KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

a hankali minister ya k’arasa Inda take ya rikota “dan Allah ka barni karka tasheni a mafarkina “cool down Zainab wannan ba mafarki kike yi ba it really gaske ne tanweer diyarmu ce kwance a gabanki tana jin abinda ya fad’a ta gyara tsayuwarta sosai ta tsaya bisa kafafunta tana maida hankalinta sosai akan tilon diyarta da sauri ta shiga daga kafafunta tana mai zubar da hawaye Wanda take Jin radadinsu har cikin ranta ta k’arasa Inda take kwance ta d’aura hannunta akan sumar kanta mai tsantsi ,ta dinga binta da Kallo “mai ya sameta na ganta haka ?sun cutar min da yarinya ko ?”sun lalata min rayuwar yarinyata ko? tayi masa tambayar ajere hawaye masu zafi da ciwo na sake zubo mata akan quncinta “ki kwantar da hankalinki tukun nan ba’a dubata ba tana dai hutawa ne “.
“Allah kasa basu cutar min da yarinyata ba ta k’arasa maganar tana sheshekan kuka tare da tsurawa tanweer idanunta , qauna da tausayin diyarta suka lullu’beta gbdy ta kasa d’auke idanunta akanta ,yarinyata tayi kyau sosai tamkar ba daga hannun yan’ta’adda ta fito ba skin dinta sai wani sheki yake .”naunayen ajiyar zuciya hjy zainab ta sauke tana cewa”Kasan san Allah zuciyata rawa take sosai akan tanweer jikina na bani an ta’ba min yarinya. “ki kwantar da hankalinki sannan ki sawa ranki komai ya faru damu daga Allah ne mu ma godewa Allah da muka ganta a raye Kuma cikin koshin lfy ….”inshallahu ma babu wani abu nasan Kai din mutumin kirki ne da yarda Allah kamewarka da jin tsoron Allah’nka bazai sa wani abu ya samu tilon diyarmu ba tana gama fadar haka ta mike rike da wayarta tana kokarin neman layin hjy baseera “
da sauri Minister ya rike mata hannu “wazaki kira a daidai wannan lokacin”? ” hjy baseera ta bashi amsa da haka “karki fara Kiran kowa tukun nan mubari musan matsayin da diyarmu take ciki, yanzu ma gida zamu wuce mu Barta har zuwa gobe idan Allah ya Kai mu sai dawo.
“Da wani kallo tabishi dashi sannan tace “kana tunanin zan iya barin tanweer ne a wannan halin “?idan ma naje gidan me zanyi “?ai zuciyoyinkmu bazasu samu natsuwa ba gara dai mu zauna tare daita ya sauke numfashi yace “haka ne ya fad’a a filin dan yana wa tanweer wani so da bai tabawa wani hallita a duniya ba .
Duk maganar da suke tanweer na jinsu dan tuni ta Farka tun shigowar mumy sai dai ta Kara runtse idanunta sosai dan karsu fahimci ta Farka tausayin iyayenta ya sake rufeta “kuyi hakuri iyayena komai muqaddari ne daga Allah Kuyi min addua kawai domin abinda kuke gudun faruwarsa tuni ya faru an raba tanweer dinku da budurcinta..

shiru tayi hawaye na gangarowa akan pillow da kanta yake kwance tana kukan zuci gefe guda Kuma bata ganin hotunan kowa face na Adnan dinta tana tsananin sonshi tasan ba Abu ne mai sauki ta daina tunaninsa ba.
a hankali hjy zainab ta dafa kanta wani zafi taji ya ratsa tafin hannunta ta bud’e baki kenan da niyyar yin magana sai sukaji an turo kofar d’akin an shigo wasu likitoci ne suka shigo d’akin sanye da kayansu na aiki sai dai puppy ne amadadin fari suna ganinsu suka dan ja baya domin basu damar suyi aikinsu .
Byn sun gaisa d’aya daga cikin likintan tace “Dan Allah ku dan je daga waje ta basu umarmin fita jiki a sanyaye suka fita .
Cikin kankanin lokaci likitan ta fara aikinta cikin iyawa da kwarewa har ta gano komai akan abinda minister yake bukatar sani, tana gamawa tayi rubuce rubuce a file din tanweer da’aka bude mata har za ta juya domin barin d’akin zuwa office dinta tanweer tayi saurin riko mata hannu tana cewa”doctor dan Allah karki fad’awa iyayena komai da kika gani .
“why “? doctor ta tambayeta shiru tan tayi kafin daga baya ta sake Bude baki da kyar “banason iyayena su shiga damuwa ne”.
ba haka aikinmu yake ba dole zan sanar musu domin idan wani abu ya faru a gaba zasuyi kuka dani doctor na gama fadar ta fice dan oready dayar likitan ta fita .”

