KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

juyawa yayi  a matukar fusace ya bar d’akin zuwa dayan bangaresa ya shiga ziriya a falon yana kai kawo “zuciyarsa ta dinga raya masa ya amincewa aurenta ko dan ya musguna mata ya koya mata hankali yayinda wata zuciyar take ce masa ” kai da baka son aure yanzu karka sake ka yarda ka aureta ya bawa kanshi amsa “ina bazan aureta ba a daren yau din nan zan sa a maidaita gidansu, taje can ta k’arata” yana cikin wannan tunanin wayarsa ta soma ringing ya ciro wayar daga cikin aljihun wandonsa yana dubawa ganin sunan zahra na yawo a screen din wayar yasa shi jan dogon tsaki , yaki daukar kiran ya kashe tare da ajiye wayar akan mirrow dinsa ya shiga bathroom wanka yayi shap shap ya fito, ya sauya kawa zuwa manya kaya farin yadi vol mai matukar kyau da tsada ya karasa inda jerin takalmansa suke ya dauki takalmin mai yanayin cover shoe Wanda bayansa ke bude ya feshe ilahirin jikinsa da turaruka masu dadin kamshi da tsayawa arai ya fito yana taku kamar baya son taka kasa ya karasa inda motorsa ferary take Parke ya shiga ya bar gidan ..

A hankali yake tuki yana tunanin zantuttukan yarinyar har ya karaso unguwarsu yayi parking a kofar gidan daya ginawa mahaifiyarsa jamar dake zaune a unguwar suna ganin motarsa suka mike domin kawo gaisuwa ya fito a natse suka gaisa cike da natsuwa tare da kwanciyar hankali ya shiga gidansu a hankali kannenshi suka shiga farincikin ganinsa haniyarsu ce tasa hajiyarsa fitowa domin jin sautinsu suna kiran sunansa ta fito , ganinshi tayi tsaf kamar koda yaushe cikin natsuwa da kamala taji dadin ganinsa sai dai ta hade rai saboda kusan sati biyu kenan bata sanya shi a cikin kwayar idanunta ba, fuskarsa ta dauke da murmushin yace “Hajiya ina yini ? Cikin rashin walwala tace “um lafiya sai yau kaga damar zuwa ? “Kiyi hakuri duk cikin kwanankin nan ban zauna bane tunda na dawo sai faman zirga zirga muke yi akan wani aiki daya tasanyomu gaba dasu jabir “shine har ka ɗauki tsawon sati biyu duk yan’uwanka sun damu da rashin ganinka “nasan zaku ji babu dadi rashin zuwana sai dai ayi min hakuri saboda yanayin aikina ai muna waya da sadiq akai akai “ya fada min sai dai ai zuwan naka na da mahimmancin “koda yake ko babu yanayin aiki zaka iya dauke kafafunka saboda maganar aure da nake yawon maka “yayi murmushin yana Kallonta cike da matsanamcin soyayyarta yana matukar kaunarta ita da yan’uwansa numfasawa yayi sannsn yace” wallahi ba haka bane Hajiya shifa aure lokaci ne “,nafi ka sanin lokaci ne amman shi kanshi niyya yana da matukar tasiri idan kuma sai na mutu zakayi shikenna sai ka faɗa min na hakura “kiyi hakuri inshallah nan kusa zan kokarta “gara ka kokarta dan ga sadiq nan yana son yin aure amman yace dole sai ka fara yi ,dogon numfashin ya sauke sannan yace “shikenan zan san abun yi'”Allah yayi jagora nan suka shiga hira da zai tafi ya bawa kannenshi kudi yace su sayi duk abinda suke so bai yi musu tsaraba ba mahaifiyarsa ma kudi masu yawa ya bata hajiya tace “haba bazan amshi kudin nan ba yaushe kayi mana sako “ki amsa hajiya da bani da shi bazan muku ba “haka ne Allah ya kareka da kariyarsa ya albarkacin da zuri’a masu albarka “shine abinda nafi bukata daga gareki adduarki tana da matukar tasiri a rayuwata kuma ina gani cigaba ,a cigaba da yi min addu’a”Allah yayi maka albarka ya baka abinda kake so duniya da lahira ya kare min kai, yayi murmushin jin dadi sai bayan la’asar sannan yayi mata sallama ya fito inda jamar unguwar suka yi masa caaaa kudi ya raba musu sannan ya wuce

DARLING’S????????????????????????
KUSKUREN BAYA
     ????????????????
????????????????????????

