KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Ana’s ya d’an kallesa a rikice ya gyada masa kai alamun haka yake bukata ,babu yadda ya iya dole yayi kamar yadda ya umarcesa amman yaso yaji sautin muryarta bai sani ba ko shi zai zamo abinda zai ji karshe kafin mutuwa ta riskeshi ,jikinsa a matukar sanyaye ya zauna a saman hannun kujera idanunshi na qoqarin kawo ruwan hawaye, jaguwa ya ciro wayarsa ya soma neman layin ammi alokacin
Hally na zaune shiru tana tunanin abinda yasa anas yaki daukar wayarta har ma akarshe ya kashe wayar gabadaya,taji qarar ringin din wayar ammi ta dubi wayar dake yashe a kusa daita sunan yayanta ta gani ta dauki wayar da sauri ta mikawa ammi tana me tsura mata ido .”

Ammi ta karbi wayar daga hannunta ta danna koren maddani tare da sallama daga can bangaren jaguwa ya soma magana cikin raunanniyar muryarsa “ammi mun fita wani aiki ne wata killa mu dawo yau ko gobe ko kuma dai sai an ganmu muna tsananin bukatar adduarki “ta dan ja doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana cewa “allah ya baku saa yasa kuyi nasara allah ya tsareku gabadaya” Ameen ya amsa tare da yin shiru yana sauke numfashi jin yadda yayi shiru tace “Anya kuwa bayan tafiyarku aiki babu wata matsala ?”babu komai ammi sai dai ina jin babu dadi ne araina ,”to a hakura mana da tafiyar “hakan bazai yiwu ba ammi yanzu haka ma muna cikin aiki sai dai fatan nasara “inshaallahu karkaji komai zakuyi nasara allah yayiwa rayuwarka albarka ,
Ameen ammi sai dai hally zata cigaba da zama agurinki har sanda zamu dawo “to shikenan yana gama jin abinda tace yay discounting din kiran ya sake fuskantarsu “.

Halima ta maida kallonta ga ammi dake zaune tana amsa waya suka hada ido daita taji gabanta ya shiga faduwa, take damuwa ta mamaye fuskarta ta dubi ammi tace “ammi me yaya yace miki ?”wai sun tafi aiki ne suna bukatar addua sannan ke zaki cigaba da zama anan har sanda zasu dawo “to ai na kira ya anas bai dauka ba byn bai ta’ba kin daukar wayata ba “yanzu me kikaji nace miki sun fita aiki “amman ammi ina jin ba tafiya wani aiki ne ya hana ya anas daukar wayata ba akwai abinda ke faruwa dashi tunda har yaya zai iya kiranki alhalin suna bakin aiki shi me yasa bazai dauki wayata ba ?.”ta fada muryarta a raunane kamar zatayi kuka .”

“ki kwantar da hankalinki karki yi wannan tunanin Kinsan yanayin aikinsu ya gaji haka inshaallahu lafiya zai dawo “duk sanda zasu aiki yana fada min kafin mu rabu me yasa yau bai fad’a min da kanshi ba sai yaya ne ya kira kuma me yasa bai dauki wayata ba ?”ta qarasa maganar tana hawaye ammi ta fuskanci rashin daukar wayarta da rashin fada mata zashi aiki ne yasata damuwa dan haka ta soma rarrashinta “inshaallahu babu wata matsala kiyi masu kyakkyawa fata .” ina masu kyakkyawa fata amman jikina yana bani akwai wani abu dabam .“haba halima me kuma jikinki zai baki kin dai tsargu ne kawai amman babu komai “allah ji nake kamar tafiyar me tsawo ce dayawa wallahi ni da zasu hakura da tafiyar nan su dawo zai fi min alkhairi .”

Tsab ammi ta gano manufar hally dan haka tayi murmushi “kiyi masu addua gamawa da aikin lafiya tayi shiru daga bisani tace to allah ya dawo dasu lafiya ta kwanta gefe wasu tsiraran hawaye na zubo mata ta gefe da gefen idanunta ,ammi ta gani akan fuskarta amman bata dai mata magana ba aranta tace “yaran zamani kenan kiriri suke nuna maitarsu a fili akan mazajensu .” jaguwa ya cigaba da sauraron su har lokacin babu wani daga cikinsu daya qoqarin cewa wani abu sai faman mulmula baki suke alamun suna son yin magana amman kwakwaluwarsu ta kasa aiwatar da komai .”

