KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Hajiya basera na zaune a falo tana kallo labarai cikin haka aka soma watso sabin labarai ciki kuwa har dana su jaguwa kamar almara taga hoton mijinta yana zayyono magana tiryan tiryan nan take ta shiga gagarumin tashin hankali mara misaltuwa jikinta na rawa ta mike tsaye zata nufi bangaren ib dake ranar ta kasance lahadi ce yana gida turus tayi sakamakon ganinsa tsaye a bakin kofar shigowa ya harde hannunwansa duka a qirjinsa yana dubanta hannunta dake rawa ta kai tana nuna masa tv “da…..dadyn..” sai kuma ta kasa magana ta cigaba da nuna masa tv.
Ya sauke hannunwansa yana sauke naunayen ajiyar zuciya sannan yayi taku uku ya qaraso inda take tsaye ya kamota ya zaunar daita akan kujerar data tashi shi kuma ya zauna akan center table yana dubanta a tsanake kamar ya zubar da kwalla “nasan komai daya faru umma murna da farinciki ya kamata kiyi zaki rabu da maseefa data dade tana damunki .”girgiza masa kai ta shiga yi tana cewa “mahaifinka ne fa Ibrahim duk lalacewarsa bai kamata ka kirasa da maseefa ba, idan ni na kirasa da hakan kai bai kamata ba .”

“Ya kamata Ummu wannan maseefar tasa naji na tsani kaina tasa naji dama ni din shege ne ,da samun gurbataccen mahaifi kamarsa wallahi gara babu ,
wallahi umma ina tsananin jin kunya cewar shi din mahaifina ne yay shiru yana furzar da iska me zafi daga bakinsa .”
A qalla ya dauki tsawon minti biyu sannan ya numfasa ya cigaba da magana cikin sanyayyar murya “duk tarin qaunar da nakewa tanwer na kasa sake zuwa ganinta ina tsananin jin kunyar abinda dady ya aikata mata ,ina jin kunyar abokan aikina in fact na tsanani kaina “.
Umma na zubar da hawaye tace “hakuri zakayi Ibrhim hannunka baya rubewa ka yanke ka yar dole dai shi din uba ne agareka ni kuma miji ne agareni bai kamata mu barshi cikin wannan halin ba ,zamu daukar masa lauya “what ?”

Ya furta cikin tsananin fushi “lau me Umma ?”
“Lauya Ibrhim yanayinsa da komai ya nuna mahaifinka yana cikin danasani abinda ya aikata ya mike tsaye jikinsa na kyarma tare sa soke hannuwansa duka cikin aljihun wandansa yana cewa”bazaki daukar masa lauya ba haka zalika nima bazan daukar masa lauya ba abarshi ya girbi abinda ya shuka .”
“Haba Ibrahim kar….”
“Wallahi Umma gara na daukarwa jaguwa lauya dana daukarwa dady lauya ya katseta ta hanyar fadar haka yana dubanta ido cikin ido yana gama kallonta bai sake cewa uffan ba ya juya fuuuuu cikin fushi ya fita daga falon bayansa tabi da kallo hankalinta na qara tashi tasan halinsa yana da matukar hakuri amman kuma bai iya fushi ba .”

Bangaren hally ma ta shiga damuwa sosai tana son tasan halin da mijinta da yayanta suke ciki amman babu ta inda zata sani dan haka kullum cikin kuka da tunani take lokaci daya ta zabge ta rame tayi duhu ta fita haiyacinta ,itama ammi ma ta shiga damuwa me tsanani kuma ta yarda ta amince wani mummunar abu ya faru da danta da surukinta a duk inda suke ,”
Tunda wannan bala’i ya faru da jaguwa ammi bata nemi kowa ba sai yau ta kira sadiq ta fada masa komai ,nima ammi naji akwai damuwa ajikina domin tun last week nake kiran layinsa baya shiga haka ma number anas baya shiga amman karki damu ammi zan biyo jirgi yau din nan zan dawo musan abunyi nan take suna gama waya ya soma kokarin siyan ticket .”

