KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

tsayuwa tayi agurin tamkar an dasata tana kallon every step of him wani irin tafarfasa zuciyarta keyi da sauri sauri tare da tsantsar nadama “me yasa tayi react irin haka ? me yasa tayi masa rashin kunya ?me yasa lokacin da yake maganarsa bata rabu dashi ta zuba masa ido ba tunda ta fahimci damuwa daita ne ya janyo haka ?”Why why tanwer!! jikinta ne ya kama rawa rawa taji kamar ta daura hannuwanta bisa kanta ta kurma ihun tare da kukan neman dauki amman haka nan ta tsinci kanta da kasa aiwatar da ko daya sai ma taji zuciyarta ta bushe tana kallonsa ya dafa kafad’ar anas cikin mawuyacin hali sannan ya zagaya ya bude bangaren direba ya shiga ya zauna .”

Tayi tunanin anas zai karaso gareta ya tambayeta dalilin fushinsa ita kuma ta samu damar fahimtar dashi komai da matsayin dr muyis agurinta sannan ta nemi alfarmar ya shawo mata kanshi amman sai taga sabanin haka shima ya bude bangaren da yake jingine ya shige jaguwa ya figi motar da dan gudu suka nufi get ,dumi taji akan kuncinta ,ko bata duba ba tasan meye ya zubo akan kuncinta tana tsaye cikin wannan tashin hankali dr muyis ya karaso zai rike mata hannu ta goce da sauri dan ganinsa ma kara mata bakin ciki yayi tunda duk shine ya janyo mata wannan tashin hankalin da take ciki ,tana zaman zamanta tana neman hanyar da zai amince wa aurenta amman kuma ga abinda ya faru “meke faruwa tanwer ?wai waye shi wannan mutumi ne? “yau karo na uku kenan ina ganinsa tare dake please ki fada min waye shi ina da bukatar saninsa da sanin matsayinsa agurinki da har yake da karfin halin fada miki maganganun banza ?”.bata ce masa uffan ba illa tsakin data ja sannan tabi gefensa ta karasa inda motarta take ya bi bayanta da kallo har sanda   ta bude gidan baya ta cilla hand bag dinta ta rufe ta bude mazaunin direba ta shiga ta zauna tare da kunna motar ta nufi get stil yabi bayan motarta da kallo kamar yayi kuka yaso ta tsaya tayi masa bayanin matsayinsa dan yasan ta inda zai dauki mataki ,”

Wani irin mugun gudu jaguwa yake yi akan titi har sai da anas ya waiga yana kallonsa “kayi parking a gefen titi please ka bari na karasa damu gida gudun da kake yi yayi yawa ,Iska mai zafi ya furzar batare da yace uffan ba ya cigaba da tuki can kuma ya soma magana “ni tanwer zata fadawa magana alhalin bata san abinda ya kai gurinta ba ?tasan me zan fada mata da naje gurinta tayi min wulakanci ? daman na fada maka soyayya karya ce ba gaskiya ba “. ya karasa maganar yana dukan stearing mota da karfi.”kamar ya kwashe masa da dariya amman kuma sai tausayinsa ya mamaye zuciyarsa dan ya fahimci zallar kishi ne ke dawainiya da ruhinsa “ni zata wulakanta akan wani banza wallahi tayi na farko tayi na karshe dan sai ta sake ganina arayuwarta sannan tayi tunanin sake min wulakanci.”
“Cool dwn my friend karka ce haka yana da kyau ka tsaya ku fahimci juna idan da hali ma ka bata umarni daina sauraron kowa “karta fasa ta cigaba da sauraran  kowani kato is not my business ko jikinta zata dauka ta bashi tayi bazan damu ba ,wai har da cemin idan ta sake kulashi me zan mata imagine anas wai ni tanwer take fadawa haka ?anas ya kawar da kansa gefe yana murmushin mugunta ” wai aurenta nayi da zan hanata kula maza tunda ban aureta ba zata kula duk wanda take so well ta cigaba da kulasu ya fada cikin daga murya Ana’s bai juyo ya kallesa ba saboda murmushin dake kwance a fuskarsa ,tanwer bata taba  burgesa ba kamar yau abinda ya kamata tayi kenan tun farko ta zauna tana lallabashi .”

