KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

a hankali ya dube abokan nasa “kamar ya kuka ga za’a sallami wancan mutumin dashi ? “a kamanta a bashi abinda ya dace inji cewar kamil “okay ka kasa abinda ke cikin wannan babbar jakar sai a bashi kashi biyu “an gama nan take kamil da Anas suka raba kudi , jaguwa ya mike tsaye hannunsa rike da cup Wanda ke dauke da ruwan coffer ya kurbi kaɗan “wannan jakar ku raba kudin ciki kashi biyar sauran kudin akai su inda aka saba kaiwa ya k’arasa maganar muryarsa a raunane “Jubi ya kira sunan Jibril da yake haka yake kiransa dashi ” ka biyoni da kason Alhaji tahir .

A tsanake yake d’aga kafafunsa Jibril na biye dashi a baya suka nufi bangaren da’aka wa Alhaji tahir masauki ,kofa biyu suka shige sannan ya sadashi da bangaren da alhaji tahir yake zaune jiran karasowarsa ya shigo makaken parlou’n da jikin bangon yake manne da tangamemen hoton mahaifansa da mahaifiyarsa sai wanda suka yi gaba-daya yan gidansu sunyi matukar kyau sosai ,Alhaji tahir na ganin jaguwa ya ɗan fad’ad’a fuskarsa da murmushi haɗe da dan mikewa yana mikawa jaguwa hannu shima Jaguwa ya mika masa hannu suka gaisa a mutunce sannan ya mikawa jubi hannun bayan sun gaisa jubi ya ajiye jakar daya shigo dashi a gefen Alhaji tahir sannan ya samu guri ya zauna tare da yin shiru, jaguwa ya kalli Alhaji tahir batare daya yi magana ba sai Alhaji tahir ne yayi magana yana murmushin “kasona kenan “ya karasa magana yana buɗe kajar da jubi ya ajiye ? ta’be baki jaguwa yayi tare da cewa “eh a takaice, dariya Alhaji tahir yayi yana jinjina kai cikin rawar murya yace “aiki yayi kyau sai dai naji labarin ance kun wuce da tanwer ? ” ya gyada masa kai kawai , “me yasa kuka d’aukota bayan bamuyi haka da kai ba duk da naji yaranka sunce marinka tayi ?kayi hakuri dan Allah kasan yara irinsu akwai tsaurin ido dan Allah ka taimaka ka maidaita “ko na baka ita ku wuce tare ne yanzu ?!”. yayi masa tambayar yana aika masa da kallon kasan ido saurin girgiza masa kai yayi “Wa?! ka rufa min asiri yanzu haka a matukar tsorace nake saboda jami’an tsaron dake kan aiki ni dai duk runtsi duk wuya karka ambaceni, Kuma kayi ko’k’arin maida Tanweer dan tana da importance sosai agurina, inada plans me kyau a kan yarinyar Alh.Tahir ya k’arasa maganar yana murmushi saboda tuna shirinsa akanta da dukiyar mahaifinta. “Bansan plans d’inka a kanta ba amma sai na kammala tawa buk’atar intakaice maka sai nayi ra’ayi zan maidata” Jaguwa yayi maganar cike da isa sannan a dake yana girgiza k’afarsa daya . Alh.Tahir ya had’iye wani wahalallen yawu sanin waye Jaguwa yasan bai isa yaja dashi ba. “To naji amma komai zaifaru a rufe sunana dan Allah”. Jin zancen Alh.Tahir yasa jaguwa murmushin gefen baki irin nasu na marasa mutunci da tsoro. “Hmm, dole kuwa inda alam yayi bolo ka shiga ciki dan informer yafi kowa laifi a cikin halkallar bare ma babu abinda zai faru kaje kawai Alhaji tahir”. bai dade ba ya wuce “kaga mutumin nan da shegen wayo inji cewar jubi “shi baya son a saka shi cikin matsala amman ya iya son kudi nifa ya bani mamaki ban ɗauka zai zo da wuri amsar kasonshi ba “manta dashi kawai ya d’auki wayarsa ya kira agbako cikin kankanin lokaci ya bayyana a gabansa ” kaje ka ɗauki kudi a ma’ajiyi ka siyowa yarinyar nan kayan ka hado da hijab da abinci ya amsa da “angama boss sannan ya juya da sauri , agbako bai fi minti talatin ba ya dawo hannunsa rike da fararen laidodi guda biyu ya ajiye a gefen Jaguwa sannan ya juya har ya fara tafiya ya dawo “boss mutanen daka saba rabawa tallafi duk safiya sun hallara fa , kai Jaguwa ya gyada masa yace “ka bada umarnin buɗe musu get agbako ya sake juyawa adaidai lokacin da Jaguwa ya mike daga zaunen da yake yana kallon jubi “muje na sallami mutane nan ,atare ya suka fito inda suka iske mutane unguwar har ma da makwaftan unguwar tsaye suna jiran fitowarsa tanwer dake zaune a dakin kamar an tsinkareta ta mike ta tsaye a bakin window ta kai hannunta ta ɗan zuge labule nan idanunta ya sauka akan jaguwa tsaye yana rabawa mutane kudi har sanda daya gama ya juya ya nufi wani ɓangare tana tsaye ,lumshe idanunta tayi sannan ta dawo ta zauna qirjinta na bugawa da matsanancin karfi “wannan mutumin na da tsananin kirki da tausayi , irin mijin da nake muradin mallaka ne a rayuwata , “ina ma zai soni ? tayiwa kanta tambayar tana kallon celling d’akin yayinda take zuciyarta ta bata amsa da” ai naki ….”yes is mine and me alone ta furta tana murmushi haɗe da gyara suman kanta ..

