KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

yayinda sp yusif ke tsaye a cikin wani kango sanye da bakin suit tare da wasu daga cikin yaransa da suka biyosa aiki daman kuma ya rabasu kashi kashi ne kowanensu da bangaren daya ɗauka ,wayarsa ce  tayi ƙara ya ciro wayar daga aljihunsa cikin sauri yana duba screen din wayar sunan wanda ya gani yasa ya dauki kiran da sauri tare da mannawa a kunneshi “hello “
“Yes noted “
Inspector hasan dake fuskantar shi yace “how far ?
“We have to move immediatly “boss there won’t be a problem there be danger today let us move ,let’s move suka faɗa gaba-daya a hankali motar Jaguwa ke gudu ganin hanyar so silet ga duwatsu kaca kaca dole ko yana son yin gudu yabi a hankali yayinda yan-sanda ke la’be hagu da dama domin ƙoƙarin cafkarsa ..

A tsanake sp yusif ya fito daga maboyarsa ya sha gaban motar Jaguwa hade da tsaita bakin bindigarsa ga glass din motar Jaguwa slow  motar Jaguwa ta koma tafiya a hankali har yayi kusa da   sp cikin haka yaran sp dake boye hagu da dama suka bayyana suka saita bakin bindigarsu pistor  “crack and shut basu tsaya wata wata ba suka budewa motar wuta bisa umarnin da’aka basu harbi motar suke da iyakacin kwarewarsu har sai da suka tabbatar da sun yiwa glass din motar ratsatsa…

DARLING’S????????????????????????
KUSKUREN BAYA
     ????????????????
????????????????????????

    WRITING BY
BAGUDO& MIMI’S QUEEN
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

????️10

…A hankali  sp  yusif ya sauke   bakin  bindigarsa  yana  haki  yana takowa a hankali  har ya karaso jikin  murfin motar jaguwa  ya ja ya  tsaya tare da d’aura  hannunsa ɗaya a  saman mota  “the wages of sin is death …….”
ya  furta haka yana duban inda  yaransa ke tsaye rike da bindiga   “yau  dai munyi nasara  kashe tantirin  ɗan fashin daya addabi  kasa da kasa   ,Allah na gode maka daka bani dama da ikon kawar dashi daga doron duniya , isar da gawarsa headquater  ma  wani  matakin d’aukaka ne  garemu ,na dade ina addu’a akan zuwan wannan rana sai gashi tazo mana  cikin sauki dole  mu  samu double promotion…… ” ya karasa maganar yana kallon sararin samaniya zuciyarsa fes cike da matsanancin farincikin samun nasara .

   “ya sake buɗe  bakinsa da niyyar sake yin magana  yaji an daki  murfin   kofar motar  da karfin gaske   kofar ta buɗe wanda hakan yayi sanadiyyar da hannun  jaguwa ya bugu da murfin kofar dashi kanshi sp  yusif dake tsaye  yayi taga taga ya koma baya sannan ya tsaya bisa kafafunsa yana kallon motar  .

Mutuwar tsaye suka yi gabad’aya  suna kallonsa take  bindigar hannun sp yusif ta subuce  yayi saurin sake  ja da baya idanunshi na kan jaguwa dake ƙoƙarin fitowa daga cikin motar,  duk ilahirin jikinsu rawa yake har sp yusif wanda hankalinsa kusan yafi na sauran tashi dan yanayin bugawar zuciyarsa da yanayin tsoronsa sai ya baka mamaki tamkar ba jami’in tsaro ba  “

  cikin isa da izza jaguwa  yake takowa zuwa inda sp yusif yake tsaye , ya tsaya nisa kaɗan dashi wanda bai fi taku biyu su fuskanci juna ba  , idanunshi dake a lumshe  ya  ware su fesss  akan  sp  yusif yana ciza gefen  lip’s d’insa na kasa,sp   yusif  ya kalli jaguwa  kamar zai yi kuka saboda gigita da ganinsa a raye da yayi , tunda yake bai taɓa ganin abinda ya d’aga masa hankali irin wannan ba , “bai taɓa ganin dan adam din da aka yiwa harbi irin wanda suka yiwa motar jaguwa ba amman ya rayu har ya samu damar fitowa  daga cikin motar cikin isa da izza ,tabbas yasan akwai wata a kasa ,wannan abu akwai tsarkakkiya acikinta     “

