KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Yaushe zaka tafi “?.

“May be yau ko gobe at anytime dai zan iya isa garesa idan shirina ya kammala “.

anas ya sake yin shiru tare da zuba masa rinannun idanunshi  ,can yace “nifa  ina tunanin kamar akwai masu bibiyarmu dan nayi mamakin yadda akayi dcp yasan da fitar scorpion”?”Eh nima nayi tunanin haka sai dai na kasa tsaida zuciyata akan kowa acikinmu kar nayi kuskuren da nayi a watannin baya wanda hakan yana cikin dalilin da yasa su jubi suke mana wani duba .”Haka ne kuma gara ma da baka ce musu komai ba amman ni kuma a tunanina sai ina ganin kamar aliyu ne .”shiru jaguwa yayi yana tauna lips dinsa da karfi yana nazarin maganar anas “zuciyata ta rigada ya yarda dashi anas bana tunanin aliyu nada saka hannu acikin abinda ya faru “.
“me yasa ma zakayi tunanin haka akansa ? sam sam bama zai ta’ba yi min haka ba ,yaron dana daukesa tamkar jinina na ‘yanta shi daga wahala zuwa dadi ,kai kasan irin abinda nayi facing kafin na samarwa aliyu aiki a ma’aikatar kudi ,to me yasa zakayi tunanin zai min haka ?.”

Anas yayi shiru yana cigaba da dubansa batare daya ce komai ba “Karka manta aliyu baya tare damu na tsawon lokaci sannan har ya bar gidan nan bai san sana’ar mu ba ,bugu da qari bashi da app dinmu da muke ganin komai da sautin muryar  juna a duk inda muke yayi maganar yana zagaye anas “.
“shi kansa anas tunani me zurfi yake sosai yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa kanshi ne ya kulle  har  yayi wannan tunani domin ya rasa wa zai zarga da munafuntarsu ,a hankali jaguwa ya kai hannunsa ya dafa kafadan anas tare da tsayawa cak yana dan jin tsoron faruwar abinda Ana’s din yayi tunani akai ,hakan fa zai iya faruwa ko  anas ? Yayiwa anas da kwakwaluwarsa tambaya”.

“A wannan zamanin mutane sun zama abun tsoro cin amana ne qarara ke zagayedamu bamu sani ba , babu abinda mutane bazasu iya zama ba ,ko su canza akowani lokaci , wadan da muka taimakawa a karshe  zasu iya zama silar fadawarmu halaka ,kai kasan wannan aikin da muke yi baya bukatar yarda da mutane ,lallai a nemoshi a tunhumesa yanayinsa kawai zai tabbatar mana da abinda muke bukata “lallai muna bukatar mu san ta yadda aka san  fitar sconpio  daga gidan nan da kuma inda zashi domin byn mu goma da muka tautauna babu wanda yasan da fitarsa kuma na tabbatar acikinmu babu wanda zai fitar da sirrinmu tunda ba yau muke tare ba dole sai mun yi bincike sosai akansa musan waye shi dan leke asiri ne ko kuwa shi din namu ne ?.

“Wannnan gsky ne na yarda da kai dari bisa dari Ana’s to yanzu me ya kamata muyi? Anas yayi shiru kawai yana sake zurfafa tunaninsa domin nemo mafuta.”ka fada min abinda ya kamata muyi mana kayi shiru kana kallona  ?” ban san me zamuyi ba wallahi kaina ya kulle  ,kayi tunani  adnan dan ka fini kaifin basera da hangen nesa akan komai kayi tunani me kyau abokina.”gyada kai jaguwa yayi sannnan ya cigaba da tafiya yana kallon yatsun kafafunsa yana zurfafa tunaninsa “da fari muna bukatar kwakwarar hujjar da zai tabbatar mana da aliyu ya shigo gidan nan acikin kwanakin ko bai shigo ba “,

“Eh mu samu wannnan hujjar  mu fara duba naurorin gidan nan tukun , duba nau’rori kawai  bazai bamu wannnan hujar da muke  nema ba saboda a wannnan falon mukayi tautaunarwa fitar sconpio kuma har muka gama babu wanda ya shigo duk wanda ma ya  fitar da maganar to yayi ne ta hanyar lebe ,amman bazan ki ta taka ba muje  mu duba tukun mu san next abinda zamuyi .”
Duk da hankalinsu a tashe yake amman a natse  suka jera  har dakin na musamman da na’urorin suke  .”jaguwa ya samu guri ya zauna ya daura kafarsa daya akan daya   tare da rike habarsa da hannu daya yana kallon anas dake kokarin  kunna  makaken tv  dake manne  da bangon dakin , nan take ya kunnu bangaren  dake daukar haraban gidan har inda mai gadi yake  zama  suka maida hankali kai .”

