KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

DARLING’S????????????????????????
KUSKUREN BAYA
     ????????????????
????????????????????????

    WRITING BY
BAGUDO& MIMI’S QUEEN
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

????️07

……Kusa daita ya ɗan duka  yana  kallonta ,a hankali yaji ta kamo yatsun  hannunsa cikin nata tana murzawa bai san sanda   ya  zauna a gefenta yana sauke numfashi tare  da tankwashe ƙafarsa  ɗaya yayinda d’ayar kafar ke kan tayis yana jijigawa , matso da kanta tayi ta d’aura  a saman  cinyarsa, idanunta a lumshe take jin yadda idanunshi ke yawo a fuskarta ,motsa hannunsa yayi da niyyar zarewa daga cikin nata saboda yanayinsa daya ji yana sauyawa, ta bud’e idanunta  tar akanshi Ido cikin ido suke kallon juna lumshe idanunshi yayi na second biyu sannan ya bud’esu akanta ya mik’e  dan baya son kusancinsu tare “me yasa baki jin magana ?”

  cikin sanyi murya tace ” me nayi maka ?” tana janyo hannusa ya rankwafo jikinta bakinsa ya sauka a daidai kunnenta hucin numfashinsa  yasa ta runtse idanunta da sauri.  “Ki tashi muje na maidake gidan ku” yayi mgnr yana sakin numfashi haɗe da ciza gefen kunnenta  ta saki qara mara sauti tana jin wani iri a gabad’aya ilahirin  jikinta .”No! bance maka bazan tafi gida  ba but atleast na…..
“Shiii!”. ya katseta ta hanyar d’aura yatsansa a kan lip’s d’inta,  shiru sukayi gbdy zuciyarsu na bugawa da karfi  “ka hanzarta maida yarinyar nan  tun bata zame maka kaska ba’. zuciyarsa ta faɗa masa haka, mik’ewa ya sake yi  yana kamo hannunta “Ke! tashi muje Karki bata min lokaci “. banza tayi masa tana  yatsina fuska “bana son Ki sake min mutsu  akan komai ” yayi maganar yana matse yatsun  hannunta cikin nashi yana ko’k’arin sauko dai ta, Cikin rashin sani ta fad’o jikinsa tare dan sakin  k’ara  “Ahm!”. Idannunta rufe, yadda ta runtse su yasa ya k’ura mata idanunsa masu matukar  kyan gaske, dan kanne d’aya idon tayi ta bud’e sai tayi saurin mayarwa  ta rufe hakan ya bashi murmushin da  bai shirya yiba me sauti jin haka yasa  tayi saurin bud’e idannunta akansa.

Murmushin  ya k’ara mishi kyau sosai kamar kar ya daina  , d’an k’ara ware idanunta tayi tana kallonsa wanda har lokacin fuskarsa na d’auke da murmushin. Ko’k’arin gyara tsayuwarta ya soma yi , Tanweer kuwa da sauri ta kai ma bakinsa cafka tamai peck a lips d’insa , ware idannunsa yayi sosai  yana kallonta cike da mamaki  ‘Do want to kill me wannan yarinya’. Ya furta a ransa Tan kuwa murmushi take masa, sake kai mai Cafka tayi a karo na biyu sai dai wannan karon taji ya bude ‘yan lip’s dinsa inda ya soma kokarin kissing d’inta,ya  cafko laulausan harshenta cikin nasa kamshi sweet taji mai kamshi lemun ,ware idannunta tayi ganin kallon da yake mata yasa tayi saurin runtse idanunta jikinta na dan rawa saboda wannan shine karo na farko a rayuwa  data yi  kokarin shan bakin wani nmj .

Tsura mata idanunshi yayi tare da d’an murmushi, yana jin yadda take jujjuya harshenta da sweet din dake  cikin bakinsa take zuciyarsa ta dasa masa  ayar tambaya akanta. ‘anya kuwa yarinyar nan  cikakkiyar buduwar ce ? anya kuwa ba watsatsiba ce take neman kawowa zuciyarsa farmaki? to idan itace kai meye ?Me ye marabinka daita? ” wata killa ma ta fika tunda bata aikata abinda kake …….
Kasa k’arasa zancen zucin nasa yayi saboda yadda take bin kunnensa da lallausan yatsunta tuni ya kasa jure abinda take masa a hankali ya cafko harshenta yana tsotsa a tare suka shanye sweet din sai ji sukayi sweet din ya kare aiko ta saka masa kukan shagwa’ba. “Wayo! Why?”
Tsura mata ido yayi yana kallonta tare da d’an janyewa, Tanweer banda tab’e baki ba abunda take tana kallonsa. “Ba…ka..kaine ka shanye sweet din byn bai isheni ba”. Tayi maganar a shagwab’e kamar zatai kuka. ‘bata face  yayi wannan karon ba alamun wasa  yanzu a fuskarsa. “okay tashi muje idan ma dubunsu kike so zan miki guzurinsa ta sauko tana gama saukowa ta rungumeshi a jikinta “i love you Mr.No Name!” I will miss you no name   tsintar kanshi yayi da kasa rabata da jikinsa “Just one day with you but ina jinka tamkar kar mu rabu, is it necessary sai mun rabu?”. bakinsa ya kai cikin kunneta yana busa mata  hucin  numfashinsa, lumshe ido tayi “ka barni zuwa gobe plz ban gaji da kasancewa tare da kai ba”ta furta cikin sanyin murya kamar zatai kuka, dan ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta. “ta kowani bangare mahaifinki ya baza mataken tsoro ya damu sosai da rashinki me yasa zaki so zama dani fiye da iyayenki why?”
yay  mata tambayar tare da ko’karin kaucewa.

