KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

mutun biyu cikin yaran nabel suka rikesa ta karfin tsiya suka danne masa makoshi yana ihu ataimakesa amman ina cikin kankanin lokaci numfashinsa ya bar gangar jikinsa lokacin da nabel ya samu shigowa hadadden hall din dazaa gabatar da birthday dinsa dayawa mutane sun mike tsaye domin girmama da tayashi murna sai dai banda jaguwa anas yayi kokarin mikewa amman jaguwa ya dawo dashi a haka yazo ya wucesu yana dagawa mutane hannu wasu kuma yna mika musu hannu .”
ya zagayo ya sake dawowa inda jaguwa suke tare da babban yaronsa ya tsaya yana gabatar masa da jaguwa “boss wannan shine jaguwa ya mika masa hannu yana murmushi “jaguwa nice name “gaku yara daku wallahi amman kuna yin abubuwan da suka fi karfin shekarunku nabel ya matso da bakinsa daidai kunnen jaguwa “ka tsaya a iya matsayinka sannan ka nemi alhj tajudenni ka bashi hakurin wulakacin da kai da wannnan banzan abokin naka kukayi masa domin har idan kukayi Kuskuren kin bin umarnina ya dauke fauskarsa akan jaguwa zuwa ta Ana’s “ina tabbatar maka zan harbeka zan fasa kwakwaluwarka ina fatan kun fahimceni ni ba kamar commissioner bane yana gama fadar haka ya wucesu ran jaguwa ya baci matuka a zahiri ake iya hango tashin hankalinsa tunda yake bai taba samun wanda yayi gaba da gaba haka ya fada masa magana ba sai yau hasalima shi mutane suna shakkar fada masa magana.”

bai iya cigaba da zama agurin birthday din ba ya juya shima anas ya biyo bayansa suka shiga mota dukkanisnu agidan baya suka zauna eku ya tayar da mota sai dai babu wanda yayi magana acikinsu wanda hakan shi yafi daga hanakalin anas yaso yace wani abu akan nabel gdy yafishi shiga damuwa sai fesar da numfashi yake jikinsa na wani irin rawa “shiyasa nace bazan zo ba ka takuramin ga irinta nan “bashi da hanyar da zai iya ganawa damu bare ya samu damar fada mana mgn son ranshi sai ta wannan hanyar,” kaga a haka ma munfi karfinsa domin kuwa yaji tsoron zuwa inda muke inji cewar jaguwa.

“har ya isa yayi mana kashedi  da barazana “wai me yasa kake yin haka né Ana’s ?yanzu kan  d’an wannan abun zaka nemi ka daga hankalinka wallahi wannan karamin abu ne, ya fad’a adaidai  lokacin da suka karaso bakin get din gidan anas jaguwa ya bude kasancewar yana da remut din get din gidan a hannunsa suka shiga anas ya fito koina ajikinsa rawa yake jaguwa ya kamosa ya shigar dashi cikin babban falonsa “karka kuskura  ka sakawa zuciyarka tunani har matarka ta fahimci kana cikin damuwa “ko dai bakaji abinda ya fada mana  bane ?”

“naji  komai mana amman babu abinda zai iya “ina ban yarda ba wannan mutumin zai yi wani abu “byn shi sau daya kawai ya fada karka manta mutane nawa muka sha fadawa hakan kuma bamuyi komai akansu ba “mu muna da wankakkiyar zuciya né amman su fa ?xuciyarsu cike take da mugunta ni idan ma mutuwar ce gara ni na tafi, dan idan wani abu ya sameka gbdy babu wanda zai tsira dagamu har ahlinka “tô sai me ya gwada mana idan zai iya .”
anas ya girgiza kai dan shi bai taba jin wani abu zai faru dasu ba sai a wannann lokacin .”

jaguwa ya kira sunansa anas ka shiga ciki gurin matarka ka kwanta karka manta gidan gbdy a tsare yake da matakan tsaro tun daga get din gidan nan  har zuwa katangar gidan to me zai tsorata?
” Kai fa idan wani abu ya sameka yaya kake son muyi babu abinda zai sameni kaima babu abinda zai sameka kamr yadda kayi auren haka nima zanyi ,
kalleni kaga ,anas ya dago ya kallesa nan da wata biyu zanyi aure inshaallahu .”
“What ?
“Abinda kaji na fada haka ne ,Ai ansa bai san lokacin da murmushin farinciki ya subuce masa ba ya rungume sa ajikinsa yana shafa bayansa ” kai amman ka faranta min rai “saboda kai ne anas amman ban so nayi aure  a yanzu ba ya fada yana zaresa ajikinsa yana cewa “sai dai safe ya juya ya fita anas ya kulle koina ya nufi dakin matarsa .
Koda jaguwa ya isa gida ya kwanta a gadonsa flat yana tunani maganar nabel bai yi zurfi cikin tunaninsa ba tunanin da yafi kowani tunani tasiri ya kawo masa ziyara daga nan bai san sanda bacci barawo ya sacesa ba .