tana nan zaune tana tunani ya shigo d’akin hannunsa rike da white lailon’s guda biyu ya cilla mata daya a saman cinyarta ya d’ago a mutukar tsorace ta zuba masa ido gabanta na faduwa tana kallonsa ya karasa gaban mirrow ya ajiye laidar abinci ya juya har zai fita , sai Kuma ya tsaya batare daya juyo ba,” ki ci abinci ki canza kaya, i don’t want to see you like ….ya katse maganar da cewa “nan da mintuna talatin zan sa a maidake gidanku”. yana gama fadar haka yasa kai zai karasa ficewa daga dakin yaji sautin muryarta da duk sanda tayi magana yake kashe masa sansar jiki saboda zakinta da Kuma yadda sautin ke fita”No I am not leaving here, har sai ka faɗa min dalilin daya sa na dawo hannunka daga hannun yan fashi, and if you are the robber man daya d’aukoni daga gidan iyayena ina son sani?

wani irin juyowa yayi da sauri yana Kallonta, ta wani langwa’bar da kai cike da shagwaba tana turo masa ƙaramin bakinta yayinda kwayar idanunta ke kansa ,bai taɓa jin tsoro da firgicin wani yasan aikin da yake ba sai yau , bai gama fargaba da tunani ba ya sake jin sautin muryarta “Look! I have falling for you since the time I have set my eyes on you, naji ka kwanta min a rai, zuciyata ,tunanina da idanuna suna masifar kwad’ayin sake ganinka sai gashi cikin sauki Allah ya sake had’amu”. Kallonta yake tunda ta fara magana har ta k’arasa itama shi take kallo.

Murmushi tayi masa me d’an sauti. “Don’t worry a yanzu bana buk’atar sanin dalilin kasancewata
tare da kai a nan ta k’arasa maganar cikin sanyin muryarta mai kashe sansar jiki .

A hankali ta soma takowa jikinta na kadawa har ta karaso inda yake ta tsaya tana busa mai nunfashin bakinta ido cikin ido suke kallon juna “ko zan iya ce..cewa ka aureni?!”. tayi maganar cikin rawar murya?. “I want to always be with you, ina son ka aureni mu zauna inuwa daya da kai”. Ta sake matsoshi kamar zata shige jikinsa duk maganganun da take yana jinta sannan babu wanda ya d’aga masa hankali kamar kalmar ya aureta “dan Allah ka aureni ina son kasancewa tare da kai ,ni ni kaina bansan dalili ba amman ina bukatar kasancewa da kai”. Ta karasa maganar kamar zatayi kuka ta tallafo fuskarsa da duka hannuwanta “dan Allah ka fahimceni believe me zan kasance tare da kai a kowani hali dan Allah accept my love”.

Ya fixge hannunsa dake rike cikin nata yana mata wani irin kallo da yasa kayan cikinta kad’awa sannan muryarsa a kausashe yace “kina hauka ne?!”. yayi maganar a fusace jikinsa na rawa “ko kina shaye shaye ne daki zaki kawo min rainin hankali ? “Oh my goodness god! na d’aukowa kaina maseefa ya fadi hk a kasan ranshi “kaga nima fa ba wai sonka nake ba kawai dai akwai wasu …..”.
“Shut up!! I said shut up!!! or else I will get you lost in second are you insane ? How dare you utter such words to a man wanda ma baki sani ba!”. Ta bude baki zata sake magana “ki min shiru bana son jin sound dinki gaba daya,” me yasa ku mata baku da hankali da tunani?”ya karasa maganar yana huci, da sauri tad’an ja da baya “Kinsan menene aure kuwa da kike cewa na aureki ? Ina da tabbacin da kinsan ciwon kanki da baki fadi wannan maganar ba ,”yaushe kika sani?! yaushe kika fara ganina arayuwarki da har zuciyarki ta karanto miki hauka akaina ? me yasa kikayi tunanin aurena? kinsan ko ni waye da har kina matsayin mace zaki proposing dina akan Aure ,bama ni Namiji na furta ba sai ke, ina kunya? Ina mutumci?!”zuwa wannan lokacin a fusace yake wadan nan zantukan. Girgiza kanta tayi alamun a’a kamar zatai kuka ta bud’e ‘yan k’ananun lips d’inta tace “I don’t care nasan ko kai waye, what I know kawai ina son ka au….
Tasss tasa tasss taji saukan yatsunsa a kuncinta hagu da dama take wani juya ya ɗauketa  tayi baya luuuuuuuu zata fadi yayi saurin tarota da hannunwansa duka zuciyarsa na bugawa ita kuwa runtse idanunta tayi saboda rad’ad’in marin data sha ,
gabadaya ta sadakar da bazata sake jin maganar komai ba saboda dummmmm din da taji kunnuwanta sun yi, a hankali ta bude dara daran idanunta ta tsura masa kusan minti goma suna tsaye a haka suna kallon juna ganin zata bata masa lokaci ya tsaida ita bisa kafafunta ya finciketa ajikinsa ,nuna ta yayi da babban yatsansa yana mata gargadi da kwayar idanunshi yayinda zuciyarsu tayi mummunar bugawa a tare, kasa tsayuwa tayi akan kafafunta ta zube kasa dafe da kuncinta ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button