KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

a hankali ya mike tsaye ya shiga bathroom ya rage kayan jikinsa ya saura daga shi sai boxes yayi kasa da idanunsa zuwa jikinsa jin damshi da kuma harbawar da jijiyarsa Ke yi , bakinsa ya tsuke tare da cewa “abun har ya kai haka Kenan “? kai ma fa kana son yarinyar nan dan me zaka dinga tauye kanka”? zuciyarsa ta fad’a masa haka kai! kai!! ba so bane sabo ne babu wani so.
da tunaninta yayi wanka ya fito ya shirya cikin wasu kanana Kaya yayi salolin da bai yi ba ya fito a parlour Kasa ya iske su anas dasu jubi suna shaye shaye cikin tsuke fuska yace “anas me yasa ka barni inata bacci baka tashemi ba “?
“sau nawa zan tasheka ?” shigowata biyar ina tashinka kaki tashi sai makale pillow kake ,sanin da nayi agajiye kake shiyasa na barka ,ai ban d’auka zaka tashi yanzu ba a yadda nazo naga baccin da kake har mafarkin tanwer kayi fa .
“Banson maganar banza ya fada yana jan tsaki gbdy suka kwashe masa da dariya “Allah karka ji da wasa ka wani makale pillow da alamun kana jin Kamar ita..”
“Ya Isa abar magana kawai banaso dan kai duk abinda kasan zai batawa mutun rai shi kake yi ya k’arasa maganar yana d’aukar remut ya canza channel zuwa tashar labari “ga abinda ya kamata Ku dinga Kallo nan kusan halin da kasa da gari yake ciki amman sai Ku zauna kuna shaye shayen banza da wofi .”

Anas ya tashi ya dawo kusa dashi”kasan Allah da gaske nake kayi mafarkin yarinyar nan da katashi bakaga jikinka ya sauya ba “?ya karasa maganar yana dubansa ,da sauri shima jaguwa ya waigo suka had’a Ido anas ya kashe masa Ido d’aya yana masa murmushin mugunta , “tabbas jikinsa ya sauya har yanzu yana jin haka “kada ka damu da dogon tunani yanzu dai ka tashi kaje kayi wanka tsarki.
” har fa nayi sallolina” kada ka damu zaka iya zuwa ka sake yi tunda na fad’a maka “kai Allah sai na kasheka da hanuna na huta da matsalarka yayi mgnr yana had’e hannuwansa duka “Ai kuwa da sai kafi Kowa kuka da shiga damuwa idan ka kasheni , tsaki jaguwa yaja yana mikewa tsaye “ba yanzu zaka mutu ba karka sake min batun mutuwa banaso “mutuwa ai tazama dole adnan , a wannan alqaltamu ai tare muke yawo da mutuwa sai dai zan mana fatan mu dainata kafin mutuwarmu Kaine kwarin gwiwarmu Adnan idan ka ajiye makaminka dole muma muajiye Ko ba haka ba friend ?”ya juya ya fuskanci su Kamil basu ce uffan ba illa haushinsa da sukaji ganinsu ya fiyye zakewa .
jaguwa bai sake cewa komai ba ya cigaba da tafiya bai san wanne zaiyi ba aciki idan ya ajiye sana’asa bai tsira ba , idan ya cigaba shima yasan ba tsira yayi ba a hannun hukuma dole sai ya shiga hannu .”
cikin kankani lokaci idanunshi suka kada suka rikide sukayi ja anas ya biyosa atare suka shiga d’akin yanata masa magana amman jaguwa yaki cewa komai ya shige bathroom ya barsa tsaye .”Ranar sam tanwer bata runtsa ba, haka tayita juyi daga farkon gado zuwa karshensa, datasani dawowarta hannun iyayenta kuwa tayishi yafi sau babu adadi shi kanshi jaguwa bai iya runtsawa ba, kwantawa yayi rigingine ya d’aga kansa sama yana tunanin yadda rayuwarsa ta faro ,idan ya tuna Shi din maraya ne bashi da kowa shi da kannesa sai Allah da mahaifiyarsu sai yaga bai kyautawa kanshi ba daya zabin sanar fashi da makami .
gbdy ji yayi komai ya kwance masa Allah yayi masa baiwar da bakowa yake daita ba tunda aka tsamoshi acikin mutane bilaadadin aka ingata rayuwarsa da ilimi addini dana boko aka bashi karfin da zai iya kowacce irin sana’a amman karshe ya bige da daukar bindiga .
sai yaji duk ya cuci kansa da yanuwansa da mahaifiyarsa, ko yaya zataji duk ranar da dubansa ya cika ..”?
Mahaifiyarsa ta cike dukkanin gurbin uwa da uba da dangi agurinsa sannan ga dan’uwansa da amininsa anas yasan Ko yau yace ya daina wannan sana’ar zai goyi bayansa tunda yana son duk wani abinda yake so, Allah ne ya hadusu da anas amman yana jinsa Kamar sadiq dinsa, yadda zai Iya bawa Sadiq rayuwarsa haka zai iya bawa Anas .”

