KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48


Bangaren  hjy  baseera  kuwa tunda nazifi ya bar gidan alhj Tahir take cikin furgici da tashin hankali  ta rasa samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali” tabbas allura na shirin tono garma domin kuwa bazata rungumi son ran alhj Tahir akan tilon d’anta ba ,bazata d’auka ba ,sam bazata zabi halin da yake k’okarin saka ita da d’anta ba akan cikar burinsa  .
shiru tayi tana kallon celling falon tana nazari , tunanin abubuwa da dama suka dawo mata tana jin kamar karta amince da shawarar nazifi na guduwa da Ib zuwa wata kasa   gara tayi komai ta ku’butar da rayuwar d’anta idan ma ta kama ta fito tayi gaba da gaba da alhj Tahir  ta nuna masa tasan komai da yake ciki , amman tasan ko taki amincewa da shawarar nazafi me hali bazai fasa halinsa ba dan ba lallai idan ta fuskancesa  ya fahimceta ba gashi har mugun halinsa yasa nazifi zarginsa akan bashi ne ya kawo Ibrahim duniya ba, da’ace shine ya kawo shi duniya tabbas duk son kudi irinsa nasa dole ya hakura ya rungumi rayuwar d’ansa dan bazai cutar da gudan jininsa  ba wannan shine tmbyr da nazifi ya sha yi mata a tun sanda Ibrahim ya fara rashin lafiya .”

Cikin tsananin damuwa tace ” wallahi shine mahaifinsa shine silar zuwansa duniya kawai dai haka rayuwarsa take yafi son kanshi akan kowa da komai, ta mike jiki a sanyaye ta shiga d’akinta a rikice Inda ta bar ib anan ta samesa kwance yayi shiru yana kallon sama d’akin tunanin tanweer yake yasan da lafiyarsa lau babu abinda zai zaunar dashi dole ta kowani hali ya dawo daita sai ga yadda Allah yayi dashi tashi ma baya iyawa bare akai ga magana duk wani kuzarinsa babu zuwa yanzu ya sadaukar da rayuwarsa  adduar mutuwa yakewa Kansa  ya huta da wannan rayuwar da yake “.

jin motsin shigowa d’akin yasa shi sauke idanunshi ya zubawa mata Idanunsa da suka rikid’e sukayi jazur , a kallon da yake mata ya fahimci bata cikin hankalinta da natsuwarta, ya cigaba da kallonta yana jiran yaji sautin muryarta ,itama kallonsa tayi dukkanin alamun sun nuna mata maganarta yake bukata ji, idanunta suka ciko da ruwan hawayen tausayinta dana yaronta ,ta zauna kusa dashi a bakin gado ta riko tafin hannunsa cikin nata hawayenta na diga  .take hankalinsa ya sake tashi jikinsa ya kama rawa kamar mazari ya soma motsi da bakinsa alamun yana cewa wani abu amman babu hali .
a hankali ta fashe da matsanacin kuka tana kallonsa “na cuceka d’ana ,hakika ban maka adalci ba ,me yasa na auri mahaifinka gashi da kaina na zamo silar cutar da rayuwar d’ana ? na boye maka Mugayen halaiyan mahaifinka amman lokaci yayi da zan fayyace maka waye shi ” duk wannan maganar da take acikin ranta take shima hawaye ne ke gangaro masa yana jin zafi da radadin halin da yake ciki da zubar hawayen mahaifiyarsa sai da tayi kukanta me isarta sannan ta zare hannunta cikin nashi tana shafa sumar kanshi “bari na gyara maka kwanciya ka kwanta kayi bacci inshallahu jibi duk yadda zanyi sai na bar gidan nan da Kai, bazan zuba Ido rayuwarka ta tagyayara ba, ta gyara masa kwanciya ta lullu’besa da bargo ta shiga bayi bayan minti biyar ta fito yana kallonta ta d’auki hijab dinta ta saka ta tsaya akan daddumar sallarta tare da tayar da sallah isha’i . “
bayan  ta  idar  ta tashi ta fita zuwa  kitchen  babu kowa aciki kai tsaye ta shiga store din da kayan  abinci  yake , anan ta kira layin nazifi kira d’aya ya d’auka, ta fashe masa da kuka tana cewa”nazifi ka taimakeni tunda ka bar gidan nan na kasa samun natsuwa  ,hankalina yaki kwanciya Ina ji ne kamar zan rasa Ibrahim dan Allah kasan yadda zamu bar gidan nan da Ibrahim daga gobe jibin da kace yayi  min nisa dan bana son a bata lokaci dan a halin yanzu hankali yayi matukar tashi Ina ji ajikina kmr zan rasashi ne ,idan na rasa Ibrahim nima rayuwata tazo karshe zaka rasani ta k’arasa maganar tana kuka “.