    WRITING BY
BAGUDO& MIMI’S QUEEN
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

https://my.w.tt/lcJskJdtpbb

????️05

Cikin  natsuwa  yake murza kan     
Stearing   motarsa  zuciyarsa  cike fal  da  matsanancin  farinciki  baro mahaifiyarsa  da  kannensa  cikin farinciki  mai  tsanani  da  yayi, a nan duniya  bashi  da  burin daya wuce sanya  ahlinsa  cikin  farinciki , numfashi  ya  janyo  ya fesar  yana ɗan  dukan  kan stearing “zan dangwama  ina  baki  farincikin da kika rasa ammina  har sai kin gaji , inshallahu   zan  ɗauke  miki kewar komai ,zan mallaka miki duk wani dadi   dake  cikin duniyar nan   ke da yan’uwana  lafiyarku   farincikinku  jin  dadin rayuwa  zan yi kokari  ……
   Kiran  Anas  da ya shigo wayarsa ne ya  katse masa zancen zuci da yake ,  ya  sauke naunauyen  ajiyar zuciya sannan   ya  kai idanunshi  kan wayar a natse  ya kai hannunsa ɗaya ya  ɗauki  bluetooth  dinsa ya manna a kunnen ya dannan wayar  take muryar Anas ta doki dodon kunnenshi   “kana  Ina  munzo gida mai  gadi  yace baka nan ? Iskar ya furzar sannan yace  “naje ganin ammina  ne   gani   akan hanyar dawowa   ku  bani  minti  goma zan karaso  “okay  sai  ka karaso muna jiranka ..
Ya cire bluetooth din ya ajiye a mazauninsa  ya cigaba  da tuki yana sake lulawa  zance  zuci har zuciyarsa ta  shiga  hasko  masa yarinyar daya baro a gidansa  dogon tsaki yaja saboda  tuno kalmar ta gareshi kalmar da yaki jininta kuma take bashi haushi ….

Jaguwa  zaune  cikin d’akin daya tanada  domin  tautauna bayanai masu  mahimmanci  akan aikinsa  ,gabansa laptop dinshi ne ,yana faman operating  yana sauraron  bayanan  jubi  inda yake bayani akan alhaji tanko gote wanda ya kasance shararraren dan kasuwa wanda   duniya tasan da zamansa sannan ya tara tarin  dukiya bilaadadin  anan  gida nigeria da kasashen  ketari  ,ya mallaki qadarori da dama  da companies a kowace jaha dake ƙasar nigeria ” bincikenmu  ya nuna mana mutumin  baya zaman gidansa  da daddare sai da rana  bayan  haka  akwai  tsaro mai tsanani tun  daga bakin get  doping  estate  har  zuwa cikin gidansa ta kowani bangare  dakarunsa  zagaye suke  da gidan  bayan boyayyun  camerori dake lugu  da sako na gidansa, me zai hana  mu hakura da wannan taget din  muyi  facing din wani  yayi shiru hade da numfasawa  sannan ya cigaba da magana “jaguwa a ganina mu hakura da wannan aiki  kawai ko me kuka ce yan’uwa ?  ya  fadi haka yana kallon  sauran yan’uwansa dake zaune suna sauraronsa , duk suka gyara  “gaskiya mu hakura tun da tsaro yayi yawa  inji cewar kamil  ,Anas ya numfasa yace  ” kuna nufin bazamu yi nasara ba akan aikin da muka ɗauki tsawon lokaci muna jiran aiwatar dashi ? a qalla wannan shine karo na hudu da muke rusa budget din aiki akan Alhaji tanko gote  gaskiya a ganina bai kamata muyi wasa da damarmu ba kawai mu fara shirin aiwatar dashi kuma a cikin satin nan “dan Allah malam ka natsu kayi nazari akan operation din nan    jabir ya katse masa hanzari  ta hanyar fadar haka”the best solution mu hakura tunda jubi da kamil suka nuna abar shi , kai koni nayi supporting dinsu mu hakura kawai muyi facing din wani aiki ……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button