KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

” a wasu shekaru da suka gabata anyi  wani natsatsen yaro wanda ya taso cikin gata da kulawa, yana da mahaifi da mahaifiya da   kane gudu  hudu  namiji daya mata uku , wahalar duniya tayi musu yawa naci ma da kyar suke samu  sai da wannan azzalumin mijin naki yayi nasarar jefa rayuwarsa cikin gararin rayuwar da yasa ya dawo wannan mutumin dake tsaye agabanki , jaguwa ya sake tsuke muryarsa  ya cigaba da magana  “abinda yasa na dan  baki  labari ,mijinki ya cancaci na kashe shi bisa girman laifin da yayi min a shekarun da suka gabata  sai dai na barshi  da halinsa dan hukuncin Allah zai fi akan nawa hukunci ,sai abu na gaba ” idan mijinki  yayi  kuskuren ko gigin sako jami’an tsaro ciki aikina  domin yunkurin tona min asiri ko bincike akaina zan…..
da sauri tace” he wont involved the police farinciki ya ziyarci zuciyar jaguwa saboda ya hango firgici da matsanancin tsoro attare daita, yana gama jin abinda tace yace    “shiga muje kou ” Alh tanko gote yayi saurin waigowa gefensa inda  Jaguwa ke tsaye fuskarsa da alamun tambaya  “karka ɗauka bansan abinda nake ba ,nasan halin  mutane azzalumai irinku masu bin mutane da bita da kulli ka shiga muje kawai ban gama da kai ba idan kuma  mutsu zaka min   yanzu na harbeka  na harbe  kaina muyi  mutuwar kasko ,babu mutsu  ya shiga gaba jaguwa na biye dashi har cikin  mota ,Jaguwa ya zagaya ya shiga bangaren direba ya tayar ya nufi get ….

Suna karasowa bakin get securities suka tsaida shi  warning  glass din bangaren Alh tanko gote yayi suna ganinsa suka shiga rigerigen kawo gaisuwa cike da girmamawa, daya daga cikinsu ya  bude tafkeken get din estate din jaguwa  ya fita  …….

Tafiya kaɗan jaguwa  yayi ya soma motsa lip’s d’insa “nasan kana mamakin kwarewata kou? tanko gote  yayi saurin gyada  kanshi ” karka yi mamaki duk acikin rashin imanin daka dasawa zuciyata ne , idan har baka tuba bisa ayyukan da kake shukawa a doron duniya ba, ka zuba ido zaka haɗu da wanda zai daukeka daga doron duniya gabad’aya ..
ya k’arasa maganar yana murmushin gefen baki  murmushin dake   kashe zuciyar yammata dan duk sanda yayi irin wannan  murmushin dole kaji ya shiga ranka sannan a take zaka rikice akanshi  ,yayinda shi agurinsa duk sanda yayi irin  murmushin to ya samu nasara ne akan aikinsa ,wayarsa ce ta soma babriting  ya   tura hannunsa d’aya cikin aljihun wandonsa ya ciro wayar  sunan Anas ya gani  yana yawo akan screen din wayar, maida wayar yayi  ya ajiye batare daya ɗauka ba sai da suka fita daga  area estate din sannan  jaguwa ya tsaida mota  a gefen titi  “fitar min a mota har yanzu  bazan hanaka kiran headquater na police ba ka kira  ……..”
Kamar jira yake ya bashi umarni ya bude murfin motar jikinsa na rawa ya fita ya tsaya a gefen titi  jaguwa ya fixgi motarsa a guje ya barshi tsaye yana bin bayan motarsa da kallo   ….

Bangaren su Anas kuwa  sun shiga tashin hankali mara misaltuwa saboda ganin jaguwa yaki ɗaukar kiransu dan babu wanda bai yi amfani da layinsa ba amman jaguwa yaki ɗauka shi ana shi so yake  yayi surprise dinsu kusan fitowa suka yi daga cikin gidan suna shawagi a wajen unguwar kowane zuciyarsa cike da matsanancin tashin hankali jubi ne yace “kunga irin halin nasa ko?  “Ban san me yasa yake mana haka ba ana kiranshi yana kin ɗauka “karkace haka bakasan halin da yake ci ba a irin tsoron dake estate din ya cancanci fiyye da haka mu dai mu dai ya dawo lafiya shine kwanciyar hankalinmu inji cewar Anas wanda yayi magana hawaye na gangaro masa ….
ita kanta tanweer haka ta kasance zuciyarta na bugawa da karfin gaske  ga zazzafan zazzaɓi daya ziyarci  jikinta haka nan ta dinga jin wani iri ajikinta idanunta ta lumshe tare da kamkame jikinta guri daya zuwa yanzu zuciyarta cike take da kewar gida ..