” ki kwantar da hankalinki umma duk yadda kika ce haka za’a yi amman tafiya a goben akwai matsala saboda gbdy Shirin na jibi ne yanzu abinda za’a yi ki shiga d’akin ib ki soma had’a masa duk abinda kika san nashi ne me amfani inshallahu jibi zan zo da zarar dady ya bar gidan ,gobe idan zanzo zanzo da maganin bacci Koda zai zamo yana gida a jibi sai  kiyi masa amfani dashi , bama anan zamu bar Ibrahim ba kasar ma gbdy zai bari na gama shirya komai tunda daman passport dinsa da naki zaku iya fita a duk sanda tafiya ta taso “.
“na gode! na gode !! nazifi Allah yayiwa rayuwarka albarka , yadda ka tsaya min kaima Allah ya tsaya maka bazan ta’ba manta hallacinka ba na gode sosai “.babu komai umma ai “yiwa Kai ne ban d’auki ib a matsayin amini ba kamar dan’uwa na d’aukesa Kuma wanda nake jinsa har cikin raina, Ina qunar ib Kuma zan iya masa komai idan ta kama zan iya sadaukar masa da rayuwata Allah dai ya bamu sa’a .”Ameen nazifi sun d’auki sama da awa suna tautaunawa Kiran alhj Tahir ne ya shigo har sau biyu yasa tayi masa sallama tana cewa  “ka katse Kiran dady’nku na kirana “,to umma  sai goben kenan , ya fad’a tare da katse Kiran ta d’auki Kiran alhj Tahir.

yana jin sautinta ya soma magana cikin fushi da zafin zuciya “kina Ina ne?  sannan dawa kike waya haka tun dazu Ina kira busy busy ? “nida hjy zainab ne ,ta bashi amsa da hakan dan ta rasa me zata ce masa, ta godewa Allah ma  da sunan yazo bakinta , naunayen ajiyar zuciya ya sauke “to ki fito ina falo “tace to gani nan zuwa .
Ta fito ta iske shi hakince akan d’aya daga cikin kujerun falon ta zauna akan kujerar dake fuskarta shi “me kuka tautauna da zainab din haka ? sai data zauna sannan ta fara magana “akan dai tanweer ne “
shiru yayi sannan ya gyara zama yana cewa ” ko ta fad’a miki halin da’ake game da ma’aikatan nan dan yanzu na rasa gane kan lamarin nasu  ?”eh to tace dai tanweer din ta kirasu cikin tashi hankali”  a matukar firgice ya tashi daga rigin ginen da yayi ya zauna sosai yana dubanta a tsorace “uhm Ina jinki cigaba da bani labari sai data numfasa sannan ta cigaba” daga baya shima dan fashin ya kirasu tare da yi musu gargadi me karfi akan jami’an tsaro dake bibiyarsa idan suka cigaba da binsa zai kashe tanweer ta k’arasa maganar tana yin shiru.

“uhm to ita zainab din me tace ? Me kuwa zata ce ai tafi bukatar rayuwar diyarta nan dai tayita masa bayani kamar yadda hjy zainab tayi mata a wayarsu ta shekaran jiya ,jinjina Kai yayi kawai yana kallonta “Suma dai yanfashi nan da wasu kudin suka tambaya suka dawo musu da yarinyarsu cikin girma da arziki dan riketa da sukayi bashi da wani amfani hjy baseera tace” uhm ”  yace “eh mana to meye amfanin riketa da sukayi  ?
duk abinda yace daga” eh! sai uhmmm take cewa a karshe ta tashi zata barsa “bari naje na kwanta. “tun yanzu ? ya fad’a yana duba agogon dake manne a falon. yanzu ne karfe goma tayi “eh yau duk ban zauna ba saboda masu shigowa duba jikin Ibrahim ko  baccin ranar da nake dan yi yau ban samu nayi ba , ko akwai abinda kake bukata ne? “eh idan zan samu bakin shayi nake so “me zai hana zaka samu mana. mikewa tayi ta shiga kitchen ,cikin kankanin lokaci ta had’a masa har zata fito wani tunani yazo mata ta fito ta shiga dakinta ta d’auki kwayar tablet din  da yake sa nazifi yana  bawa Ibrahim  ,ta fito ta markada ta zuba masa aciki shayinsa  ta soma  juya wa a hankali yadda bazai nuna ba “Kai ma kaji azabar da d’ana yake ji inshallahu kafin mu bar kasar Nan  sai karfin jikinka ya ragu mugu kawai  azalumi “
   ta fito ta ajiye masa akan center table ta janyo gabansa alokacin yana kallon labarai ya d’auka ya kur’bi kad’an ya ajiye .
ita Kuma ta wuce daki tana shigowa Ibrahim ya bud’e idanunshi dake lumshe , a natse ta k’arasa Inda yake kwance ta Kai bakinta daidai kunnensa “Ibrahim d’ana jibi idan Allah ya Kai mu zamu bar gidan nan da Kai zuwa kasar Egypt domin duba lafiyarka tana gama fad’ar haka ta cire bakinta ya kura mata Ido yana bukatar qarin bayani “nasan Karin bayani kake bukata zanyi maka amman sai mun bar gidan nan .idanunshi  ya shiga  juya mata alamun bazashi koina ba, idanunta suka ciko da ruwan hawaye “idan har ban bar gidan nan da Kai ba mahaifinka zai yi sanadiyyar ruguza rayuwarka , idan har kana son ka mike bisa kafafunka ka taimaki tanweer ta dawo garemu dole sai ka bar gidan nan kayi nisa da mahaifinka ,zan maka bayani komai kamar yadda na fada maka amman sai mu bar nan , idanunshi ya lumshe mata alamun ya gamsu daita .ranar sam hjy basera bata runtsa ba ta zauna tana shirya duk abinda tasan zasu bukata har  karfe d’aya saura sannan ta koma ta kwanta akan daddumar sallarta .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button