KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Ahankali  suka   dubi dady  suka  gaisa kafin  su sake wata magana  dady ya fad’a musu komai dake faruwa  duk sukayi shiru  tare maida hankalinsu inda tanwer  ke  durkushe tana  kukan zuci .
Idanunsu na Kanta na tsawon  lokaci kafin uncle  Jamil ya dube uncle bashir  sannan ya cire kan mumy ya d’aura a jikin dady ya k’arasa inda take cikin hanzari yasa hannu ya fizgota  ba karamin tsoro  ya bata ba ta kwalla qara tana rike cikinta
tare da furta “wayyo Allah cikina “. wani  bakinciki  ya qara turnukesu bai san lokacin daya buge mata  baki ba yace “maza ki  rufe mana baki shasha banza shashar wofi Kawai ” .
da sauri tasa hannu ta dafe bakinta wanda take kyautata zaton hakoranta zasu iya ficewa su bar bakinta Idan bata dafe bakin ba  “jawota yayi kiiiiiii  bai direta akoina ba sai a gaban mumy  ta zube har tana  cin karo da gwiwar  mumy ya  zaro mata Ido kamar zasu fad’o waje mumy tace ” matsa kusa dani  dan  zan iya shake miki wuya ki mutu na huta”.
da sauri ta janye jikinta dan  wani irin tsoron mahaifiyarta ne ya shigeta, a hankali hawaye ke   ambaliya a fuskarta   sun fi minti  biyar  jugun jugun babu wanda ya sake  cewa  komai saboda  takaicinta.. “gbdy kina son ki rusa rayuwarki, ki lalata asalinki, me zakiyi da wannan ciki ?”bari kiji idan  ma kin  barshi babu abinda zai janyo miki  sai bakin fanti da cila rayuwarki cikin garari , sannan  babu mai  aurenki da dan shegen  ‘yanta’ada dan haka wannan cikin  dole  a zubardashi tana  jin haka ta sake fashewa  da wani sabo  kuka .
gbdy suka nemi natsuwarsu suka rasa ji suke Kamar zuciyarsu zata buga wallahi sun san da soja  yana  kasar  to da sai  ya balbalata yayi gudunwa gunduwa daita dan  ya tsani ganin   mumy  cikin damuwa bare kukanta  uncle Jamil jikinsa sai tsuma yake yana faman jan tsaki .”

A  natse  uncle bashir ya  mike  ya riko hannunn tanwer ya nufi  waje daita , ta gaban  abokan dady suka  wuce  dan suna zaune  har  lokacin a matukar firgice suka bisu da kallo “Kamar tanwer  nake gani Ko kuwa  idanuna ne?” inji cewar alhj Lawan Shuaib  “ba  idanunka bane  itace “a’a to yaushe  aka dawo daita da  bamu sani ba ?” wa zai baka wannan  amsar  tunda duk yanzu muka ganta .?alhj rufa’i ya fad’a yana kwabe baki.