Haka ma can gidan minister of health   Kuka sosai Hajiya zainab take  Alh Abubakar   shima kuka yake babu mai rarrashin wani ganin Alh Abubakar na goge hawaye yasa hajiya zainab ta saki wani gigitaccen kuka mai karfi tace “nashiga uku ni Zainab diyar tawa kwaya daya take hannu yan fashi da makami yau kusan kwana biyu Allah idan wani laifi nayi maka ka hukuntani ni kad’ai karka hukunta yarinyata dan batayi laifin  komai ba ,saurin toshe  bakinta Alh Abubakar yayi “haba zainab karkiyi sabo mana  kaddara ce kuma tana kan kowa  tanweer will be fine da yarda Allah lafiya zamu ganta ina iyakacin kokarina akan lamarin ta ko ina jami’an tsaron na kan bincike sannan nasa a tsananta addu’a bana jin tanweer na cikin damuwa kamar yadda muke ciki ,nasan killa suna bukatar wasu ƙarin  kudade ne  daga garemu yasa suka riketa a shirye nake da ko nawa zasu bukata zan mallaka musu komai dana mallaka akan tanweer dan Allah ki kwantar da hankalinki “wani kwantar da hankalinka  zanyi ..”?
“Yan fashi da makami sun ɗauke min diyata kwaya daya tal yarinyata mafi soyuwa acikin raina ta yaya kake tunanin zan iya kwantar da hankalina ?
” waɗan nan  yan sanda dake rike da case din  basu san aikinsu ba basa komai kawai lamuran gabansu suke idan bazasu nemo min yarinyata ba ni na fita na  nemota a duk inda take,  gabad’aya ta gama fita haiyacinta sambatu kawai take zubawa  hawaye na gangarowa daga cikin kwayar idanunta “wayyohlly tanweer ko a wani hali kike ciki” ?”Allah kasa tana cikin koshin lafiya , Allah kasa basu taba min lafiyarta ba ..”

Hajiya Zainab ta zabura daga zaunen da take  ta  mike tsaye  kamar an mintsineta jikinta na wani irin  rawa ,ta soma neman  police headquater ganin take kamar basa komai akan bincike wasu abubuwa take kamar zarariya ko mahaukaciya sabuwar kamu ..

“Sp me  ake ciki akan batun  ‘batan yarinyata har yanzu shiru  banga aikinku ba ?” idan har haka aikin police yake hakika bashi da wani amfani gareni  yau tsawon kwana biyu har yanzu babu wani tsayayyen magana akan batan yarinyata  “
“muna kan aiki ranki ya dade ya fadi haka yana cizan gefen lip’s dinsa da tsotsa geyarsa  “dakata ni ba wannan na tambayeka ba Kawai inda yarinyata take nake son sani  tayi maganar wasu zafafan hawaye na sake wanke mata fuska “ranki ya dade hakuri dai zaki sake yi, babu wata hanya da zamu samu damar gano inda waɗan yan fashi suke sai  Kira daga yan fashi domin bukatar wani abu daga gareku  ta haka ne kawai  zamuyi saurin kamasu ” Alh Abubakar dake tsaye a bayanta a tun sanda ta soma magana yayi gyaran murya ya amshi wayar hannunta yayi disconneting din kiran  “kiyi hakuri zainab tayi saurin zubewa ajikinsa tana kuka”yarinyata tanweer ” “inshallahu za’a kamasu nan kusa ,
Dole akamosu sannan  dole a hukuntasu da hukunci mai tsanani domin  laifinsu daidai yake da wadan da  sukayi kisa..


Gudu jaguwa yake akan titi  ya yaga wata mota baka kiran marcende C class  na bin bayansa duk inda yabi sai motar tabi a karshe ya dauke bakin glass ya rufe kwayar idanunshi ya dauki hanyar da zata kai mutun aja ,gudu yake sosai har ya ‘bacewa motar ya bi wata hanya mai ciyayi ya ja numfashi ya fesar jikinsa na bashi Alh tanko gote ya kira mahaikata, yanzu kam a hankali yake murza stearing motar yana sakin  murmushin cin nasara  Idanunshi ya ɗan lumshe ya ci-gaba da driving dukkanin alamu ya nuna yana cikin jin dadi ya gama da Tanko gote bai yi tunanin abun zai zo masa  cikin sauki ba sai gashi yayi nasara kara lumshe idanunshi yayi …..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button