KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

“Idan yaki fitowa ku jawo shi akasa har cikin mota domin abinda ya kamaci titirai irinsu kenan tozarci da wulakanci tare da sakasu jin kunya a idanun duniya “. har jaguwa ya bud’e labbansa da niyyar gasawa Ib magana sai kuma ya fasa yafi son ya ganewa kansa abinda zai gigita rayuwarsa dan haka ya cigaba daga kafafunsa ”

Haraban gidan kuwa cike yake makil da jami’an tsaro idanunshi bai sauka akan kowa ba sai akan alhji tahir kallo daya yayi masa ya dauke idanunshi akansa ya maida kan Ib dake qoqarin fitowa yaga yadda zai yi raact idan yaga kuma yaji abinda mahaifinsa yake fadawa yan jarida turus IB yayi saboda gigitan ganin dadysa cikin mutanen dake tsaye gaban wasu daga cikin yan jarida na aika masu da tambaya.”

shiru IB yayi zuciyarsa na bugawa da sauri sauri kar dai wannan tantirin ne ya taimaki amininsa nazifi daga hannun makisan da mahaifinsa ya aika masa?”.ya jefawa kansa tambayar da bashi da me bashi amsa alokacin .”

Tsayuwa ya cigaba dayi a guri daya kamar wanda aka dasa tsabar tashin hankali sai wasu hawaye da sukayi nasarar biyo fuskarsa yana kokarin sharewa izzadeeni abokin aikinsa ya qaraso da sauri yana girgiza masa kai alamar kar yayi kuka hannunsa yasa ya share masa hawayen fuskarsa tun kafin hankalin mutane ya dawo garesa ya rungumesa ajikinsa “tun dazu nake tunani yadda baza kaga wannan tashin hankalin ba ni kaina I was shock da naga mahaifinka yana da hannu dumu dumu tare da jaguwa dake yaji komai daya kawo alhji tahir hannun jaguwa sakamakon tambayoyin da yan jarida suke masa ,
bai boye masu komai ba akarshe yace a tabbatar da an mikasa hukuma anyi masa hukunci daidai da abinda ya aikata .”

“Why dady yayi mana haka ?.”da farko nace how can this even be possible dady ya aikata haka ?”.amman da naji da bakinsa yakewa yanjarida bayani naji kamar an jona min shocking ,hawaye ne suke kokarin sake zubo ma ib ya danne sai dai yayi shiru ya kasa cewa komai .”

“Shine fa dansa daya tak tilo amman ya rasa me zai bar masa sai wannan katoton abun kunya walwal ya biyo bayan gama tmbyr da yan jarida suka masu haka ne ya tabbatar masa da hotuna ake daukarsu cikin tashin hankali da firgici ya waigo inda jaguwa yake lokaci daya sukai ido biyu dashi ya sakar masa murmshi cike da farinciki “wannan ma yana cikin wasan sauran na gaba kamar haka ya fahimci abinda labbansa yake nufi cikin abinda bai wuce minti biyu ba gumi ya rufe IB ya dimauce yayinda jaguwa ke cigaba da sakar masa murmushi wanda ko bai fad’a masa ba yasan na mugunta ne ,cikin karfin halin nan nashi ya bude baki yana son ya furta kalma ko daya ce garesa amman ya kasa kawai ya dinga girgiza kai shi kam me gadi da sauri ya bar gurin ganin irin kallon kaskancin da jaguwa ke masa kar yaje ya karbi bindiga ya harbesa a banza .”

Hankalin ib ya qara tashi domin jami’an tsaro sun qara yawa a inda yanjarida suke hotuna aka dinga dauka mahaifinsa hotuna alokacin da wasu jami’an tsaro ke ta kokarin ingiza keyar jaguwa zuwa waje ba’a samu damar d’aukar hotunansa sosai ba kamar yadda ake ta daukarsu alhj tahir da sauran mutane “wayyo allah dady ka cuceni ka tozartani me yasa kayi min haka “? yaya zanyi da wannan bala’i”?da Wanne kake son umma taji “?duk wadan nan maganagun a kasan ransa yake yinsa yana jin wani zafi aikin zuciyarsa bai sake kallon inda jaguwa yake ba haka zalika bai da ya karasa inda alqali yake ba ya shiga furta inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yana maimaitawa gabadaya ya fita haiyacinsa saboda tsananin tashin hankalin dake tare dashi zufa ce sharkaf ta jike masa ilahirin kayan jikinsa har wani diga yake kai kace daga kogi aka tsamoshi danasanin zuwansa kuwa yayi yafi sau babu adadi.”

wajen gidan kuwa har lokacin mutane ne domin kuwa sun sake dawowa ganin alamun ana fitowa da jaguwa yasa sauran jami’an tsaron dake tsaye a waje suka bubbude murfin motocinsu suka shiga qarar jiniya ta sake karade ilahirin unguwar da kewaye da hanzari jami’an tsaro dana sirri dana sojoji suka fito daga cikin gidan jaguwa duk inda jaguwa yasa kafa nan suke ajiye nasu.”