Kai tsaye part din mumy   uncle  bashir ya  nufa  daita ya murda  handle din  kofar suka shiga ya zaunar daita abakin gado  shi kuma ya janyo  karamar stood ya  zauna  ya fuskance na  tsawon  lokaci sannan ya  fara magana jiki  a sanyaye “tan….!
Ta d’ago runannun idanunta  da suka kode tsabar kuka  ta zuba  masa  tana  jiran taji  mai zaice “mai yasa  baki  son a zubar  da cikin nan ? “tayi shiru tare da sunkuyar  da  kainta  kasa wasu  hawaye na sake gangaro  mata suna diga a tafukan hannunta.
” kiyi  hakuri my  daughter a zubar da  cikin nan  babu abinda  zakiyi dashi barinsa  bai  da wani  amfani  ,wannan cikin matsala  ne a rayuwarmu  gbdy”.
on-expecting yaji  sautin muryarta cikin dodon kunnensa  “yanzu   uncle bashir zaka  jagoranci  kisan kai ?” take zufa ya shiga tsatsafo masa hankalinsa  yayi mugun  mugun tashi”, wannan  cikin dole na haifesa  domin  yunkurin  zubar dashi yafi  samunsa  barna da  ta’addanci  da tarin zunubi  .
“Inna lillahi wa inna  ilaihi rajiun ya  dinga furtawa  had’e da mikewa  tsaye cikin tsananin tashin hankali   ya  shiga zagaye  d’akin  yana maimaitawa abinda ta fad’a  gumi na sake karyo masa duk da gudun ac dake aiki a  d’akin  amman hakan gumi ke tarara ajikinsa kamar ruwa kwakwaluwarsa ta hargitse
tana hautsinewa   cike  da buguwar   zuciya ya  tsaya  cak  a tsakiyar d’akin  yana kallonta  tare da nazarinta  a matsayinsa  na barrister take ya hango wasu abubuwa a tattare daita a hankali ya lumshe idanunshi tare da sanya hannunsa a daidai saitin zuciyarsa ya dafe dan wani irin bugawa take saboda abinda ya zowa zuciyarsa ,still idanunta basu daina zubar da hawaye ba cikin kasa da murya ya kira sunanta “tanwer !
Idanunta ta sake da d’agowa wadan da suke cike da ruwan hawaye ta kalli uncle bashir murmushin takaici ya sakar mata wanda yafi kuka ciwo.
“ba cikin kike so ba wanda yayi cikin so Ko idan na kintata daidai  ?”shiru tayi tana tunanin amsar da zata bayar kafin idanunta su sake Kawo wasu ruwan hawaye .
Ya numfasa ni kadai ne anan ki fad’a min gaskiya  zan fahimceki.   “wannan  gaskiya ne  uncle ina son shi sosai ,ina masa son da bazan iya zubar da gudan jinsa ba “. ware idanunshi yayi sosai akanta yana  cewa “are  you out of your sense   dan fashin kike so tanwer? shiru tayi tana nazari cikin zazzafa murya yace “why tanwer ?”me yasa zaki mana hk ?mai yasa zuciyarki zata kamu da sonshi ?”a Ina ma kika san zaki qara ganinsa ?”mutane da ba guri d’aya suke zama ba Ke yanzu kina tuninin zamu yarda dashi ne ?”
Da sauri ta rike masa hannu  tana cewa” dan Allah uncle ka taimakeni Adnan mutumin kirki ne qaddara ce take yawo a rayuwarsa, wallahi idan kagansa bazakace dan fashi bane,yana da kirki da kamala da tausayi ….”

“Tausayin banza da wofi yana tausayi ya kwana dake ?yayi maganar yana k’okarin cire  hannunsa cikin nata ta sake rikewa gam”wayyolhhly Allah ka taimakeni uncle ta fad’a jikinta na rawa Ina son shi wallahi zan iya mutuwa akanshi, zaku rasani akanshi, ni dai ina sonshi ..” da sauri ya runtse idanunshi kafin ya fizge hannunsa cikin nata, kuka take sosai tana rokonsa amman Ina a fusace ya juya ya bar d’akin zuciyarsa  na bugawa da karfin gaske  . “

A falo sukai cikibis dasu dady sun kamo mumy da sauri ya karasa  ya sa hannu suka nufi d’akin dady daita, nan fa hankalin mutane dake zaune  falon yayi kansu atare  suka mike tsaye suna kallon juna “Ku da alamun gidan nan  babu lafiya ,nima abinda na gani Kenan mu wuce Ko mu tsaya neman qarin bayani ?”gasky gara mu tsaya muji Ko meke faruwa suna cikin tautaunawa sai ga dady ya fito daman niyyarsa ya sallamesu kowa ya kama gabansa ,cike da damuwa suka matsoshi suna tambayarsa “fatan dai lafiya zainab take Ko jikin ne ?”eh jikin ne amman da sauki yanzu likinta nake shirin Kira “okay to Allah ya kara sauki inji cewar alhj rufa’i dady na gama magana ya nufi kofar fita dole tasa suka biyosa alhj hamisu yace”Ashe kuma tanwer ta dawo ?”eh! Kawai yace ya kara gaba   ya nufi inda motarsa take fake  ya shiga  ya zauna tare da kunnata kamar zai fita hakan yasa kowanensu  ya sha jinin jikinsa ya  nufi inda  motarsa take dan ga dukkanin alamun yana bukatar su bar masa gidansa dan haka  suka soma k’okarin  barin gidan zuciyarsu cike da sake sake Kala Kala .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button