Washegari da yammaci ya isa asibitinta yayi parking ya kira layinta cikin kankanin lokaci ta fito sanye da doguwar riga zuciyarta cike da mamaki take takowa zuwa haraban hospital ta iske shi jikin motarsa tsaye fuskarsa a hade yayi mata alamar ta shiga mota tayi shiru tana kallonsa fuskarta dauke da alamr tambaya ,”shiga ina son magana dake “jiki a sanyaye  ta bude gaban mota ta shiga ta zauna zuciyarta na rawa dan bata san da me yazo mata ba allhairi ko akasin haka ya zagaya ya bud’e bangaren direba ya shiga ya zauna ya tada motar “ya naga kana kokarin tafiya dani ina zaka kai ni byn mgn kace zamuyi ?
Tayi mgnr a matukar tsorace .

“zanje na cinyeki ne bata sake yin mgn ba shima haka bai tsaya  akoina ba sai bakin maria beach byn yayi parking ya fito itama ta fito tana sauke numfashi dan sai yanzu hankalinta ya kwanata tana kallonsa ya jingina bayansa da mota itama tayi kamar yadda yayi bayan wasu mintuna ya juyo ya tsura mata idanunshi “Kinsan abinda yasa na kawoki nan gurin “?ban sani ba amman nasan ba dan saboda sumbata bane ,ke abinda ya fara zuwa zuciyarki kenan sumbata yayi taku daya biyu zuwa uku ya tsaya yana kallonta mace a rayuwarta sumbata , kywun jiki me kyau ,tsayu da kuma fadi qirji shi suke kira soyayya ,magana akan jiki tsayi ta wan bangare kenan gbdy a haka kake kallon qaunar da nake maka ?

Ya matso kusa daita sosai har suna iya jiyo bugun zuciyarsu da saukar numfashinsa “sam ba haka bane “to me kake nufi da lissafosu “?Ya rungume hannuwansa duka a faffadan qirjinsa yana kallonta itama cikin kwayar idanunsa take kallo “nasan zaki iya fadar abu bayan idona sannnan idan ina nan zaki iya fadar sa koma menene amman ni bazan taba canzawa ba naunayen ajiyar zuciya ta sauke taya akayi ka canza da sauri haka adnan ?”.

“nayi tsamanin kazo ka sake haukatani ne .”

“kiyi min shiru da wata magana shiru din tayi tana sauke numfashi.” a wannnan zamanin mata suna daukar maza a wani abu da zarar sun samu wani abu daga gurinsu sai suyi murna da zarar kuma yayi masu abinda suke bukata sai suyi farinciki ,tsuke bakinta tayi sannan ta motsa lip’s dinta sunayin haka ne ga wanda suke so ni ko galashinka na kalla farinciki nake sosai bare ka bani na gani shiru yayi yana cizan lip’s dinsa na kasa yayinda idanunshi na kanta” idan wanda kike só aka wayi gari kinyita kiransa bai shiga ba ko kuma bai samu ya daga ba ballantana ma ya kiraki me ye abinda zai faru ?

“Bani da matsala komai daidai a soyayya cike da tashin hankali yace “me kike so agurina tanwer?ta kalli yatsun hannunta sannan ta dago ta kallesa idanunta cike da hawaye “ina son na kare gabadaya rayuwata da kai adnan kasancewa ta tare da kai zai sani farinciki damun rayuwarka da abubuwa dayawa sa kaina akafadarka ba wai saboda kuka ba soyayyarka ce tasa na kasance a halin da nake ciki yau gbdy muryarta ta sauya alamun kuka hakan yasa ta tsaida maganarta ta sunkuyar da kanta a lokacin da hawayen dake makale da idanunta suka samu nasarar zubowa tasa dan yatsan hannunta ta dauke tana sanyawa jikinta jarumta sannan ta cigaba da magana .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button