KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

  “yaron   nan gali  wai  zai  turo  iyayensa  ranar   lahadi  tare da saka rana   gbdy ”  murmushi   jaguwa  ya saki  na  farinciki   yana cewa  ” Allah ya  nuna mana  ranar  lafiya so nake na  aurar dasu gbdy kafin nawa auren . “a’a ban yarda da wannan  tsarin  ba ,idan ma  son samu ne a had’a  auren  da naka ba qaramin  farinciki zanyi ba “shinkenan ammina yadda  kikace  haka za’a yi  bani da za’bin da ya wuce naki  zanyi   k’okari naga anyi auren da nawa sai dai  ki qara  addua akan wanda kike  min     Allah  yasa  na samu me sona tsakani da  Allah  “zaka  samu da iKon allah dan  baka  da  makusar da wata diya mace   zata  kika  ni dai  fatana kayi kokari  ka  cika min alkawarina  Ina  son kyakkyawar  suruka me nagarta   idan   son samu ne   wacce  ta  fika kyau”. wani  narkakken  murmushi    ya   saki  kamar  yana gabanta  kana yace “kin samu kin gama  ammina  dan sai na  kawo   miki  irin matan  hurul’ain  dan irinta  kike  bukata ta zama  surukarki   ya k’arasa  maganar yana dariya    tare da  matsowa  ya kamo  yatsun  hannun  tanweer  ya rike gam  cikin  nashi yana massaging a hankali  ,   itama ammi dariya take sosai tana sake tabbatar masa da hakan  take  so  , ita Kuwa tanweer  gbdy  ranta  a dagule  yake  sbd haushin   abinda yayi mata da Kuma haushin maganarsa da mahaifiyarsa  dan  duk  tana ji abinda mahaifiyarsa ke fada masa   sannan tana   Jin amsar da yake  Bata    cike da  fushi ta  soma k’okarin zare  hannunta  cikin  nashi  tana sauke wahalalle numfashi  sai dai ta kasa  kwatar hannunta dan haka tayita jan  tsaki babu kaukautawa ganin  hk  yasa yayi  sallama  da ammi  tun  kafin  ta  tunhumeshi  ,ya  katse Kiran yana  cewa   “ki  daina wahalar da  kanki  bake  ba ko namiji dan’uwana na rike bai Isa  ya kwace ba bare ke    ” ko   kina tunani ni din irin  lusaran  samarinkanki ne da zaki gwada  karfi  dani   ..?”ya karasa  tmyr  yana furzar da  iska mai zafi daga bakinsa.”

danne abinda taji ya tsaya mata arai tayi  tana zance zuci” shi take  mutuwar so amman shi burinsa kullum ya cusguna mata tare da nuna mata ita din ba kowa bace ,  tunda suka  had’u  yake kyautata mata  ta hanyar  bata  kulawa  sai dai a fahimtarta bashi da burin daya wuce   ya ‘bata  mata  rai  ta hanyar fada  mata  baqaqen  maganganu . tasan  ba lallai ta zamo test dinsa ba amman at least itama tana da daidai nata  kyau sama  sama ta dinga fidda numfashi  tana danne damuwarta  “dan  Allah  direba ka taka  motar nan da sauri  Ina son d’aura kwayar idanuna  akan  iyayena wad’anda   suka zamo min bango abun ma jingina  kuma  farincikina   nasan suma  nice farincikinsu rashina baqaramin  babban  tashin hankali bane  garesu  suna can suna mararina”

