KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Kamar sauran mata nima ina son abubuwa dayawa ina son na cigaba da sonka adnan ,ina son a kowace rana na dinga kallon idanunka sannan a rana daya idan na rufe idanuwana na mutu a hannunka nayi mutuwa cikin salama shine abinda nake bukata ta karasa maganar tana dago idanunta dake tsiyayar ruwan hawaye,tsawon mintuna shabiyar suna tsaye babu wanda ya furta uffan hakan yasa ta sake maida kanta kasa sannan taji sautin muryarsa cikin wani irin yanayi mai gigitarwa “ina sonki surayya….”
Da wani irin sauri ta dago Kanta tana dubansa hawaye na turereniyar zubowa “ina sonki kuma akoda yaushe tun daga sanda na fara daura kwayar idanuna akanki alokacin da kika kusan bigeni amman karya nakewa zuciyata da kuma ke haka ne yasa banason na fada miki .”

Tunda ya soma magana jikinta da zuciyarta ke karkarwa at the same time tana sheshekan kuka maganarsa ta rikitata bata taba tsananin zataji wannan kalmar a bakinsa ba runtse idanunta tayi da mugun karfi tana ciza gefen lips dinta da karfi domin ta tabbarwa kanta gaske ne ko kuwa mafarki ne “zaki aureni surayya? “wani sabon gigita ya mamaye jikinta nan take jikinta ya kama rawa ya matso sosai kusa daita ya kai hannunsa ya dago habarta yana kallon cikin idanunta da suke arikice “ki bani amsa kina nan akan raayinki zaki auri gagarumin barawo kiyi rayuwa dashi “?Ajiyar zuciya ta sauke da karfi tare da cire hannunsa dake rike da habarta ta rungumeshi tsam tsam ajikinta tamkar zata rabashi gida biyu ya daura kanshi akanta yana jin soyayyarta me zafi kissing din kanta yayi sannan ya kai bakinsa kunnenta “ki aureni da sana’ata surayya .”
a hankali ta soma girgiza masa kanta tana kokarin zare jikinta tace “a’a bazan aureka da wannan sana’ar ba ta fad’a tana sheshekan kuka ta juya da sauri ta soma daga kafafunta…….”

Har dana Monday ????

????????????????????????
KUSKUREN BAYA
     ????????????????
????????????????????????

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

????️41

……a matukar kidime ya biyota yana kiran sunanta “tanwer ina zakije ki barni ki tsaya mu qarasa maganarmu mana ? sai dai ina bata tsaya ba ta cigaba da tafiya cikin sauri tana kuka mai tsanani tunda ya furta mata kalmar yana sonta taji kamar an yaye mata dukkanin damuwarta akanshi ne”
“oh my goodness wai me ye haka ne ki tsaya mana ya fad’a yana cigaba da binta a baya “nace ki dakata tanwer ki bani amsar tambayata “?ya qarasa maganar yana qara sauri cikin zafin nama ya shan gabanta ya rike tsintsiyar hannunta cikin nashi dayan hannunsa kuma ya riko kugunta dashi .”
tayi sauri kawar da fuskarta gefe tana sheshekan kuka ya juyo daita gbdy suna kallon juna , cikin tsananin tashin hankali yake kallon kyakkyawar fuskarta zuciyarsa na sake narkewa akanta ,wani irin sonta ne ke ratsa tsantsar jikinsa yana yawo acikin jininsa ,ya matsota sosai sunyi mugun daf da juna wanda da zai qara taku daya zai iya masauki a jikinta .”

ya kai hannunsa gefen fuskarta yana shafawa a hankali ahankali yana cigaba da kallonta “bai ta’ba d’aukar idan ya furta mata kalmar yana sonta zai aureta zata nuna damuwarta bare ma taki amincewa ba “ why tanwer ina zaki tafi ki barni alhalin baki bani amsar tambayar dana yi miki ? bata bashi amsa ba ta cigaba da sheshekan kuka “Why’re you crying tanwer?” please ki daina kukan nan haka yana touching heart dina ya zaro hanky a aljihunsa yana goge mata hawayen dake gangarowa akan kuncinta yana cewa “I don’t won’t see your tears just tell me zaki aureni ?ya sake tambayarta abinda ke d’aga mata hankali da dagula mata lissafi cike da raunin zuciya ta girgiza masa kai alamun “a’a!

