KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Jaguwa,anas,kamil duk suka shigo dakin daaka kwantar daita suka zuba mata idanunsu cike da tausayawa suna dubanta ,a hankali jaguwa ya lumshe idanunshi tare da kai hannunsa daidai saitin qirjinsa dake bugawa very fast yana shafawa ko zai samu sausauci yanayin da yake ji ,kodaudun idanunshi ya bude sosai akanta tana kwance tana sauke wahalallin numfashi ,ya sauke ajiyar zuciya ahankali wani abu mai daci daya tsaya masa a makoshi ya hadiye a tun sanda hatsarin ya faru .
“da wani abu ya sameta bai san yadda zaiyi da rayuwarsa ba ,ya qara taku biyu ya matso kusa daita sosai ya kai hannunshi bisa suman kanta dake zube akafadanta yana shafawa yana maida numfashi a hankali .”wasu irin abubuwa yake jin suna masa yawo a sansar jiki suna ratsa jinin jikinsa gbdy , nan take tsigar jikinsa suka mike yana jin ina ma ciwon ya dawo jikinsa ……”
Cike da natsuwa anas ya matsoshi ya dafa kafadanshi gbdy yanayinsa ya canza kallo daya zaka masa ka fahimci baya cikin natsuwarsa idanunshi sun canza kala sun sake cika taf da ruwan hawaye alamun zai iya zubar da hawaye akowani lokaci ,cikin tsarkewar muryar anas yace “please adnan ka kwantar da hankalinka inshaallahu babu abinda zai sameta zata samu lafiya har ma ta kaiku ga yin aure .”ya juyo a natse ya tsurawa anas idanunshi da suke cike da kwalla amman ya kasa cewa komai , dan bama zai iya furta masa komai din ba burinsa a yanzu yaga ta bude idanunta akanshi cikin koshin lafiya har ma ta kira sunansa da zazzakar muryarta “adnan dina yaji kuwan sautin muryarta acikin kunneshi yaushe ka dawo da baka fada min ba “? ya rasa wani irin so take masa gashi nan adalilin haka tayi masa ganganci da rayuwarta.
“Ya kamata zuwa yanzu mu wuce kafin karasowar iyayenta ,qasa yayi da muryarsa yana cewa “bazan iya barinta cikin wannan halin ba,kona tafi zuciyata bazata samu natsuwar da kake bukata ba kawai ku tafi ni zan zauna tare daita.”
“No no zamanka anan akwai damuwa domin komai zai iya faruwa most especially idan iyayenta suka karaso tunda sun rigada sunsan komai akanka “I don’t care da sanin komai da suka yi ,bazan damu dan sun iskeni anan ba yayi mgnr Kmr zai zubar da kwalla, anas da kamil suka juya suka bar dakin suka bar jaguwa ya cigaba da tsayuwa ya tatttara gashin kanta zuwa bayanta still idanunshi na kanta yana kallonta kmr zai maidaita ciki .

Hankali a matukar tashe mumy tashigo dakin rukayya na biye daita jaguwa ya zabura ya mike tsaye qirjinsa na wani irin bugawa da karfi bai san yana da tsoro ba sai daya ga mumy ,ta nufo tanwer tana cewa “rukayya meke faruwa da tanwer dina?” ta fada hade da kokarin taba tanwer mumy acci…”tayi saurin katseta ta hanyar cewa “Shine nake tambayarki a waya kika gagara fada min ?”
Ta karasa mgnr a tsawa ce “garin ya ya hakan ya faru da tanwer dina?” Gbdy ta rude tana tmbyr rukayya dan sam bata fahimci waye a tsaye yana kallonsa kasa rigarsa da jini ba har kusan min biyar yana tsaye bai daga kai ya kalleta ba saboda tsananin fargaba da tashin hankalin daya tsinci kansa, ya juya jiki a sanyaye ya bar dakin sai dai kasa tafiya ya koma koridoor dake gaban dakin ya dinga kai kawo yana duban gaban rigar jikinsa sai yanzu ya fahimci ta baci da jinin tanwer .
naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfi sannan ya tura hannuwansa duka cikin aljihu wandonsa yana ciza lips dinsa na kasa ,mumy ta zauna abakin gadon da jaguwa ya tashi tana duban fuskar tanwer nan take hawaye ya cika idanunta har ya soma zuba akan hannun tanwer dake rike cikin nata ta dade zaune sannan ta yunkura ta fito waje a koridoor ta sameshi zaune akan doguwar kujera yayi tagumi da hannuwansa duka fuskarsa na kallon kasa yaji alamun tsayuwar mutun amman ya kasa dagowa yaga ko waye ya cigaba da kallon kasa .
“Mumy shine mutumin daya taimaka ya kawota asibiti “waye shi ?”I don’t know him ta fada a matukar tsorace , ita kuwa ta fadi haka ne saboda tasan muddin tace shine adnan din da tanwer take mutuwar so zaa yi dauki ba dadi tunda tasan yadda suke kyamar soyayuarsu , a hankali ta karasa har inda yake zaune“sannu malam mun gode fa allah ya saka maka da mafifinci alkhairi yadda ka taimaka ka ceci rayuwar diyarmu kai ma allah ceci rayuwarka tana gama fadar hk ta juyawa ta nufi hanyar fita kunneta manne da waya tana magana da dady “.