  “shiiiii…….” munafurcin  banza kawai   kina dai  son kije kiga wad’an can  rubabbun  samarin naki   barin wancan  me murya  gangarin da bata  dadin  saurara “ya Allah ta furta dan sai  lokacin ta fahimci  a fili tayi maganar , muryarta qasa qasa tace “kafa  san  irin maganar da zaka dinga fad’a  min dan ni din ba motar haya bace bare  kayi tunanin Ina tara kwashe  kwashen  samari Ko da yake yau ne final  kasancewata    da  kai zaka  mayardani  gidanmu  na  gode da  taimako  ta k’arasa maganar tana murgad’a masa  ‘karamin bakinta “karki gode min ki godewa Allah sannan  na fiki jin dadin zan rabu dake na huta da ganin wannan fuskartaki .
muryarta a raunane tace ” aikin banza  kawai  Nima daga yau ai  bazaka sake ganin ko me kama dani bane tayi mgnr tana jan  dogon   tsaki shiru yayi yana ciza gefen lips dinsa can kuma ya murtuke   fuskarsa    yace “wannan shine Karonki na farko Kuma Ina son ya zamo Karo na karshe karki yarda ki sake min tsaki a rayuwarki , ko ni sa’anki ne da zaki dinga ja  min tsaki yayi tmbyr  yana murd’e mata hannu qara ta saki mara sauti tare da cewa “a’a kayi hakuri hannuna zafi  bai mata  magana ba ya sausauta rikon da yayiwa hannun  tare da bud’e tafin  hannun  ya tsurawa tsakiyar hannunta   kyawar Idanunshi yana kallo , a hankali ya d’aura dayan hannunsa ciki  ya fara  mata tafiyar tsutsa wani  irin tsalle hade da bugawa zuciyar tanweer yayi  take tsigar jikinta suka mike kasa cewa komai tayi illa numfashin  da take saukewa  da kyar  tare da jin wani sauyi na dabam  a sansar jikinta.  Shima  wani  irin abu  yake ji yana masa yawo a gbdy ilahirin jikinsa wanda ya haddasawa qirjinsa tsananta bugawa wani tunani yayi gara ya sake musguna mata kafin su rabu   ,wayarsa  ya d’auka ya soma danne  danne bayan kmr second biyu ya kira sunan eku remo dake  tukasu  .”eku ka duba wayarka na  tura maka sako  eku yace “noted  boss ya  tura wa su anas  dake   bayansa  Sako  kamar yadda ya turawa eku sannan ya  koma ya jingina bayansa ya runtse  idanunshi ..”

motar    bata  tsaya a koina  ba  sai   gaban   katon    get   din  Rita Lori hotel   dake  onipan  , get  din   already a bud’e yake kamar Koda yaushe security’s  ne  tam ciki da wajen  hotel din saboda manya  masu kudi da kusoshin  gwanati  dake zuwa  da manya manyan yan fashi da makami , gurin  fitowa daga ciki hotel  din  dabam haka zalika  gurin shiga dabam , eku ya  sanya  hancin  motarsa  cikin Rita Lori,  d’aya daga  cikin security’s din gurin  ya mike da sauri  ya  zare karfen da sakale  Wanda  ke  bawa  mutun damar shiga,   eku  ya   samu  guri ya soma k’okarin  parking  adaidai   lokacin  da motar  alqali  danasu anas   ya shigo
haraban    hotel  ne  dake da  bangare dabam  dabam  dan  shakatawa sam  tanweer  bata fahimci  Inda suke ba saboda ranta dake ‘bace .
a natse jaguwa ya fito ya zagayo bangaren da take zaune  ya bud’ mata   kofa “fito ko “.ya fad’a  yana furzar da iska mai  zafi  daga bakinsa
ta  yunkura a hankali ta fito  tana  jiran ta ganta a haraban  gidansu kawai ta  ganta a Rita Lori hotel a hankali ta dinga bin gurin da kallo qirjinta na dokawa da matsanacin karfi  tana son gano Inda take bata Ankara ba taji ya riko tsintsiyar  hannunta  ya fara tafiya daita  zuwa cikin had’ad’d’en  club din dake ciki,   banda sautin kidi da waka  baka Jin sautin  komai “Ina ne nan ka kawoni  ? tayi masa  tambayar muryarta a tsarke  “gurin  shakatawa yayi  maganar a dake  yana cigaba  da tafiya daita  yayinda har lokacin  hannunta  na cikin nashi jikinta  na rawa taja ta tsaya  qirjinta na wani irin  bugu fiyye da kaida   juyowa  yayi  ya tsaida  idanunshi  a kanta  take ya fahimci damuwar data shiga adalilin ganinta a Inda suke  “gida  mukayi  da  Kai zaka Kai ni me yasa zaka kawoni nan ?shiru yayi kawai yana bin qaramin bakinta da kallo yana jin kmr ya rungumota jikinsa ya hau  sotsan  lips  dinta  .” ni gaskiya gida nake son  zuwa  ba nan ba ka Kai   gidanmu  tayi maganar  kamar zatayi kuka  dan  tuni hawaye sun gama cika mata Ido kafin kace me hawaye sun shiga turereniyar zubowa har da shesheka  hankalinsa ya tashi dan hk cikin tsarkewar murya yace  “Kinga  dan  Allah ki kwantar  da hankalinki bazan cutar dake ba Kuma bazan bar kowa ya cutar dake ba domin ba haka yasa na d’aukoki ba dan haka ki natsu ki kwantar da hankalinki ya dan yi shiru dan jin me zatace itama shiru tayi saboda jin  maganrsa  ” kennan idan ta fahimci maganarsa shine d’an fashin daya d’aukota daga gaban iyayenta  ? wani irin bugu gabanta ya sake yi  da karfi kafin daga bisani qirjinta ya shiga dukan uku uku da numfashinta dake k’okarin  tsayawa hankalinta  yayi matukar tashi ta  dinga maimaita kalmarsa  ta karshe daya furta .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button