Tafiya kawai yake akan titi batare da yasan ina zai nufa ba lokaci lokaci anas ke waigosa ya kalli yanaynsa agogon hannunsa ya kalla yaga karfe biyu har ta dan wuce ,yace ” dan allah ka dawo haiyacinka ka dauki hanyar zuwa gida sai yawo kake yi da mutane ,jiki babu Kwari ya dauki titin unguwarsu cikin minti goma suka karaso jiki babu kwari ya fito ya shiga parlour sai dai kafin ya shiga ya boye abinda ke ransa baya tunanin zai bari su jubi su san halin da yake ciki dan sai suyi masa dariya, tsabar fadin rai da bakinciki bai kula kowa ba acikin gidan ya wuce dakinsa ya zube akan kujerar yana sauke naunayen ajiyar zuciya.”
Kwalin sigari dake ajiye akan karamin table ya dauka ya zaro guda daya ya kai bakinsa ya kunna ya fara zuka yana fitar da hayaki ta hanci ta baki zuciyarsa na sake shiga rudani da tashin tashin hankali “Ni zaki wulakanta tanwer wallahi baki isa ba ” anas daya shigo ya zauna kusa dashi yace “dan allah ka samu natsuwa bafa haka akeyi ba ,barni kawai anas dan dai ba a gabanka tayi ba nasan da sai ka wanke min ita da mahaukacin mari da zai sa ta dawo haiyacinta tasan tayi Kuskure ,yarinyar nan sam bata da mutunci ai kuwa ganin idanunta zata ga aikin marasa mutunci dan wallahi tayi kuskuren takowa gidan nan sai na ballata naga uban daya tsaya mata “Wallahi adnan kai ma har da laifinka yarnyar nan sam bata da laifi , wani irin kallo ya waiga yayi masa yana kashe sauran sigarin hannunsa ya dauki wani ya kunna ya kai bakinsa .”

“yes bata da laifi adnan tunda tabika ta sadaukar maka da komai nata ,ta soka fi sabililla bata kyamaceka ba me kuma ya rage ta maka ?mu ajiye maganar wasa ta fika gsky tunda baka aureta ba kuma bakace zaka aureta ba kaga baka da damar bata umarni akan wa ya kamata ta kula ” tashi yayi bai ce masa komai ba ya dauki kwali sigari da farantin zuba toka ya shige bedroom dinsa cikin fushi tashi anas yayi ya biyosa da sauri yana masa magana “oh biyoni kayi ka cigaba da qara min damuwa akan wanda nake ciki ? “kai dai adnan bazaka canza ba bafa haka ake yi ba, sai anyi hakuri ni nasan zata kiraka ta rarrasheka cikin lumana ta baka hakuri duk da bata maka laifin komai ba “a wajen ka kika ganin bata min laifi ba amman ni a wajena jin abinda tamin nayi kamar na mutu
mace bata taba min abinda tay min ba kai kasani .”

“Nasani adnan amman dan allah kayi hakuri kaji maganata har yanzu tanwer yarinya ce sai ka kara hakuri daita sannan kayi kokari ka fada mata cewar kana sonta zaka ga sauyi na ban mamaki “sai na furta ina sonta zata daina kula maza ?yayi masa tambayar a fusace yana fesar da hayaki idanun shi sunyi jawur sun canza kala tsabar tashin hankali da shan sigari dan ya kusan tashi da kwali daya ,”no adnan ba haka nufi ba zata dai ….”kaga ya isa ya isa !! kama hanya ka wuce gida kawai muradin ranka na can tana jiranka ,” Ana’s bai san sanda dariya ta subuce masa ba ai kuwa ya shiga yi yana kallon jaguwa ,shi kuwa tsaki ya ja ya soma zariya a dakin still yana  bankawa cikinsa hayaki sai da anas yayi dariya mai isarsa sannan ya matso kusa dashi ya amshi sauran sigarin hannunsa ya dauki kwali ya bude ya duba sauran kara daya aciki “me ye haka adnan ?jaguwa ya tsaya tare da juya masa baya “karka sake shan sigari wanda ka sha yanzu ya isa haka, haba zaka kashe kanka ne akan mace just common mace fa ? yarinyar ma dakace baka sonta me yasa zaka damu kanka dan kaganta da wani “?.

Ya juyo a hankalin ya fuskancesa sosai zuciyarsa na karkarwa da zafi kamar ana diga masa wutan dalma, kamar yayi kuka yaji saboda maganarsa sai dai shima yasan haka ba me yuwa bane agurinsa ya bari anas yaga rauninsa akan tanwer ,a hankali ya motsa lip’s dinsa ya soma magana cikin sanyi murya “gsky bai kamata na damu ba well daman bawai kishi bane kawai dai naji babu dadi ne ,ganin yadda wancan mutumin yayi kusa kusa daita kamar zai cinyeta amman daga yau inshaallahu bazan sake damuwa ba ko naganta dani .
“very gud abinda ya kamata kayi kenan tunda baka sonta bazaka aureta ka barta ta cigaba da rayuwarta cikin salama da kwanciyar hankali,ka barta ta kula duk wanda take so kuma a sanda taso ,ko cinyeta zasu su cinyeta ina ruwanka tunda kai bata da amfani agurinta?  “ya karasa maganar yana danne dariyarsa jaguwa yayi masa  wani rikitaccen kallo yana maimaita abinda ya fada a kasan ransa babu kalmar data nemi zautar dashi kamar “ko  cinyeta zasu su cinyeta ina ruwanka . ya lunshe rikitattun idanunshi yana jin zafi da ciwon maganar “Ana’s me yasa zaka fada min irin wannan maganar “?Wacce magana  na fada maka ?saurin bude idanunshi yayi yana dubansa sakamakon jin abinda ya fada a she a fili yayi manager bai sani ba ,murmushi ne sosai akan fuskar anas dan shi abun nasa dariya yake bashi amman kuma babu halin yinta .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button