KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Ranar karasa yini sukayi cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa kowa ka kalli fuskarsa babu annuri ,kuma shiru har karfe biyar anas bai kira ba shima kuna bai kirasa ba kamar yadda yace ya bar wayarsa a kunne zai kira ,dan haka ya kira layinsa kira daya hally ta dauka tana gaishesa cike da girmamawa,bai amsa ba yace “ina Ana’s?”
“Yana bacci yaya bashi da lfy ko na tashesa ne ?”.
“No karki tashesa but idan shida tayi bai tashi ba ki tashesa kice ya kirani kinji “to !ta fada ya katse kiran yana runtse idanunshi ,kwakwaluwarsa tunani hanyar da zai fito da scorpion take ba tare daya dauki lokaci a hannun polisawa ba.”
daren yayi babu wanda ya runtsa acikinsu har anas dan sunyi waya daga baya kuma ya fada masa komai alokacin yaso zuwa shine ya hanashi hatta hally ta fahimci akwai damuwa sai dai tayi masa tambayar duniya yace babu komai allah allah ya dinga yi gari ya waye ya isa gidan su san yadda zaayi.”

Washegari

A hadadden falon jaguwa zaune wasu mutane suke akan kujera suna fuskantar juna daya sanye da bakaken kaya yayinda dayan ke sanye da fararen kaya  jaguwa na  zaune akan wata karamar kujera ya juya masu baya jikinsa sanye ciki blue black din riga da Wando gbdy yaransa suna tsaye ban da anas bai samu damar karasowa ba ,a hankali daya daga cikin bakin mutane da suke zaune ya fara magana cikin zafin rai “kasan irin hasarar da nayi dalilinka kuwa ?  kasan irin abinda na rasa dalilinka sakarcinka?” ko bakaji ina maka magana ne kayi banza da kanka wai kayi dani ? Jaguwa sam bai juyo ba sai danne danne yake acikin wayarsa zuciya tazo masa wuya damuwa kashi da kashi sun sanyoshi gaba .”
“ban da sakacin banza da rainin hankali irin na…….”Ana’s wanda ya karaso yanzu sanye da blue jeans da riga ash colour yayi taku daya biyu yana cewa ” kai kai kai  !!! Ya fuskanci wanda ke gabansa “da kai nake yin maganata wai meke faruwa ahankali ya juya ya kalli na bayansa ina tambayar wai meke faruwa abani amsa mana.” wai yanzu har kuna da zuciyar da zakuyi mana maganr akan wani abu naku bayan mun sha biya muku buririnkanku lokaci dayawa mun sadaukar da rayukanmu.”

ya juyo ya kalli mai farin kaya “bakasan iyakacin sau nawa bane muke shiga hatsari duk adalilinku ya karasa maganar yana nuna masa kofar fita da d’an yatsansa babu mutsu ya mike tsaye jiki a sanyaye “kunyi kuskure domin lokaci ya rigada ya canza ya kai hannu ya dafa kafafan jaguwa “wai me yake faruwa né ? “Kai kabasu dama su dinga mana magana irin haka inji cewar kamil ya fada yna fuskatar jaguwa ?.
Jubi yace “wadan nan fa costom department ne Kullum kawai matsalar jami’an tsoro costom gashi mu bamu da kowa acikin jami’an tsaro ,acikinmu babu wanda yake da halaka da polisawa sai dai da yarinyar minister  kawai ,shin yana haduwa da minister ne ko kuma da yarinyar minister  kawai , koma dai menene ita kan bata da wani amfani agurinmu ,gashi scorpion ya shiga hannu bamu san a wani hali yaje ciki ba ga wadan nan mayun kudin sunzo karbar kasonsu ,yanzu da me zamuyi amfani mu fito da scorpion “?

