KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

A tsanake ya zare hannunsa cikin nata ta sake runtse idanunta gam jikinta na sake ɗaukar zafi  jallabiyar jikinsa ya zare, ya ajiye akan madaidaicin table din dake  gefen  gado, idanunshi na kanta yana zance zuci. ‘Allah kada kasa wani abu ya sameta a dalilin wannan shirmen nata na banza ,ban da abunta ma  guda nawa take da zata d’aurawa kanta damuwar  soyayyarsa ?  tayi kankanta da daukar wannan nauyin, matan da suka fita girma da wayewa da komai  fiyye da nata  sun kasa shawo kansa a batu na soyayya bare ita , shi sam babu wannan a ransa “

   Rankwafowa yayi  jikinta tare da tokare hannunsa  da katifa idanunshi na kanta zuciyarsa cike da matsanancin tausayinta duk cikin masu nacin sonshi ita kadai zuciyarsa da gangar jikinsa ta tausayawa ,bai sani ba ko dan ita din yarinya ce mai karancin shekarun da bata wuce autar d’akinsu ba ,hannuta daya ta Kai gefen kanta da taji yana sara mata da karfi  a hankali ta soma  motsa bakinta, matsota ya sake yi dan jin abinda zatace “mr.no name am feeling very dizzy”. tayi mgnr tana bude idanunta akan shi eye’s into eye’s suke kallon kwayar idanun juna “bana gani sosai ta karasa maganar tana kai hannunta kan  damtsen hannunsa ta rike gam jikinta na sake daukar zafi  “Mr.no name!”. ta sake  kira sunansa tana lumshe ido “na kasa fahimtar meke damuna kaina ke…”
tayi shiru tana sake rike gefen kanta, cike da sanyi jiki yake binta da idanunshi yana shafa gefen fuskarta har ya kai   hannunsa daidai kunnenta tare da zira yatsansa ɗaya , wani irin zirrrrrrrr taji a  gbdy ilahirin jikinta mai kama da shoking  take jikinta ya ɗauki rawa ganin haka yasa yayi saurin  yin kasa da hannunsa zuwa gefen fuskarta ya cigaba da  shafawa a hankali ta sake Kai hannunta kan damtsen hannunsa tana lumshe ido matso da fuskarsa yayi daidai nata  har karan hancinsa na gugan nata tare da   riko yatsun hannunta ya dunkule guri daya yana kallon kyakkawar fuskarta yana jin yadda bugun zuciyarsa ke karuwa ,numfashi kawai take janyowa tana fitarwa da kyar .

Motsin kwankwasa kofar d’akin yasa ta tsaitsaita numfashinta  ta buɗe idanunta fess tana kokarin kallon kofa shi kuwa har lokacin hannunsa na kan shafa fuskarta haka idanunshi na kan fuskarta ya kasa daukesu “mr.no name, kamar wani yana buga kofa”. Ta furta a hankali “karki damu babu Wanda zai shigo d’akin nan sai da izinina tayi shiru “ki yarda dani babu wanda zai shigo hannuwanta duka ta Kai qirjinsa tana yarfesu,  sautin wata murya ce ta doke dodon kunnenta “hey adnan open the door plz, is me”. hade da buga kofor da karfi kamar za’a balla a hankali ya dan juyo yana kallon kofar sakamakon jin kuryar zahra “adnan!”……….
ta furta sunan   tana lumshe idanunta  wani irin dad’i taji ya mamayeta atleast she know his name yadda  yake da tsananin kyau haka sunansa ke dadin ……. .

Tsura mata ido yayi saboda jin sunan daga bakinta “sautin mace naji ko matarka ce?!”. tayi maganar hankalinta a matukar tashe tana mai sake Kai hannuwanta qirjinsa ta fara turesa ya mike yayinda take kokarin saukowa yayi saurin maidaita “ki kwantar da hankaliki ki kwanta ki dan huta bari naje na dawo sai mu tafi”. ya janyo rigarsa ya zira ya nufi kofar  sai ganinta yayi ta mike tana neman hanyar buya yayi saurin riko hannunta “ina  zaki?!”hannunsa tabi da ido  “,ki koma  ki kwanta ki bani minti biyu yanzu zan dawo mu wuce”

