KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48


Wahegari tun da asuban fari fari nazifi yayi wa gidan alhj Tahir diran makiya Koda ya karaso ib na bacci hakan kuwa yayi masa daidai dan zai samu aiwatar da shirinsa, domin a Shirin da yake son yayi domin fitar dashi Ibrahim baya son kowa yasani daga shi sai mahaifiyarsa dan haka ya Kara masa da allurar bacci wanda zai d’auki lokaci yana aiki ajikinsa sannan ya d’ago ya Kalli hjy baseera “kin tabbatar kin sakawa dady maganin cikin abincinsa jiya ?”eh baccinsa ma yayi nauyi sosai dan ko d’aga yatsunsa baya iyawa ,”very good yanzu zan nade ib cikin kayan wanki domin wannan hanyar ce kad’ai zata mana saukin fitar dashi “duk yadda kayi daidai ne nazifi bani da ta cewa tana kallo ya d’aure ka’fafun ib ya curesa guri d’aya sannan ya nadesa yanzu abinda za’a yi ki kira masu aikin gidan su taimaka min na fita dashi. “
shiru umma tayi na second biyu kafin daga baya ta yi mgn “ince kace dani za’a yi tafiyar ?yace “eh dake zaa yi mana “kaga kenan nice yakamata na fidar dashi da hannuna idan ya kasance kana ciki zai zamo da matsala tunda nasan idan ya nememu ya rasa dole zai yi bincike sosai akai “.
“haka ne Kuma kin kawo shawara bari na fita sai mu had’u a airport “to shikenan na gode sosai .
nazifi ya bar gidan yayinda hjy baseera ta kira masu aikinta da taimakonsu ta fitar da gangar jikin Ib zuwa haraban gidan suka Saka a bayan motar hjy basera su kansu sunji nauyi matuka sai dai babu halin tambaya suka juya zuwa cikin gidan suna haki .
Hjy basera ta dawo ta Bawa kowacce aikin yi sannan ta shiga d’akinta bayan kmr minti goma ta fito lokacin duk suna kitchen tana k’okarin shiga mota direbanta ya taso da sauri ta dakatar dashi yayi mamaki matuka ya dai koma ya zauna a mazauninsa da kanta ta tuka motar bata tsaya akoina ba sai airport Inda suka hadu da nazifi cikin kankanin lokaci akayi komai aka gama jirginsu ya tashi ….”

D’aure jaguwa yake da dan karamin towel a kungunsa yayinda hannunsa ke rike da Daya yana tsane jikinsa a gaban mirror Wanda da gani wanka ya fito anas ne ya turo kofar d’akin ya shigo “yanzu wanka ne sama da awa biyu jaguwa “?
“ya son ranka bafa na son damuwa “? to Dan Allah kayi sauri tun dazu bakin can ke zaman jiranka aiki suka zo dashi mai nauyi “idan sun matsu su wuce idan Kuma zasu iya jira su jira. ya fad’a yana daukar body lotion ya fara shafawa ajikinsa “ai bazasuyi fushi ba suna can suna jira ka daiyi hakuri ka takaita kawai anas na tsaye har ya gama shirya Kansa ya fito zuwa inda bakinsa suke zaune zaman jiransa ya samu guri ya zauna anas ya juya cikin sauri ya fad’awa su jubi jaguwa ya fito babu yadda suka iya haka suka fito suna cika suna batsewa dan har lokacin basu daina Jin haushin abinda jaguwa yayi musu ba , shi Kuwa ko ajikinsa yayi watse dasu yaki bi ta kansu kowannensu ya samu guri ya zauna sannan bakin suka fara magana akan abinda ya kawosu har sanda suka dasa Aya “Kuna nufin Aysha oil and gas ?”sosai Mai gidan man yayanamu ne uwa daya Uba sai dai sam bama amfana da dukiyarsa daga shi sai matarsa da yayansa suke ci Kuma hasali wannan dan’uwana ne silar arzikina nasa “dakata ban tamabyeka duk wannan ba aiki dai kuke bukata Kuma za’a yi dae yarda Allah “to to shikenan Amman dan Allah kuyi yadda asiri bazai tono ba “shiiiiiii ku tashi ku kama gabanku .
jikinsu na rawa suka mike suka bar gidan daga nan su jaguwa suka cigaba da tautaunawa tare da tsara yadda komai zai tafi daidai wanda aranar suka shirya dasu jubi ,a ranar basu kwana a gidan ba a gidansa na oluwale suka kwana gbdy har da yaran aikinsa .
Wadhegari a hankali jaguwa yake saukowa akan matattakalar bene jikinsa sanye da bakaken kaya wondo da riga bayan rigar an rubuta jaguwa hannunwansa duka cikin aljihun wandonsa tun kafin ya k’araso kunnensa ke jiyo masa tautaunawar yaransa
“Ina da tabbacin har da tsananin tsoron allahnsa da kyautatawa mutane yasa muke samun nasara akoda yaushe “wannan haka ne duk da abinda muke yi ya sa’bawa shari’a Amman hanyar da kudaden suke bi na alkhairi ne “sosai kuwa ” inji cewar anas.
“you all know there’s no time when we can’t do what we want suka fara sakar masa murmushi gbdy yaransa suka mike suna Sara masa ban da abokansa “safe da dare babu lokacin da bazamuyi abinda muke so ba kawai abu mafi mahimmam ku karkafa zuciyoyonku akan komai ,ko da yake ku din gwanaye mutane ne da sukayi gasar mutuwa meye bazasu iya ba ?”
gbdy suka gyada masa Kai suna murmushin Jin dadi “wannan haka yake Kuma babu gudun babu ja da baya Kuma duk abinda ka shirya dole ya tabbata tunda kana da maganin kwalaye ” akwai mutane dayawa da suke son su zama fadera kamar ka Amman abun ya faskara sai dai sun tsaya a matsayin local government domin Kai kadai ne kawai zaka zama fadera ka zama state a karshe Kuma ka zama ceo the only armed robber’s international plc you’re the most supreme leader of us all “.
jaguwa duk runtse duk wuya Muna tare da Kai muna jinjina maka Kai kadai ne acikin garin Nan daka gagari kowa we hail you jaguwa inji cewar jabir ya fad’a yana Kai ta’ba wi bakinsa ” muna sonka kmr yadda anas ke qaunarka dan Allah ka daina zarginmu da cin amanarka da hannu ya dakatar dasu gbdy yana gyada musu Kai .