“Jaguwa shi ya saba sace yammata ya nuna kwarewa rasa ya sato mana karamar kanwar dcp bincike mu ya nuna wani sati zaa fara bikknta ya karasa maganar yana dariya ,gbdy suka sa dariya banda anas da jaguwa dan ransa a bace yake gbdy suka fita , falon ya saura daga shi sai ana babu wanda yayi mgn acikinsu wayar jaguwa ta soma ringin ya duba tanwer ce yaki dauka ta sake kira yaki dauka cikin haka wayar anas ta fara ringin ya ciro ya duba “tanwer ce ..” ya fada jikinsa a sanyaye “ka rabu da wannan yarinyar abinda nake gudar mata kenan ta kasa fahimta , irin wannan matsalar anas, nifa nasan da rayuwata da nata da kai da hally duk suna cikin hatsari yanzu kuma kaji abinda jubi ya fada ni ne na saba satan yammata ” yayi maganar tamkar zai zubar da hawaye “ka manta da maganr jubi ni ban damu da abinda yace ba .
Ya mike daga zaunen da yake ya goya hannunwansa duka a bayansa ya soma zariya acikin falon gumi na karya masa,hankali ya kamo lip’s dinsa na kasa ya ciza da karfi Ana’s ya karaso ya dafashi “dan allah karkasa damuwa aranka hanyar fito da scorpion ya kamata mu fara nema ,”yanzu ba wannan bane a gabana domin kuwa gabadaya nagama tsara komai na fitowars scorpion matsalar dai yarinyar nan tanwer halin zata shiga kawai nake tunani ranar dana shiga hannu .”…

Fatan munyi sallah lafiya allah maimata mana ,allah ya biya mana bukatunmu na alkhairi,allah kuma ya jikan iyayenmu,mu kuma allah ya gafarta mana .”
????????????????????????
KUSKUREN BAYA
     ????????????????
????????????????????????

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

????️40

“Ana’s yayi shiru yana kallonsa yana nazarin maganarsa “yanzu ba wannan bane a gabana
domin kuwa gabadaya na gama tsara komai na fitowar scorpion matsalar dai yarinyar nan tanwer halin da zata shiga kawai nake tunani ranar dana shiga hannu .”Ya maimaita maganar yafi sau uku acikin ransa yana dubansa tamkar ranar ya fara ganinsa,bama halin da mahaifiyarsa da kannensa zasu shiga ne damuwarsa ba halin da tanwer zata shiga ne yafi d’aga masa hankali “.?”lallai abinda yake gudar masa ne yake shirin faruwa dashi fad’awa cikin makauniyar soyayya .”

nan take shima zuciyarsa ta hasko masa matarsa hally baiwar allah “tabbas shima ita yafi ji da tausayawa ,gara ma tanwer tasan waye jaguwa da alqallarsa  shifa ?”.halima bata san komai akansa ba  ko ya zataji idan tasan alqallar mijinta da yayanta “?
“Subhallah ya furta a fili kana ya numfasa yana jin wani tashin hankali na sake mamayesa , jiki a Sanyaye ya soma magana  qirjinsa na dokawa “shiyasa nake gaya maka mu bar sana’ar nan idan ta kama ma sai mu canza gari mu cigaba da rayuwarmu da iyalinmu tunda babu wanda yasan ainihin fuskokinmu “ana wata magana anas kana wata “ yayi mgnr a fusace  wanda a zahiri ake iya gani jijiyon kansa da suka tashi sukayi rudu rudu “kana ganin barin wannan sana’ar kai tsaye ko canza gari abu ne mai sauki .?”bafa abu ne mai sauki ba  kamar yadda hasashenka yake hango maka   .”

Dukkaninsu shiru sukayi suna duban juna suna tunani me zurfi kafin daga baya anas yaja numfashi da karfi ya sauke “to yanzu taya ka tsara fito da scorpion ? hanya daya ce na tsara ,rike wuyan dcp ,”taya zaka samu damar isa inda yake bare ka rike masa wuya ?”Ka kwantar da hankalinka kana nan   zan fara aiwatar da komai amman ni kadai zanje gurinsa ,”bazan iya barinka kaje kai kadai ba saboda ina matukar bukatarka araye banason kayi kasadar daka saba akanmu,idan kuma lallai sai kayi kasadar sai dai muje tare amman bazan iya barinka kaje kai daya ba .” ya karashe maganar cike da rauni .”na sani ana’s kana gudun wani abu ya sameni kamar  yadda nima  ina jin tsoron abinda zai sameka,abinda zai sameka idan ina da dama kafin  ya sameka  ya fara samuna  bare  kuma babu abinda zai samemu daga ni har kai saboda bamu  rayu dan mu  matu a hannun makiyanmu  ba ,dan haka ka kwantar da hankalinka anas babu abinda zai faru dani  zan tafi kuma ni kadai , Kai dai kayi min addua kawai  shine abinda nafi bukata daga gareka .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button