Minister na gani fitowar doctor ya biyo bayanta da sauri kusan atare suka shiga office dinta .
zaune yake a gaban doctor yana sauraren bayaninta daki daki a natse take sanar masa diyarsa ta san nmj ba kamar yadda yayi tunani ba . wani irin bugawa qirjinsa yayi da matsanacin karfi take gumi ya shiga tsatsafo masa ta koina ajikinsa “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun allumma ajirni Fi musibatihi waklifni khairan minha “an yiwa diyarsa fyade kenan “? inna lillahi ya sake furtawa, kenan ta wannan hanyar Allah zai yiwa ya’yan mutane sakayya ? Allah yayi iKonsa da qudirarsa bai san lokacin da hawaye ya shiga zubo masa ba abun yayi matukar taba zuciyarsa Kuma yaji zafin abun sosai “likita ta maida kanta ta cigaba da rubuce rubuce hanky ya ciro a gaban aljihunsa ya goge hawayensa “likita Ina son ayi mata wanki mara “.likita ta sake dagowa tana dubansa sannan ta lumshe masa Ido alamun taji.
ya mike ya dawo d’akin Inda ya iske hjy zainab ta tasa tanweer gaba tana dubanta cike da farinciki ita Kuma tan hannunta rike da cup din ruwan zafi tana kurban tea a hankali , kallo d’aya tanweer tayiwa mahaifinta ta fahimci an fad’a masa komai .
“Mai likita tace “?
bai boye mata komai ba ya fad’a mata har ma da abinda yace likita tayi ,a razane hjy zainab take kallonsa sannan ta juya ta surawa tanweer Ido “da gaske sunyi Miki fyade “? Tan tabi mahaifiyarta da Kallo domin rasa abinda zata ce mata.
Ganin tayi shiru kawai hjy zainab ta fashe da kuka .
Kuka take sosai tana tsinewa jaguwa Allah bazai barsu ba hakika ya zalinceni ko ta wacce hanya sai Allah ya Saka min sai yaga sakayya sai …” tanweer tayi saurin matsowa kusa daita “no mumy stop “!
“Stop what “?
“Me kike nufi da stop “?
“Bana nufin komai mumy amman ki daina tsine musu ki barni naji da abinda nake ji a halin yanzu ,mumy wallahi nafiki shiga bakinciki abinda ya faru dani ta fada tana goge mata hawaye “ki daina kuka mumy na yarda da qaddara muyi Imani daita su Kuma idan masu shiryuwa ne Allah ya shiryesu idan bama su shiryuwa bane Allah ya tona musu asiri….” Bata gama magana ba mumy ta karbe “nifa wallahi bazan daina tsine musu ba har na koma ga Allah tan ta runtse idanunta”oh !Ni dai nace ki barsu ta fad’a tana d’aura kanta a kirjin mumy “mumy banason wankin marar nan Allah zafi garesa kice wa dady abarshi kawai .
“Ina bazai yiwu ba gara dai ayi idan ma da wani abu yayi gaba shi dai dady shiru yayi kawai yana kukan zuci ba shakka ba’a cin bashin Allah duk daren dadewa sai ya d’auki fansa bama mutuen kirki ba suka d’auki fansa yan fashi yan taada wannan abu da ciwo yake ciwon da bai san ranar da zai daina jinsa ba .”

“Mumy bari nayi sallah ko ? ta fad’a tana kokarin saukowa Ina ne bayin? Shi dai dady tsaye yayi yana kallon ta zuciyarsa na bugawa ta zura takalminta tana sake kallon dady “dan Allah dady kar min wankin mara da zafi sosai” ke dai kije kiyi alwala kiyi sallah Amman bazamu barki haka ba dole ayi tan tace “uhm dad tare da shigewa bayi .
Tayo alwala ta fito mumy ta shimfida mata dankwalinta tayi sallah suna zaune suna jira ita Kuma taki tashi dan bazata yarda a mata wakin mara ba zafi garesa tayi shiru akan sallaya tana zullumi gbdy a tsorace take ta marairace fuskarta “dan Allah dad mumy kuyi hakuri wallahi bawai banaso bane zafi garesa “karki tsorata ki bari ayi a gama komai shine kwanciyar hankalinmu kefa likitace kinsan illar abinda kike son yiwa rayuwarki”. tayi yar murmushi yake wanda yafi kuka ciwo “shikenan zanyi da kaina. “yarinya jikinki zai gaya Miki gara ki bari ayi Miki allurar bacci ayi Miki cikin sauki inji cewar mumy taja kujera ta zauna tana nuna damuwarta .
tan ta kauda fuska “ni dai gsky zanyi da kaina dama mun wuce gida a yanzu tayi mgnr cike da shagwaba .
“iKon allah akwai aiki a gabansu inji cewar mumy “kinsan Allah baki Isa ba bazan d’auki wannan kasardar ba “to mumy amman Ina rokonki ki barni babu abinda zai faru nasan kan aikina bama lallai sai anyi wanki mara ba akwai table din da zan sha da zai maye gurbin wanki mara ganin ta nace sai da tayi da kanta suka hakura tunda sun san tasan aikinta dady ya zauna akan Baki gado ya d’aga kan tan ya d’aura akan cinyarsa yana shafa sumar kanta .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button