A hankali ya fara tafiya a tsakiyarsu Yana dubansu daya bayan d’aya kafin daga bisani ya fara motsa labbansa a hankali ” my name is Adnan amad jaguwa and iam of different body dimensions duk Wanda yace bazamu muyi bacci ba shine bazai ba, Wanda ya barmu da lafiyarmu shima zai zauna lafiya Wanda yace zai damemu to muma zamu damesa am jaguwa and iam ceasar as well so give unto jaguwa what’s belong to him Yana gama fad’ar haka ya d’auki bindigar pesto su kuma sauran suka d’auki AK 47 ya nufi haraban gidan suka biyo bayansa suka shiga mota suka bar gidan zuwa Aysha oil and gas dake cikin apapa.”

Da misalin karfe Tara na safiyar ranar tanweer ta matsa lallai sai an sallameta tunda babu Inda ke mata ciwo akan hanyarsu ta koma gida ne “dad !
ta kira sunansa “yes my tan ya amsa yana dubanta “dady banason ka sheidawa kowa na dawo gida ka bar mutane a yadda suke dakon jiran dawowata “ko me yasa kika fadi haka ?”ina da dalili amman idan lokaci yayi da kanka zaka fahimci haka “har jaminan tsaro dake kokari binciko Inda kike kar a sheida musu “? “Eh !
“to shikenan anything for my baby bani da ja duk abinda kike so nima Ina sonshi ya k’arasa fad’ar haka yana cigaba da kallonta “kema mumy please “naji ..”
suna karasowa gida minister ya gargadi dolapo da kar ya sheidawa kowa dan shi kad’ai yasan da dawowarta yace yaji .
Kai tsaye had’add’en d’akin ta shiga komai very Niet kamar tana gida sai kamshi air freshener yake a hankali ta soma neman karamar wayarta Aiko batasha wata wahala ba ta gani, ta sauke naunayen ajiyar sannan ta kunna , gani taki kawo wuta ta fahimci babu caji ne dan haka ta jonata a caji ta nufa bayi domin tayi wanka .
tunda ta shiga bayin taji kanta ya fara Sara mata sakamakon kanshi sabulunta fair and white daya gauraye bayi ba tsamani taji zuciyarta ta tsani Kamshi .
ba zato kawai ta fara amai ta kwarara amai Mai isarta wai ma Dan cikinta babu abincin kirki tana gamawa ta shiga bathtube ta kunna shawa ruwa na shiga jikinta batare data cire kayan jikinta sai da ta samu natsuwa sannan ta mike ta janyo towel ta d’aura ta banko kofar ta fito ta dawo daki ta bar bayin kaca kaca da amai ta fad’a saman gadonta tana fad’in “wash !wayyo Allah meye haka kuma…..?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button