“daman karya kike ma zuciyata tanwer?.“Me yasa kika min karya ?“ wannan karya haka tanwer?“kenan karya kika fada min cewar kina sona zaki aureni ?a she karya kika min na cewar baki son kowa a duniya sai ni a she bani kike so ba .”? Yayi mata tamabayr cikin wani irin salo da bata ta’ba ji daga bakinsa ba hucin numfashinsa na dukan wuyanta wanda ya haddasawa tsigar jikinta mikewa sannan bugun zuciyarta da tausayinsa ya qaru .”
kafin kace me wasu daga cikin mutanen dake gurin domin shakatawa suka zagaye su suna dubansu bai damu da mutane dake tsaye suna kallonsu ba ya had’e fuskarsu guri d’aya ta yadda zasu iya shakar numfashi juna ,anyi sa’ar faruwa hakan domin kuwa nan take suka dinga exchanging din numfashi junansu ta lumshe idanunta tana cewa “Kaga ka sakar min jiki mutane na kallon mu fa “.

“baza’a saka ba kuma har abada wannan jikin nawa ne dake Karan kanki ,dan baki isa ba ,baki isa ki barni ba tanwer dole ki kar’beni a yadda nake tunda da halina kika ganni kika nace ,kika koyar dani yadda zan bayyana son da nake miki ,”alhamdulillah gashi na furta miki ina sonki idan hakan bai miki bane ki fad’a min yadda zanyi .”?

muryarta cike da in inna tace “ni… ni fa ba wai bana sonka bane,ba kuma karya nake maka ba ,dan so ina sonka har yanzu adnan, burina ka zamo uban ya’yana amman bazan ta’ba auranka da wannan sana’ar ba, idan kana son muyi aure lallai adnan ka rabu da wannan aiki , sannan ka tuba zuwa ga allah abinda kasamu acikin sana’ar ka kyautar dashi gabadaya sannan Kazo muyi maganar aure .”
Kamar mai rad’a yace “kinga nayi miki kama da irin nmjn da za’a bawa umarni yabi ? tanwer ni ba irin wad’an nan mazan da mace ke iya juyawa bane ,ki tsaya a yadda nake so shine zaman lafiyarmu da kwanciyar hankalinmu , ina sonki kuma zan aureki haka zalika ina son aikina kuma bazan iya rabuwa dashi ba ,kema kuma dole ki amince da abinda nazo dashi sannan ki so aikina “.yana gama fad’ar haka ya soma tafiya daita da kallo tabi bayansa tana d’aga kafafunta da kyar har suka qaraso inda motarsa yake idanunt dana mutane na kansu sosai suka burge mutane duk da basu san akan me suke jayayya ba .”

ya bud’e mata murfin bangaren da zata zauna jiki a sanyaye ta shiga ta zauna tana sauke naunayen ajiyar zuciya,ya maida murfin kofar motar ya rufe ya zagaya ya shiga bangaren direba ya zauna ya bawa motar wuta har suka hau babban titin jakonde babu wanda yayiwa dan’uwansa magana ya cire hannunsa daya akan stearing ya daura akan hannunta dake kife akan cinyarta batare daya kalli inda take zaune ba .”waigowa tayi ta tsura masa ido yana murza stearing da hannu d’aya yayinda dayan hannun ke fama shafa hannunt sanye ac na ratsa jikinsu da zuciyoyinsu .”halayensa bazai sa taki morewa kallonsa ba dan kallonsa ba karamin jefata cikin nishadi yake ba, tafiyar mintuna talatin ta kawosu asibitinta yayi parking batare daya kashe motar ba yana jiran da zarar ta fita yaja motarsa yayi gaba ,
ita kuwa zuciyarta da jikinta rawa suke tana jin tsoron ya juya mata baya ,a hankali ta dinga jin kamar ta amince masa kawai suyi aurensu a haka “a’a surayya karki soma wannan ganganci dama ce ta sameki ,kiyi iyakar kokarinki ya canza karki sake ki biyewa son zuciyarki ki auri dan fashi da makami “
wannan karfin gwiwar da wankakkiyar zuciyarta ta bata yasa taji zata iya komai ciki kuwa har da juya masa baya ta cigaba da rayuwarta babu shi murmushin jin dadi ya bayyana akan fuskarsa
ganin bata fita da sauri ba kamr yadda yayi tsammani suna gama qarasowa zata fice ta barshi dan haka tunaninsa ya bashi hakuri zata bashi .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button