KUSKUREN BAYA 1 TO 48
Numfashi jaguwa ya furzar ya mike tsaye zai bar daki “ka maidani gidanmu plz yaji sautin muryarta cikin sanyi ya doki dodon kunnenshi “nasan ka taimaka min ,ka karasa taimakon ta hanyar maidani ga iyayena “idan kina bukatar zuwa gida ki ci abinci kina gama ci ko second biyu ba zaki kara a cikin gidan nan ba zan maidake gaban iyayenki “yana gama fadar haka yaga ta matso da kujera da take zaune ta bude kwanon abinci daya fara yin sanyi ta soma tsukura ….” wayarsa ce ta dauki qara sauti ya ciro wayar daga cikin aljihunsa yana duba screen din wayar sunan Alh Tahir ya gani yana yawo ya lumshe idanunshi sannan ya dauka batare da yayi magana ba “cike da in inna alh Tahir ya soma magana “har yanzu baka dawo da yarinyar nan ba gashi akwai next taget dina akanta ya kamata zuwa yanzu kasan yadda zakayi ka dawo daita plz “doka ce ko iko kake son min ? ya furta masa haka a natse wanda zaka ɗauka maganar ba daga bakinsa ya fito ba sai agurin alhaji Tahir kamar saukar aradu yaji maganar .
saurin girgiza kai Alh Tahir yayi kamar yana gabansa “no babu ko daya naga dai ya kamata ne a dawo daita haka nan “to baza’a dawo daita ba kayi duk abinda zakayi ya ja tsaki yayi disconneting din kiran ya maida wayar cikin aljihunsa tare da zura hannunwansa ciki ya juya “ki tabbatar da kin ciye abinci nan tass kin shanye driks da ruwa ke everything dake gurin make sure kin gama dashi idan kina son barin gidan nan “, Allah bazan iya cinyewa ba yanzu ma da kyar nake tura wa “,Karki yi kiga abinda zai faru “ya karasa maganar yana barin dakin kai tsaye bangaren daya tanada domin shakatawa ya nufa a can ya iske abokansa da yaransa suna shaye shaye , masu shan wiwi nayi masu shan win nayi, duk sun cika gurin da hayaniya da hayaki suna ganinsa suka hau sara masa suna masa kirari gutun wiwin dake rike a hannun jubi ya amsa ya ɗan zuka yana fitar da hayaki ta hancinsa da bakinsa sannan ya fita ta kofar baya yana tunanin mugun hali irin na Alh Tahir ko me zai yiwa ƙaramar yarinya kamar wannan gashi kuma shi din aminin mahaifinta ne?
Kusan minti goma yana tunanin agurin “
“Wai Ibrahim kana so ka kashe kanka ne akan mace”. Momynsa tayi maganar cike b’acin rai wanda ke had’e da tsantsar damuwar halin da d’anta ke ciki. “Momy I can’t live without Tan, ta riga ta zama rayuwa ta, inda abunda nakeso bai wuce Tanweer ba Mo…”. “Dakata!”. Ta katse shi ta hanyar daga masa hannu da tare da mai tsawa. “Ibrahim bazan taba son ka rasa ranka akanta ba duk da nima ina matukar kaunarta saboda irin son da kake mata ,but at least ka duba lamarina kai kad’ane d’ana taya zanso akan wata ‘ya mace wani abu ya sameka ?”.
Tayi maganar tana kallon Ibrahim wanda tunda ta soma maganar idanunsa ke runtse.
“Ibrahim!”. Ta kira sunansa cikin wani irin yanayi wanda bai taba saninta dashi a rayuwarsa ba” gaba daya Inaso kayi hakuri da Tanweer!”. Ta karashe maganar cikin dakiya tana kallonsa ganin yadda har ya samu courage d’in tashi zaune shida tun b’atan Tanweer bata ganshi a zaune ba.