washegari a kasalance yayi komai daga karshe ma a kwance ya yini Ko ya Samu zuciya da gangar jikinsa su samu natsuwa da suka rasa, yana kwance yaji shigowar sako wayarsa ya mirgina ya lalubo wayar yana dubawa ga abinda ya gani wanda sai da gabansa yayi wani irin mugun tsalle sannan ya fadi .

mai yasa kaki d’aukar kirana ?” kasan zaka barni kayita wasa da nonuwana ?”mai yasa ka amshi budurcina alokacin da bana cikin haiyacina kayi yadda kaga dama dani ? ka kirani dan allah zuciyata tana rawa sannan cike take da tsoron abinda zai biyo baya Sai dai ban yi tunanin zaka min hk ba bazan iya rayuwa babu kai ba kamar yadda nasan kai ma bazaka iya rayuwa babu ni ba

“Oh my goodness god tanwer kina da damuwa, kina damun rayuwata nifa zan iya rayuwa babu Ke Kuma babu abinda zai dameni ya fad’a a fusace yana jan tsaki ,a hankali ya kwanta ya janyo pillow ya Kankame ajikinsa yana sake karanta sakonta yana jin zafi aranshi bayan kamar minti goma sha’awarta ta dinga taso masa tsaki yayita ja yana k’okarin kawar da tunaninta .

da yamma lis ya fito ya wuce su anas zaune suna kallo da sauri anas ya tashi ya biyo bayansa har ya kai bakin gate zai fita ya tsaida shi da dan gudunsa “lafiyarka kuwa Adnan “?anas ya fada yana fuskantan sa sosai ,sai ma yaga Kamar idanunsa sunyi ja “babu komai anas amman kaina , zuciyata , kai komai na jikina Kamar ba nawa ba ,ya k’arasa maganar Kamar zaiyi kuka “Kwantar da hankalinka duk fa ba komai bane Allah idan ma akwai abinda ke damunka har da rashin yarinyar nan atare da kai, ka d’aure ko sau daya ne kabawa zuciyarka abinda take so. “girgiza masa kai yayi alamun bazai iya ba ” ka barni da maganarta anas ina da Kanne mata yaya kake tunanin zanji idan daya daga cikinsu ta kamu da soyayyar dan fashi “?
Sannan kana tunanin iyayenta zasu yarda su dauketa su bani”?
“Karka damu wannan ai al’amari ne na soyayya idan ta tsaya tsayin daka sai kai dole zasu baka aurenta .
“Shikenan tunda ka nace akan lallai ina son yarinyar nan zan bawa zuciyata dama mugani Ko zan fahimci hakan ,zanje gurin ammina bazan Jima ba zan dawo ka tsaya Ku kasa komai yadda ya kamata sai na dawo .”shikenan ka gaisheta dan Allah “zataji ya fada tare da juyawa ya cigaba da tafiya Kamar bai son taka Kasa har ya karaso wajen gidan .

a hankali yake taku zuciyarsa na hasko masa fuskar tanwer da tunanin sakonta yana jin Wani iri abu wanda bai san ko menene ba sai dai yasan ba normal yake jin jikinsa ba .
ya karasa bakin titi ya tari mai mashin zuwa unguwarsu adaidai kofar gidansu aka saukesa ya sauka ya Ciro duba daya ya mikawa mai machine ya juya ya soma tafiya,mai mashin ya Karba yana cewa “yallabai ga canjinka da hannu yayi masa alamar ya barshi batare daya juyo ba . “
Kamar koda yaushe jama’ar unguwar na ganinsa suka hau rigerigen Kawo gaisuwa , sai dai sunyi mamakin ganinsa babu mota yau, a hankali yake binsu daya byn daya yana mika musu hannu tare da mika musu kudi a karshe ya Shiga gidansu a falo ya Tarar da ammin tare da hasera da kannesa shafiq ta gaishesa tare da d’aukar dadduma ta shimfid’a masa ya amsa mata had’e da zama yana gaishe da ammin ta amsa cikin sakin fuska tana cewa “Sannu da zuwa, yayinda hasera ta gaishesa “Ina yini ya Adnan ?yajita sarai amman yayi Kamar badashi take ba, Sai da ammi tace “ana gaisheka fa sannan yace “lfy! atakaice shafiq ta shiga kitchen ta d’auko masa abinci wanda Kaida ne kullum sai an zuba an ajiye Idan yaxo yaci idan bai zo ba abayar, ammi tace wa maza ki Tashi ki amsa abincin Shafiq ta mikawa hasera abinci hasera ta amsa ta ajiye a gabansa tana sake masa sannu da zuwa sannan ta mike cikin rawar jiki ta d’auko masa ruwa ta Kawo masa bayan ta zuba masa abinci ta tashi ta kama gabanta .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button