Ammi bata ajiye waya ba ta kira diyarta shafiq tace “maza maza tazo tana son ganinta sadiq ya biyo jirgi daga abuja zuwa lagos cikin tashin hankali kai tsaye gidan ammi ya wuto kusan a tare suka qaraso da shafiq suka kulle kansu adakin ammi domin neman mafuta batare da sun bari hasera ta fahimci wani abu ba ,dukkaninsu zuciyoyinsu babu dadi domin kuwa daga dubansu kasan wannan taron ya sha bambam da sauran da sukayi domin kana hango fuskokinsu zaka gano dimbin damuwar dake tattare acikin zukatansu.”
Tunda aka soma gudanar da taron hally ke zubar da hawaye yayinda zuciyarta ke hasko mata fuskar mijinta ,murmushinsa kawai take gani wanda ya zame masa jiki ko cikin fushi yake dole sai anga wannan murmushin,sosai zuciyarta ke cike da keyarsa, sadiq yayi gyaran murya “kukan nan ya isa haka hally karki manta da condition din da kike ciki damuwarki zata iya haifar da matsala wa abinda kike dauke dashi addua zakiyi masu a duk inda suke allah yasa lfy ya dauke idanunshi akanta ya maida kan ammi da itama yanayinta ya nuna dauriya kawai take “zanje yanzu na samu malam mudi mu tautauna akan alamarin domin nasan bazai rasa sanin halin da’ake ciki ba .”
“To shikenan sadiq sai na jika allah ya tsare yasa muji kyakkyawan labari “Ameen ya fada tare da mikewa ya wuce .


Mumy na zaune taji sallamar Unty maryam tare da turo kofar dakin dake an fada masu a second flow no 20 tanwer take kwance mumy ta amsawa Aunty maryam matar uncle jamil ce kanita tana gama kutso kai sai ga uncle jamil da diyarsa amira me sunan mumy suka shigo kana ganin fuskar mumy kasan tana cikin damuwa da tashin hankali amira dake biye da uncle jamil ta qarasa da sauri ta fada jikin mumy tana tambayarta tanwer “mumy ina aunty tanwer take ita nazo na gani please ki kaini gurinta kinji “.?
Da kyar mumy ta bude baki tace “karki damu zan kaiki gurinta kinji takwarata ta fada tana shafa kanta tare da yiwa kaninta da matarsa sannu da zuwa “aunty ya me jiki kuma ?inji cewar aunty maryam “alhamdulillah mun godewa allah likitoci sun tafi daita zaa duba brain dinta sun dade suna tautaunawa a tsakaninsu har sanda dady ya shigo bakinsa dauke da sallama amira ta mike ajikin mumy ta fada jikinsa ya rungumeta ajikinsa sai yaga kamar tanwer dinsa ce ajikinsa ,tana yarinyar babu abinda ya rabasu da amira uncle jamil ya mika masa hanunsa suka gaisa shima ya tamabayesa me jiki sun dan ta’ba hira ya mike ya fita zuwa office din likita .”

Washegari

Suna zaune aka turota akan gadon marasa lfy tana bacci babu abinda ke motsi ajikinta idan ka dauke bugun zuciyarta hannunta na manne da qarin ruwa aunty maryam na kan sallaya ita kuma mumy tana lazimi zuciyarta na zugi cikin bacci tanwer take jin kanta na mata wani irin nauyi zuciyarta na mata radadi a hankali bakinta ke motsawa “adnan ka cuceni me yasa kamin hk ?”me yasa ka zabi sana’ar fashi da makami ?sosai mumy ta tsura mata ido tana kallon bakinta tasan bai wuce sunan adnan take kira ba ita dai tana ganin lokaci yayi da zata shiga cikin lamarin zata dauki lauya har lokitoci suka bar dakin batasani ba sallamar dady ce ta dawo daita daga duniyar tunani ya mayar da kofa ya rufe ta amsa tare da goge kwalla da ta cika idanunta lokaci guda ta katse lazimin da take tai masa sannu da zuwa ya amsa yana tambayarta mai jiki .?”

“Da sauki “ta bashi amsa zainab yau bata bude ido bane “Ya tambayeta yana tsayuwa a gefen gadon yana kallon tanwer cike da tausayawa har yanzu bata farka ba yadda suka fita daita haka suka dawo daita aunty maryam ta gaishesa ya amsa yana cewa “bari naje naga likita ya juya ya fita.”
Doctor muyis na rubuce rubuce akan file dady ya shigo dr ya dago yana dubansa sannan ya mike cike da girmamawa yana gaishesa tare da nuna masa kan kujera yana cewa “yanzu nake shirin kiranka nan ya shiga karfafawa Dady zuciya “karka damu dady muna iyakacin kokarinmu inshaallahu nan ba dadewa ba tanwer zata dawo daidai kamar yadda take domin mun gama magana da dr sadiq zai zo cikin satin nan ya dubata kuma inshaallahu zaa samu nasara kafin nan ya fadi irin gwaje gwajen da zaa mata yanzun haka anyi mata .”
ya fad’a yana sake karfafa masa gwiwa “wani irin matsalata ne haka idan kunsan bazaku iya dawo min da yarinyata daidai ba ku fad’a min na fitar daita zuwa wata kasa na huta da wannan bakinciki kullum magana daya “? Ya jefa masa tambayar

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button