,allah kiyaye hanya allah yatsareku allah kuma yayi muku albarka gbdy yayiwa rayuwar auren ku albarka .

“Halima!
Ammi ta kirsa sunanta “Ina bukatar natsuwarki halima ina bukatar hankalinki hally ta natsu sosai qirjinta na bugawa da karfi “kiyi hakuri ! kiyi hakuri!! kiyi hakuri !!! sai data maimata mata sau uku tana zubar da hawaye ,babu komai acikin aure sai hakuri ,kiyi hakuri kiyiwa mijiki biyaye halima mijiki maraya ne a yanzu bashi da kowa sai ke ki kular min dashi ina son anas bana son kiyi wasa dashi idan yayi miki laifi ki kirani ki fada min kaima idan tayi maka laifi ka kirani ka fada min bance ka boye min ba dan hally tana matsayin diyata ku rike junanku amana tashi kuje allah yayiwa rayuwarku albarka hally ta soma kokarin mikewa kuka yaci karfinta ta kasa tashi ammi ta kamota tana gyara mata mayafinta dake kokarin zamewa ta riko hannunta ta kamo na anas ta damke guri daya “anas ga amanar auta nan na baka kayi hakuri daita allah yayi muku albarka suka fita a hankali jaguwa na biye dasu har haraban gidan ammi ta rakosu idanunta cike da hawayen tausayin diyarta yau ko gobe zata shiga wani aji na musamman da kanta ta budewa hally mota ta shiga ta zauna ya rufe,yayinda anas ya shiga dayan bangaren suka bar gidan suna fita dangin zuhra suka kawota gurin ammi domin girmamawa gareta daga nan suka nufi gidan da zata zauna.

A natse motar ke tafiya kamar yadda matukin motar yake sam babu mahaukacin gudu ahankali yake jansu bai tsaya akoina ba sai egbeda a kofar wani madaidaicin get yayi parking ya ciro wani madaidaici remut yayi warning glass ya danna nan take get din ya bude yasanya hancin motarsa ciki .
Yayi parking ya fito haka zalika anas ya fito hally taki fitowa jaguwa yayi murmushi “ai sai ka bude mata itama wai aji,ai daidai kenna idan cewa tayi na dauketa na goyata duk zanyi ya fad’a yana bude mata kofa hade da riko hannunta “lallai ka haukace wallahi“.

????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

????️34

…..a hankali anas ya bude bangaren da take zaune tana sheshekar kuka ya riko laulausan tafin hannunta cikin nashi ya fito daita suka fara tafiya jaguwa na biye dasu a baya cikin tsinkewar zuciya da tausayawa yar karamar kanwarsa da batasan meye rayuwar duniya ba gashi yau zata kwana da gogen dan harka wanda ya kware agurin iya sarrafa mace . da kyar take daga kafafunta suna daf da shiga babban parlaur’n gidan taja burki ta tsaya tana sheshekar kuka ya tsaya ya waigo gefensa inda take tsaye yana kallonta ,ta kallesa cikin lullubinta tana kokarin zare hannunta cikin nashi bai damu ba ya sakar mata hannun ya koma gefe guda ya tsaya yana wa jaguwa alamar ya shigar daita.”
Naunayen ajiyar zuciya jaguwa ya sauke sannan ya kamo hannunta suka shiga ,kai tsaye d’akinta ya nufa daita ya zaunar daita a gefen gado wani sabon kuka ta fashe dashi mai tsanani wanda hakan ya sake rikita jaguwa sai dai yay kokarin sanyawa jikinsa jarumta domin rauninsa zai sake rikitata ,
anas ya isa inda take ya sanya kanshi cikin lullubenta ya hade fuskarsa guri daya yana shakar numfashinta yana mata mgn cikin rada ,shi dai jaguwa yana tsaye shiru rungume da hannuwansa duka a qirji yana dubansu har sanda anas ya dago still idanunshi na kanta “hally ni zan wuce idan na samu lokaci zaki gani zuwa gobe ko jibi yana gama fadar haka ya sauke hannuwansa ya juya tare da riko hannun anas suka fito zuwa haraban gida, “yana ga kana mata kallon maita ? dan allah ka tausayata mata kaji abokina “ yayi mgnr muryarsa a raunane Kmr zai yi kuka ,anas ya kasa cewa komai illa kunyarsa data kamashi , har gurin motarsa ya rakashi ya shiga yana sake mika masa hannu sukai sallama yana tsaye har sai daya ga wucewarsa sannan ya dawo ciki .”

Byn tafiyar jaguwa shiru ne ya biyo baya anas nata kare mata kallo kafin a hankali ya matso sosai kusa daita ya bude fuskarta tayi kasa da kanta ta sunkuyar ta maida lullubinta tana wasa da yatsun hannunta murmushi yayi yana cewa “bafa zamuyi haka dake ba amaryata ya karasa maganar yana yin baya da lifayan dake nade da jikinta “kayan nan sunyi miki matukar kyau sun cinyeni “ yayi mgnr a tsanake yana kallonta ita kanta yanayin da take ji ajikinta tasan tayi kyaun da bata taba yin kamar ba a iya tsawon rayuwarta rigar jikinta ta dan kamata daga sama wanda ya bayyana dukiyar fulaninta ta sama a hakan ma da yake cewa tayi kyau bai ga komai ba saboda tana lullube cikin lifaya .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button