KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“suna dayawa fa kana ganin zamu iya dasu gbdy ?me yasa kayi wannnan tamabyar ?bansan dalilin ba amman haka nan nake  dan jin tsoro yin aikin .”shiru jaguwa yayi yana kallonsa up and down yana taba qirjinsa sannan yace “why anas?  akoda yaushe ina fad’a maka ka dinga  karfafa zuciyarka  ka cire tsoron a ranka babu abinda zai faru damu ,please  ka kwantar da hankalinka a yanzu nima na soma hango haske acikin maganarka zan  yi kokari na dawo kan hanya  kamar yadda kake bukata amman kafin lokacin akwai bukatar muyi komai cikin tsare…..”
“ba tsoro bane adnan wallahi bana son hally ta rasani ne adalilin akin nan ni kaina  yanzu  na fara jin dadin iyalina  ka fahimceni kai kanka kasan aikinmu akwai hatsari, ada rayuwarmu kawai muke ko mutu ko mu rayu amman yanzu fa?”ina da hally acikin rayuwata kai ma kuma ina fatan nan kusa ka ajiye tanwer a gidanka  for how long zamu d’au….”qarar bude kofar dakin da suka ji  ne ya katsesa sky ne ya shigo hannnsa rike da farar takarda guda uku “boss ga sakon bayanai nan mlm mudi ya turo ta system gashi har na yi prit dinsa out ,okay sky ja  ajiye a can ya ajiye akan table ya juya.”
“Am sky yayi saurin juyowa da sauri cike da respect ,
ka kawo min bakin shayi yanzu “okay boss ya fada tare da juyawa ya fice daga dakin .

Anas ya dan yi murmushi ya cigaba da magana “rayuwar yanzu data da ba daya bace agurina ina matukar son halima kamar yadda kasani banason na bar rayuwarta cikin kuncin da matsalolin rayuwa , cikin haka  sky ya sake yin knowking ya shigo hannunsa rike da farin glass cup mai dauke da ruwan coffee mai zafi  ya ajiye ya juya ,jaguwa na kokarin daukar cup din coffee wayar anas ta soma ringing dan haka ya dakata  yana son sauraron yaji daga ina wayar tace  .
  Ana’s ya  zaro wayar  daga cikin aljihun gaban rigarsa yana kallon screen din wayar my princess wife ya gani  yana yawo daman da sunan da yayi saving kenan  ,ya lumshe idanunshi yana jin sanyi na ratsa sansar jikinsa ya dauka tare da rage sautin muryarsa “my princess ya kike ya jikin naki hope kin dan samu relief ?okay to shikenan my princess wife ki kular min da kanki gani nan dawo wa yanzu  ,
jaguwa ya maida hankalinsa sosai akansa “ina sonki sosai my princess wife bazan jima ba  muradin raina da wannan kalmar ya kawo karshen maganarsu ya katse wayar da murmushi akan fuskarsa.”

“muradin ranka anas a kuma gabana ko  kunyata bakaji ba kamar ni ba surukinka bane ?wani kunya kuma adnan a zaune kalau ?ai maganar wata kunya ta kare kaga bari na wuce gida my princess wife bata da lafiya gashi har uku saura ya  juya , har ya  kusan bakin kofa ya tsaya sakamakon jiyo sautin muryar jaguwa data fito a hankali ,”gbdy maganganunka kunya suke bani anas,Karsu baka kunya adnan ka dai yi kokari Kaima   ka mallaki muradin ranka zai fiyye maka ya sa kai zai  fice daga dakin yana murmushin tsokana shima jaguwa yayi murmushi yana shafa sumar kansa  yace “ka shigo gobe da wuri please mu fara tsara abubuwa “okay ya fada tare da karasa ficewa.
Numfashi jaguwa ya sauke yana jin dadin yadda anas ke kulawa da kanwarsa gbdy rayuwarsa ma ta sauya ya daina shan giya yanzu iyakarsa sigari shima sai idan yaga yana sha ne .a hankali ya karasa ya dauki farar takardar da sky ya ajiye yana dubawa a tsanake yana kurban coffee at the same time kuma yana cizan lip’s dinsa na kasa yana jin faduwar gaba  akan tanwer duk sanda ta fado masa sai yaji gabansa yayi mummunar faduwa gashi yanzu duk bayan sakonni take fado masa yaji kamar yaje gidansu ya ganta  amman bazai iya ba .