A hankali ya qarasa inda matattakala take cike da sand’a ya hau ya kasa kunnensa sosai sautin wata murya yaji yana magana “ba zamu bar nan ba sai mun kamashi dan haka Kuyi pata pata da gurin ta yadda harbi zai samesu a duk inda suka boye acikin gidan domin na lura suna son suyi wasa da hankalin hukuma ai kuwa kamar jiran umarni policewar dake rike da bindiga suke suka cigaba da harbin cikin gida wanda windows kam tuni an patattakasu har ana iya hango cikin gidan kuma hakan ne ma ya bawa jaguwa jiyo magana.”ya sauka a hankali ya koma inda anas suke ya janyosu suka yi wani bangare “ku tsaya anan ina ganin ni zan fita ni kad’ai da sauri ana’s ya mike tsaye jikinsa na kyarma yana girgiza kai yana kallon jaguwa da yanayinsa ya nuna alamun rashin tsoro wata irin damka yayiwa hannun JAGUWA da karfi yana cewa “babu inda zan bari kaje,wato kana son ka rigani mutuwa ko “?yadda yake maganar zaka fahimci yana cikin tsananin rud’ani da tashin hankali.”

Kamo kafad’un ana’s jaguwa yayi ya zaunar dashi akan kujerar daya tashi yana qoqarin kwantar masa da hankali “please ana’s kayi qoqarin ka dinga rage wannan tsoron , idan ina hango tsoro acikin kwayar idanunka kana karyar min da gwiwa d’ago idanunshi yayi ya tsurawa JAGUWA yana kallonsa tabbas maganarsa haka ne a yanzu ma da yake kallonsa yaga jikinsa yayi sanyi runtse idanu anas yayi ya fara tunanin abinda zai faru idan jaguwa ya fita ”
“Har yanzu basu shigo ba suna haraban gidan ya kamata na hanzarta fita tun kafin su shigo“
kamil yace “no jaguwa zuciyata bata amince da fitarka kai kadai ba ko kuma nace bamu amince ka fita ka mika kanka ba ,wannan gaskiya ne kamil bamu yarda ba me yasa ma ka bari muka shigo .”?ai da an sani abi shawarar anas tun farko anyi bata kashin amman yanzu allah ya taimakemu mun samu mafaka me zai sa kuma mu maida kanmu da kanmu .”? ka dai sake wani tunani amman wannan sam sam bai yi ba inji cewar jabir .”

Wani sanyi dadi anas yaji ya mamaye zuciya da gangar jikinsa sakamakon goyon bayan da suka bashi ,jaguwa ya shafa sumar kansa da hannunsa daya, yayinda dayan hannun ke cikin na anas wanda yake dubansa cike da tausayawa, furzar da huci me zafi yayi ya zare hannunsa dake cikin na anas yana jin wani irin mummunar fad’uwar gaba ya isa inda dining area yake ya tsaya cikin tsananin tunanin abinda zai yi bayansa suka bi da kallo ,ganin haka ya zira hannunwansa duka cikin wondonsa ya cigaba da tafiya still suna biye dashi har ya shiga wani d’aki basu daina binsa ba har anas ,hakan yasa yaransa ma suka biyo bayansu cike da tsananin tashin hankali.”
Ya tsaya cak ajikin bango yana kokarin saita kanshi bayan kamar second biyar sannan ya soma magana muryarsa can kasa kasa “Tabbas na gama nazari da duk wani tunanina akanmu sai dai banga mafuta ba ,daman na shigo damu nan ne domin boye sannan mu san yadda zamu tsara fitar da kanmu kafin su riskemu akwai wata boyayyar hanya ta nan amman magudanar ruwa ne ,da iya mu biyar din nan ne nasan zamu iya ficewa tunda mun ta’ba yin haka a can baya amman wadan nan dake tare damu acikinsu babu wanda nake tunanin ya iya iyo.”ya qarasa maganar tare da yin shiru yana fuskantarsu.”

Babu wanda yayi magana acikinsu suka cigaba da sauraronsa ya dan numfasa sannan ya cigaba da mgn “idan gabadayanmu muka kasance anan hakan zai iya janyo mana asarar rayuka dayawa ciki kuwa har dani ,a yanzu ne fa muke cikin wani yanayi me matukar wahala da hatsari dan haka gabadayanku ina bukatar kuyi hakuri ku zauna anan ni zan fita, idan na riski mutuwa daman ni din me kararren kwana ne, idan kuma ina da sauran rayuwa zan dawo gareku mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka faro yana gama fadar haka yayi wuf ya fice acikin dakin tare da janyo kofar dakin wacce bata da maraba da magnet kofar bata kai ga rufewa ba anas yasa hannunsa kofar ta tsaya cak bayansa yabi da kallo kamar ya zubar da hawaye sai daya daina hangosa sannan ya koma ciki dakin cikin tsananin tsinkewar zuciya ya zauna yana dafe goshinsa yana fidda numfashi sama sama .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button