a hankali suke kallo duk abinda ke faruwa har suka kawo wani guri inda suka ga yana nuna musu dishi dishi alamun an rufe idon camerar kuma daga waje can kuma komai ya daidaita suka cigaba da ganin komai har zuwa fitar scorpion a jiya  da shigowar bakinsu na dazu da shigowar anas .”jaguwa ya mike tsam  ya hade hannunwansa guri daya yana tura lips dinsa na kasa cikin bakinsa cike da zafin rai ya soma magana “anan aka samu matsala “a wannan gurin aka samu matsala ya sake maimaitawa yana furzar da iska  mai zafi daga bakinsa,idan ma aliyu ne lallai suna da hadin baki da wannan tsohon dake mana gadi “.

A dan firgice anas ya dubesa zuciyarsa na rawa kafin daga baya ya soma magana cikin tsananin tashin hankali “gaskiya bana tuanin tsohon nan zai yi mana haka, za dai mu tambayesa amman mutamin nan  yana da kirki  bazai zama da hadin bakinsa ba,idan kuma har ya zamo da hadin bakinsa lallai wayo aliyu yayi masa dan wannan tsohon bana tunanin zai iya shirya wannan kimurmura kuma na tabbatar bazai boye mana komai ba tabbas idan aliyu ya shigo gidan  nan zai fada mana idan ma aliyu ya yaudaresa ne ya bashi wani abu dan ya ida nufinsa akanmu zai fad’a mana .”

jaguwa bai ce komai ba ya fito zuwa babban parlour’nsa ya karasa inda fridge yake ya bude ya dauki goran ruwan mai sanyi ya kafa a bakinsa dan  tashin hankalin da yake ciki yasa makoshinsa ya bushe ,har cikin zuciyarsa bai yarda aliyu zai masa haka , zuciyarsa tafi amince masa da me gadi ne
idan kuwa hakan ya tabbata zai bashi mamaki ,zai masa abinda mutane zasu tsaneshi sai daya shanye ruwan tas sannan yayi wurgi da goron ruwan yana sauke numfashi ,ya rike kugunsa da hannunsa daya ya fara tafiya babu shiri shima anas ya biyosa a baya ,yana cikin damuwa da tashin hankali amman idan ka kallesa bazaka fahimci  komai ba sakamakon dakiyar zuciyar da allah ya bashi .”

Kafafunsa basu tsaya akoina ba sai inda mai gadinsa yake zaune yana cin dafaffiyar kyada ya tsaya a gabansa kyam bayan ya zuba hannuwansa duka  cikin aljihun wandonsa tare da zuba masa rikitattun idanusnhi yana kallonsa,shi kansa mai gadi sai daya tsargu da irin kallon da jaguwa yake masa dan bai taba masa kallo irin haka ba har tsakiyar idanu,babu shiri ya ajiye ledar gyadar hannunsa yana cewa “yallabai barka da fitowa?jaguwa ya daidaita kansa yana sake boye tashin hankalinsa ya gyada masa kai kawai .” sai da anas yayi masa alamar yayi magana sannan ya bude bakinsa da kyar yace “baba ya aiki “?
“alhamdulillah mun godewa allah ina ta son ma na shigo nayi maka magana akan Jama’arka sun dade yau a kofar gida suna jiran fitowarka ,wasu sun gaji sun wuce wasu kuwa suna  nan  har yanzu sunki tafiya “.

Shiru jaguwa yayi daga maganar farko da yayi bai sake cewa komai illa idanu daya zuba masa ganin bashi da niyyar sake yin magana yasa ana’s ya shafa sumar kanshi shima yaso yayi masa magana dan lokacin da zai shigo ya mutane dayawa a kofar gida sai dai tashin hankalin da ya taho dashi ya mantar dashi .”Allah sarki bari yanzu idan ya koma ciki zai sa azo a sallamesu inji cewar Ana’s .shi dai jaguwa bai sake cewa  uffan ba sai idanu daya zuba ma mai gadi yana karantar yanayinsa gabadaya yanayinsa ya nuna masa rashin gsky Ana’s ya cigaba da magana “daman baba mun zo mu tambayeka wani abu ne ? allah yasa na sani yallabai yayi maganar  da sauri zuciyarsa na rawa “nace ko aliyu yazo gidan nan acikin kwanankin nan  da suka wuce ?shiru mai gadi yayi yana tunanin amsar da zai bashi   “baba
ana tambayarka kayi shiru .”eh yazo ko bai zo ba that’s all ?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button