“I know zasu damu sosai hatta I.B ma zai damu da rashina mutumin da muryata kadai idan bai ji ba a rana  babban tashin hankaline gareshi “
take qirjinsa ya buga zuciyarsa ta shiga rawa  shiru yayi yana ƙoƙarin ‘ban’bareta a jikinsa idan bai manta ba shine mutumin da suke waya daita a wancan ranar da tayi accindent “wannan kuma damuwarki ce yayi maganar cike da rashin damuwa , murmushin karfin hali tayi wanda yafi kuka ciwo “mutum mai dakakkiyar zuciya kamarka bai dace ya damu da lamuran mutane ba sai dai acikin kwayar idanunka kadai za’a iya hango tarin tausayi mutane bila’adadin”. “Ki daina wasa da zuciyarki da tunaninki  muje kawai”. Yayi yunkurin sake  bambareta a jikinsa ,sake   manne masa tayi tana gyara tsayuwarta a jikinsa gabansa na bugawa da matsanancin karfi yayi nasarar  zareta a jikinsa suna fuskantar juna ” ki daina bata mana lokaci saboda hakan babu abinda zai janyo sai tarin damuwa dan bazan taɓa sonki ba kuma ki daina sona dan soyayyata babu amfanin da zata miki , sannan daga yau ki sawa ranki  bazaki sake ganin ko mai kama dani ba, kiyi rayuwarki  tare da wanda kika fara zai fiyye miki , ni ba irin  mutumin da zaki yi rayuwa dashi bane”

gabanta ya dinga dokawa da karfin gaske jikinta ya kama rawa bakinta ya kasa furta komai a dalilin  maganarsa  dake  bugar mata da zuciya ,  riko tsintsiya hannuta yayi, yana gaba tana d’aga kafafunta da kyar tana kallon bayansa yayinda wani duhu mai haɗe da juya ya gilma cikin kwayar  idanunta daidai tsikiyar d’aki yaji jikinta ya sake tana kokarin yin baya ya juyo idanunsa ya sauka akanta gbdy yanayinta ya sauya ta dafe daidai goshinta da hannunta daya  cak ya tsaya a lokacin da take  kokarin zubewa kasa yayi saurin tarota jikinsa hankalinsa a matukar tashe gabadaya ya rungumeta , ita kuwa cike da bakinciki take fidda numfashi kusan minti biyar suna tsaye tana rungume ajikinsa tuni hawaye ya wanke  fuskarta, cike da tashin hankali take motsa lip’s dinta ” muje ka maidani gida kawai   thanks for all the helps tun daga ranar farko da muka hadu har zuwa yantoni daga hannun yan fashi”. magana take jikinta na rawa take yanayin jikinta ya sauya daga  dumin zuwa  zazzaɓi mai  zafi, cikin tsoron da bai san yana dashi ba ya matseta gam  ajikinsa yana fidda numfashi tare da lumshe idanunshi,  “ki dawo daidai sai na maidake” ni muje kawai ina son ganin  iyayena, i really want to see them”. ta k’arasa maganar tana shirin zubar da hawaye jin numfashinta na kokarin tsayawa ya fara  tafiya  daita cikin sanyin jiki ,ya kwantar daita a gefen gado a hankali  hannunsa daya dafe da byn  kanta, yayinda d’ayan hannun ke   tsarke cikin  nata  ya rankwafo jikinta  “ki natsu plz qirjinta na dokawa tace “dan Allah say you love me ka fad’a min  dan Allah koda itace zata zamo kalmar da zanje karshe daga bakinka ina son ji …
cike da matsanancin fargaba yace “dan Allah ki bar zancen nan babu wata soyayya a gabana, soyayyata ga kowace mace bata da  wani  amfanin ,bare ke karamar yarinya dake banason zunubin laifina ya shafe ki ,gara duk wani hukunci da zai zo min ya sameni ni kad’ai bazan ta’ba barin zunubina ya shafi kowa ba bare ke plz, dan Allah ki dawo daidai mu tafi dan hankalina bazai taɓa kwanciya  ba idan  na kai ki gidanku cikin wannan yanayin lumshe idanunta tayi numfashinta na tsarkewa heart beat d’inta na k’aruwa akai akai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button