“Mom!”. Ya fada cikin daga murya tare da gyara zamansa yana binta da wani irin kallo idanunsa ko kiftawa ba yayi, already ya gama zazzarosu waje gaba daya what !”. Yayi maganar yana kallonta kamar bai fahimci abunda yake faruwa ba musamman furucinta. “Mom!”. Ya Kuma fad’a yana kallonta cike da mamakin furucinta.”Haba Momy, taya zakiyi wannan furucin na rabu da Tanweer bacin kinfi kowa sanin irin son da nake mata? How could you utter such words uhm?!”. Ya jero mata tambayoyin cike da damuwa lumshe idanu tayi tare da fadad’a murmushinta tana shafa sumar kanshi.
“Ibrahim kenan,”. Ta fada tana kad’a kanta ,sannan ta tashi ta soma taku yana binta da koda’dd’un idanunsa da suka sha wahala saboda rashin ganin abincin su Tan, har ta Kai k’ofa sai Kuma ta juyo tayi murmushi me sauti tana kallonsa lokaci guda Kuma fara’a dake tattare da fuskarta ya d’auke nan take bacin rai ya maye gurbinshi.”Hmm! Yaro yarone nan gaba zaka gane da kanka nasan dalilin da yasa nace ka hakura da yarinyar nan “. Tana fad’in haka ta fice ta barshi zaune zuciyarsa cike da tunanin zantukan ta musamman bacin rai daya hango cikin idannun Momyn nasa wanda kusan ya jima baiga hakan tattare da fuskarta ba. Wayarsa da ta soma ruri ne ya katse mishi tunanin daya shiga ya soma zurfi, hannunsa na rawa ya kai hannunsa ganin me kiran, da sauri ya manna wayar a kunnensa banajin me ake fada masa a can d’aya bangaren naga ya tashi da sauri. “What?!”. Ya furta da d’an k’arfi tare da runtse jajayen idanunsa ya bude su tuni suka k’ara rinewa tare da k’ara tiruwa zuwa ja sosai kamar jan gauta. “Alright I am coming”. Ya fad’a da sauri tare da wullar da wayar kan bed d’insa.
Yunku’rin k’arasawa wardrobe yayi amma me wani irin jirine ya kwasheshi da sauri yasa hannayensa akansa saboda wani irin nauyi da rada’dd’i da suke masa, yana ciza pink lips d’insa kanana wanda suka sauya colour saboda azabar ciwo a d’an bushe “Ya Salam I.B!”. Dadynsa ya furta wanda ya bud’e ko’farsa kenan a daidai lokacin da I.B ke ko’k’arin k’arasawa k’as, cike da matsanancin tashin hankali Alh.Tahir ya k’arasa ya tallafoshi zuwa jikinsa inda yak’arasa sauke su kan bed d’in. “Ta…Ta…Tan! Da….”. Karasa kulle idanunsa yayi hankalin Alh.Tahir ya tashi a wannan lokacin banda ihun kiran sunan matarsa cikin tashin hankali babu abinda yake dan ya fara tsorata da yanayin dan nasa ..”
????????????????????????
KUSKUREN BAYA
????????????????
????????????????????????
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686
alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
????️12
……Cike da dakiyar zuciya alqali ya cigaba da bin bayan motar jaguwa land cruiser prador yana sake neman layin IB domin bashi direction din Inda yake a daidai wannan lokacin sai dai Kiran na shiga ba’a d’auka ,ya kira ya kai sau goma bai d’auka ba wanda a wannan lokacin nazifi da alhj Tahir da hjy baseera ne tsaye a kanshi nazifi na qakokarin bashi taimakon gaugauwa , haushi ya kama alqali ya ciza gefen lips dinsa yana dukan sitiyarin motarsa “oh my goodness ko me yasa yaki d’aukar Kiran yanzu bayan bamu gama wayar ba ya ajiye ? yayiwa kanshi tambaya yana d’an rage gudun motarsa dan kar jaguwa ya fahimci su yake bi .”