Hally kuwa tunda anas ya fada mata kalamansa masu sanyi taji ta sake nitso acikin soyayyarsa “kece muradin raina ta maimaita tana lunshe ido “nima kai ne muradina ,karfe hudu na yamma tai wanka tai kwaliyya kamar jiya sai dai kayan datasa ba irin na jiya bane dinki atamfa ne sai dai su din ma sun dan matseta daga kirji ta canza tasha zuwa zeeworld alokacin ana wani film din india mai kyau kuma na soyayya (sanam teri kasam ) daman itama mayar son kallon film din india ce karfe biyar yayi sallama taji matukar dadin dawowarsa ji tayi kamar ta tashi ta rungumeshi ajikinta bai shigo ba ya tsaya a bakin kofa .
Ta kallesa tace “Lafiya ka tsaya anan?”
Ya dan daga kafada “bazan shigo ba sai da kulawarki tayi murmushi tana mai tsaida idanunta akanshi “kulawa kuma tame “?ai ya kamata na samu ko yar runguma ne ayi min ko ba haka ba ?Tayi kasa da idanunta ta gyara zamanta babu alamun zata tashi “da gaske fa nake idan baki taso kin rungumeni ba alamar barka da dawo wa a haka zan ta tsayuwa bazan shigo ba gashi kuma na dauko yunwa .”

Jikinta a sanyaye ta tashi ta nufi inda yake tsaye yana aiko mata da kallon love sai dataje daf dashi sannan ta tsaya “to shikenan ka rufe idunka ya kuwa rufe a hankali ta karasa ta rungunesa tsam,shima ya hadeta acikin hannuwansa ya rungumeta ajikinsa yana shafa gadon bayanta “my princess wife nayi kewarki duk  abinda nake hotonki nake gani na tabbatar dana bari na kai Kmr jiya zaki sha mamaki domin zan iya ramewa.”

Tayi murmushi “ramewa kuma ?”Wallahi zan iya ramewa domin kawai tunaninki nifa kin kara siyo min wata kima da daraja agareni sonki ya ninku a zuciyata fiyye da wanda banyi tsammani ba ina jinki a sahun macen da ko mutuwa idan ta rabu mu ita kanta tasan bata mana adalci ba ,ya dan zareta ajikinsa yana kallonta  itama shi din take kallo da kwayar idanunta  ya kai hannunsa yana shafa lip’s dinta “ban taba jin bakinki ya fadi irin haka ba ina son nasan yadda kike jina acikin ranki “.Taja hannunsa zuwa kan table domin abincin rana datayi bata dauke shi ba yana cikin flak’s “kace kana jin yunwa?”
“Eh ina jin yunwa amman kuma bazan ci abincin ba sai kin gaya min yadda kike jina acikin ranki “ka fiyye fitina yanzu  ya anas mai yasa ne ?”saboda na damu dake  ne kuma mutuwar sonki banason abinda zai nisantani dake my princess ya fada idanunshi na kanta ta danyi kasa da idanunta a hankali ta soma motsa lips dinta “ina… ina ..” sai kuma kunya ta hanata furta abinda take son fada masa .

da murmushi ya sumbace kumatunta suka zauna bisa table “zanso ace muna rayuwarmu kullum atare batare dana fita zuwa koina ba amman ina hakan ba mai yuwa bane kullum cikin aiki muke ta dago ta kallesa daga zuba masa abincin da take “haka ai shine daidai ,abun haushi ma gobe akwai aikin da zamu fitar dani ta sake dagowa da murmushi a fuskarta “meye abun jin  haushi aciki dan zaka fita nemo mana halal?”.nan take yanayinsa ya sauya zuciyarsa ta soma rawa  ,yayi shiru  yana kallonta cike da tausayawa “karka damu nasan na dan kewar juna da zamuyi ne wannan kuma na dan wani lokaci ne kawai ta ajiye abun zuba abinci ta kamo hannunsa  cikin nata ganin yanayinsa ya canza “haba mana ya anas ai baa acan zaka  kwana ba da ka wani canza Kmr idan ka fita goben bazaka dawo ba ?”

Yayi saurin girgiza mata kai “to ko na shirya goben muje tare ne ?ya harareta cikin tsigar wasa yana dawo da natsuwarsa “allah sai muje tare,shimkenan zan muje tare amman a zuciyata zan miki kyakkyawan riko ya fada yana shirin fara cin abinci .”Sarai ta gane ba zuwa zaiyi daita ba “ai kuwa idan bakaje dani ba bazamu kwana tare ba ya dago yana dariya “ai kuwa yarinya baki isa ba ai daga yanzu kullum tare zamu dinga kwana har na samu na isar da duk sakonnina gareki inda da rabo har baby ya samu ya shiga ,hararsa tayi tare da yin shiru ya bita da kallo “kinyi kyau sosai my princess wife kamar a India tayi murmushi gefen baki “ai duk kyau na ban kai matar jiya daka zage kana ta faman kallonta kana murmushi ta cikin wannan film din na jiya ya danyi dariya ya ajiye spoon a gefe ai yarinya tayi kokari ne ko ba haka ba ?”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button