  ” adnan dan Allah ka bude min kofa mana!”. Aka Kuma fad’a daga daya bangaren take jikinta ya kama rawa ta soma zazzare idanu hannunsa  duka yasa ya riko kafadunta ta zaro ido tana  kokarin fixge  jikinta “wayyo Allah tsoro nake ji kar matarka ta ganni, if she see me what will she do nasan! kasheni zatai “yes she will definitely kill me, dan Allah ka boyeni”.  tayi mgnr a rud’e sound dinta na tashi tana ko’k’arin buya a jikinsa , hade rai yayi “ke malama ki kwanta nace!”.
yayi mgn a tsawace  yana nuna mata katifa cike da sanyin jiki da tsoro tayi taku biyu ta zauna a gefen katifa jikinta na rawa  ya k’arasa jikin kofar ya Kai hannunsa kan handle yaji kofar a kulle gam tsaki yaja “a she a rufe kofar take  shiyasa Zahra ta kasa shigowa” yayi magana a k’asan ransa , murda key yayi  hade da zarewa ya fito yana sauke idanunshi akanta “Kai da waye  a cikin d’akin?!”. tayi tambayar kamar wata zararriya tana wani irin huci tamkar mijinta .

“Muje”. Ya mata alamu da hannunsa yana nuna mata daya part d’in. Kallonsa tayi cikin zafin rai tabi ta gefensa ta tunkari ko’far da Tanweer take cikin zafin nama yasa hannunsa ya fincikota baya. “Me kake nufi Adnan karuwa ka kawo gidan nan ?”. Tayi maganar tare da k’ura mishi ido. “Ba karuwa bace kar….”. “Karuwa ce mana” ta sake  furtawa cikin d’aga murya, runtse idannunsa yayi jin tana Kuma had’a Tanweer da mummunar kalmar sosai ranshi ya soma baci.
“Na fada miki ki daina kiranta da wannan mummunar kalmar dan ba ita bace”. ya fada cike da bacin rai  yana huci  yayi  cilli da hannunta daya rike , Kallonsa tayi tare da murmushin takaici ta kara yunk’urawa. “Koma wacece wannan karuwa sai na…”. Fisgota yayi da karfi  tare da shimfid’a mata wani irin gigitaccen  mari, kan ta dawo hayyacinta ya fisgeta tuni zuwa hanyar da bataso, bai ajiyeta ko Inaba sai wani katon d’aki.
  Cillata yayi gefe ya juya zuciyarsa na masa wani irin zafi. “Adnan!”ta Kira sunansa cikin d’aga murya tana sha gabansa. “Wacece kuke magana? Wace matsiyaciyar yar kar…”. Tasssss ya sake  d’auke  kyakyawar fuskarta da wani  gigitaccen mari wanda yafi wanda ya mata a baya, fashewa tayi da wani irin kuka. “Nace ki daina me yasa bakya…”. “Yanzu akan wata ‘ya mace kad’au hannu Ka mareni? na shiga uku!”. Ta katse shi cikin muryar kuka tare da k’ara fashewa da wani sabon kukan ta koma gefen gadon ta zauna baka Jin komai sai fitar sautin kukanta.

Shiru yayi qirjinsa na masa wani irin rada’d’i da zafi  wanda baisan na meye ba b’acin raine ko kukanta ko kuma kalmar karuwa  da zahra ta danganta yarinyar dashi ne , shiru yayi yana sauraron kukanta gashi  abunda yatsana kenan  a rayuwarsa  yaga mace na kuka ,sanin hakan yasa Zahra ta k’ara k’arfin kukanta, bud’e  idanunsa dake runtse  yayi , cikin wani irin zafi ya soma taku a hankali har ya k’arasa bakin gadon, zama yayi daga gefenta. “Look Zahra! Kiy…”. Sake fashewa tayi da wani sabon kukan  “Ya Salam!  dan girman Allah kiyi shiru ki daina wannan kukan dan Allah”ya fad’a lokacin daya  Kai hannu yana d’an bubbuga kafad’arta, a hankali Zahra ta sulale ta shige jikinsa. “Baby  wacece wannan yarinyar daka mareni  akanta ? “tayi masa  tambayar tare da sauke  ajiyar zuciya ..

“Bakowa bace!”. Ya furta hakan cikin ko’k’arinsa na kauda zancen dan jinta a jikinsa ba k’aramun tada mishi sha’awa tayi ba musamman yadda ta tura hannunta cikin k’irjinsa tana wasa da kan nipple’s dinsa lumshe idanunsa yayi gaba daya  tare da laso busasshen labbansa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button