  Jaguwa  ya had’iye dariyar sp  yusif dake  neman kufce masa saboda gabad’aya ya gama karantar yadda sp yusif da yaransa suka tsorata dashi  ,dan gabadaya fuskokinsu ya sauya daga farinciki  zuwa matsanancin tsoro da firgici  kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin tashin hankali mai tsanani …

“waye  kai  sp yusif karaye  ? mutumin da cin hanci da rashawa ya aura  tun kana ƙaramin  mataki har zuwa yanzu daka taka wannan matsayin , har kake godiya ga Allah bisa samun nasara akaina  “wani mataki ka taka tukunan ma a rayuwarka da zaka so kama mutun irina  “?yayi masa tambayar yana kafeshi da kyawawan idanushi hade da sauke numfashi .

“Ya kamata kusan ko waye ni kafin ku dinga bibiyar rayuwata  kana min kallon mamakin ko ? “Kana mamakin yadda na rayu ko ? Zan so bude maka hanyar da zaka fahimci ko wanene ni  da kai da sauran tawagar dake bibiyar rayuwata amman bazan yi ba zan barku  cikin duhu da wasi wasi da kai da waɗan nan yaran naka daka taso  gaba ” babu abinda zaku iya  akan jaguwa sp yusif karaye  , ba ku   ba hatta shugaban tawagarku  gaba-daya wato commition of police yayi kankatar da zai iya gaba da gaba dani bare kai da yaranka  ya karasa maganar a fusace yana nuna sp  yusif da yatsansa “

“a kasar nan  kowa abinda ranshi yake so yake tare da aiwatar da son zuciya akan kaskantattu marasa  galihu  , “to bari kaji wani labari  da baku isa ba   dubunku ma  basu isa suja da yaran jaguwa ba bare shi kanshi jaguwa , ni nan nafi karfinku nafi karfin hukuma kuma yanzu na sama addabar rayuwar manyan kasar nan   ya karasa maganar yana dukan qirjinshi yana murmushi ……

“Anyway nasan daga inda shiriku  yake kowanen daga cikinku ƙoƙarin raya kanshi  da ahlinsa yake ba domin kare kasa da kasa   kuke yin komai ba domin raya kanku kuke  ,dana soma wannan aikin domin ɗaukar ran wani  to da ina tabbatar maka  kai ne mutun na biyu bayan wancan tantarin tanko gote ….”

duk wannan  Maganar da yake yana yi yana jujjuya jikinsa  ne  kafin daga baya ya shafa fuskarsa ya cire  fuskar dake manne  da fuskarsa wata fuskar ta bayyana da tsananin kyau da sage zagaye daita  “ka kalleni da kyau sp yusif   muddin akaina  zaka samu double  promotion ina tabbatar maka  bazaka taba samu ba har duniya ta nade  saboda jaguwa mutun ɗaya ne mai fuska daban  daban  yana gama  maganar ya zaro  bindiga daga kugunsa ya  saita daidai  gwiwar sp yusif  ya sakar masa bullet biyu a jere   wata irin razananniyar qara ya saki tare da  durkushewa a gurin  “jaguwa ya nuna sa da bakin bindiga “bance ku daina farautata ba , sai dai ku shirya iya shiryawa kafin ku tunkareni  yana gama fadar  haka ya juya a fusace tamkar mayunwacin zaki  yana taku  kamar baya son taka kasa ya buɗe motarsa  ya shiga yayi mata key a hankali motar ke motsawa tana  moving  gbdy suka bi bayan  motar da kallon mamaki har sanda motar tayi musu nisa  …..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button