rukayya ta karaso inda yake “please ya dace ka wuce gida haka kafin dady ya karaso wani irin dagowa yayi yana mata wani kallo da yasa kayan cikinta juyawa kafin a hankali ya mike ya sake komawa dakin da tanwer take kwance ya tsaya agabanta kallonta kawai yake cike da tausayawa har baya qaunar ya dauke idanunshi akanta wanda ita sam batasan yana yi ba ,ahankali ya matso kusa da fuskarta yana hura mata iskar bakinsa at the same time yana shakar nunfaahinta sai kusan goma saura ya fito daga dakin jiki a sanyaye ya shiga mota zuciyarsa na bugawa da karfi eku ya jashi suka fita daga hospital tafiyar mintuna talatin ta kawo su gida eku yayi parking ya kashe motar ya fito yana tafiya yana balbale botiran gaban rigarsa kai tsaye hanyar bedroom ya nufa yana karasa cire rigar gbdy ya shiga bathroom zuciyarsa cike da tunanin halin daya baro tanwer.
Shima dady agigice ya shigo dakin “Me ya samu tanwer?” inna lillahi me ya faru da ita please dady ke tambaya rukayya dake rarrashin mumy muryarta a raunane tace “ tsautsayi ne dady ku mata addua inshaallahu zata samu lafiya dady ya kalli mumy yana shafa kan tanwer “please karki kuka zainaba babu abinda zai samu tanwer dinmu zata samu lfy zata dawo daidai muyi wasa muyi dariya kamar yadda muka saba bazamu rasata ba , duk da zuciyarta na cike da jin haushin laifin da yayi mata amman sai daya bata tausayi ta matso ta rungumeshi tana kuka “ina son tanwer bana son na rasata “bazamu rasata ba inshaallahu sai munga yayanta “.

Jaguwa ya jima a bathroom cikin halin tunanin kafin yay wanka ,ya nemi rigar towel tare da towel dinta ya lullube koina ajikinsa ya fito ya dan leko yana dube dube yayi saa ganin fitowa anas daga dakinsa cikin sauri ya nufosa alokacin da ya juyo ya koma cikin dakin,anas ya murda kofar ya shiga yana kiran sunansa, ya kallesa cike da manaki “adnan yaushe ka dawo gidan nan ? .
“Ban jima ba ya fada ,shiru anas yayi yana sake kallon jaguwa fuskarsa cike da zullumi da fargaba yace “ka samu natsuwa please kai kasan rashin samun kwanciyar hankalinka daidai yake da nawa rashin kwanciyar hankali , jin haka yasa jaguwa ya sakar masa murmushin karfin hali,”Na kasa jurar ganin tanwer da ciwon nan , da mutun na cirewa wani ciwo wallahi dana cire mata na dauki nauyinsa. “ba cire ciwon yafi dacewa kayi ba ka aureta shine kawai abinda zaka mata ka samar mata kwanciyar hankali”bai sake cewa komai ba dan yasan ba abu ne me sauki da yuwu ba agaresa .
“Me zakaci naje na siyo maka?jaguwa ya kallesa sannan ya kalli agogon dake manne a parlaur’sa karfe shadaya ta wuce muryarsa a kasalance yace “karka damu “haba adnan duk wunin yau fa ina lura da kai baka sakawa cikinka komai ba ka daure kaci wani abu,bazan iya ci bane anas“okay bari na hada maka coffee first ka fara sha ya juya da sauri bai dade ba ya dawo ya mika masa cup din tangaram “ka dan sha please cikinka zai warware har ka iya cin wani ba ,zanje checking republic yanzu zan dawo ya juya da sauri ya sake fita .
jaguwa ya fesar da numfashi yana jin wani irin faduwar gaba mai tsanani ya samu guri akan kujera mai zaman mutun uku ya zauna yana kurban coffee ahankali, hoton fuskarta ya shiga gani acikin kwayar idanunshi yana jin wata irin tsantsar soyayyarta na ratsashi shi fa duk daukan da yake zai iya cigaba da rayuwa ko babu ita a she babban kuskure ya tafka bazai iya ba,tabbas bazai iya cigaba da rayuwa babu ita ba dan yana mata soyayyar da bazata misaltu ba zuciyarsa bata bugawa in har babu tunaninta sai dai kash aurenta kuskure zai yi akan KUSKUREN BAY

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button