Jamaar unguwar na tsaye aka tasa keyar jaguwa bayan mota batare da sunga fuskarsa ba dan kanshi na sunkuye akasa ne bakinciki agurinsu ba mai boyuwa bane saboda irin taimakawar da yake masu, dayawa daga cikin yaransu shine ke dauke da dawainiyarsu tun daga lokacin daya tare a unguwar ya bawa ya’yansu da su kansu farinciki hawaye suka shiga sharewa suna biye da motar suna ihun basu yarda a wuce da white lion dinsu ba, dake haka suke kiransa dashi .”

“White lion me yafiya ne ,White lion me tawakkali ne,white lion me farin zuciya ne ,me taimako ne , ku bar mana shi ko wani irin mutun ne shi muna qaunarsa haka akan qaunarsa a shirye muke damu sadaukar da rayukanmu akanshi suka cigaba da bin motar suna ihu suna jifan jami’an tsaro a matukar fusace wasu daga cikin sojoji suka fara laftar mutune da bulala yayinda polisawa kuma ke badesu da tiyagas amman hakan bai sa sun hakura ba suka cigaba da bin motar .”shi kansa jaguwa yayi matukar mamaki bai dauka haka zuciyoyinsu yake cike da qaunarsa ba tun jama’ar unguwar na iya hango motocin jami’an tsaro har suka daina hangosu amman haka suka cigaba takawa wasu kuma suka hau machin suka cigaba binsu har headquarter.”

Headquarter makil da jami’an tsaro kowannensu sanye da uniform sannan rike da bindigu cike da qarar jiniya motocin jami’an tsaron da suka taho da jaguwa suka qaraso bakin get masu tafiyar da halakin bude get suka soma kokarin budewa motoci suka shigo cikin haraban headquarter,direbobi sukai parking aka fito da jaguwa kowani ma’aikaci shi yake kallo , akayi wani qaramin daki mai duhu da jaguwa aka zaunar dashi akan kujera aka daure shi da tsarka sannan aka kulle aka dauki alqali zuwa hospital mafi kusa da headquarter domin a duba lafiyarsa tare zahra domin sune kawai basu da laifi acikin wadan da jaguwa ya boye a gidansa amman sauran duk rukakkun masu laifi ne .”

Ib kam kasa zama yayi ya wuce gida cikin tsananin damuwa yana jin kamar ya hadiye zuciya ya huta da wannan rayuwar “ me yasa ma nazifi da mahaifiyarsa suka tallafi rayuwarsa basu barshi ya mutu ba “?wallahi da wannan rayuwar gara mutuwa agurinsa domin bai san da wani ido zai kalli abokan aikinsa da manyansa ba cewar mahaifinsa dan taada ne .”
yana qarasawa gida part dinsa ya wuce mahaifiyarsa ma bata san da dawowarsa ba ya shiga ya kulle kansa sannan ya shiga balbale botiran gaban rigarsa har lokacin zuciyarsa ta kasa daina mamakin mahaifinsa “wai mahaifinsa na tare da jaguwa ya sha kai masu aiki ba sau daya ba wannan wacce irin rayuwa ce .?”
Ya zube akan kujera yana kuka tamkar qaramin yaro,”

Ya ciro wayarsa acikin aljihunsa ya kira layin nazifi yana dauka yasa masa kuka “ kaga abun kunyar da dady ya aikata min nazifi “? “Nagani kayi hakuri Ibrhim nasan dole zakayi kukan bakinciki amman gaskiya dady baya kyautawa nasan yana da hannu a satar gidan minister da kidnapped din tanwer daakayi nasan komai amman bazan iya fada maka ba wannan ma makisan nan dole ce tasa kasani da har abada Ibrhim bazan iya fada maka ba nan take maganganun ummansa ke dawo masa daki daki alokacin da suka bar kasar “wannan shine dalilin dayasa ya dinga raunata masa jiki dan kar yayi wani abu akai.”
alokacin yayi tunanin duniya da mahafiyarsa ta fada masa mahaifinsa ne yasa amininsa ya dinga masa allurar karya garkuwa jiki ya rasa dalili, lokacin da nazifi ya fada masa batun dady ya kusan ganin bayansa shima bai fada masa dalili ba a she duk sun san komai boye masa sukayi wani sabon kuka ya fashe dashi batare daya kashe wayar ba yana allah wadai da kasancewarsa mahaifi garesa .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button