KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

camerar  part  dinsa ya kunna yayi rewarning d’aga Inda ta shigo masa ya juyo da tv Inda take “ki bud’e idanunki da kyau ki  Kalli  komai  daya faru “shiru tayi tare da tsaida kukanta shi kuma ya koma jikin bangon d’akin ya tsaya rungume da hannunwansa duka a saman faffadan qirjinsa sai dai gbdy hankalinsa da Idanunsa sun tattara  ne akanta .
a hankali ta fara ganin komai tun daga shigowarta d’akin da yadda ta kunna wutar d’akin ta Isa Inda yake kwance tana shafa jijiyarsa har zuwa sanda ta d’auki bindigarsa da yadda ya amince mata ya kusanceta suman zaune tayi agurin , lokacin data ga yadda ya dinga sarrafa dukiyar fulaninta da yadda ya dinga tumurmusanta bata san sanda ta zamo kasa a gigice ba tana furta kalmar “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ” me ya sameni haka ?”me ya shiga cikin tunanina ?”wallahi ban san na aikata haka ba, bansan abinda ya sameni ba “inna lillahi na shiga uku shikenan na rasa budurcina ?” wayyo Allah ni surayya  ka kuwa san maseefar da ka jefani aciki ? me yasa kayi  sex dani ? “yanzu me kake son nacewa mijin da zan aura ?hawayen ya zubo mata sharr … akan  quncinta  take Kuma jikinta ya kama rawa “gbdy zuciyarta ta sake  karyewa “me yasa  baka  dawo dani haiyaci ba a lokacin ?”wallahi bansan na aikata hakan ba Shima jikinsa rawa yake tausayinta ya kamashi gbdy ya manta wancan tashin hankali da dcp ya jefashi ciki ya matsota sosai yana me jimamin da nadamar abinda ya faru.”

kusancin dake tsakaninsu yasa ta jiyo yadda qirjinsa ke bugawa da karfin gaske “dan Allah kiyi hakuri nasan bakya cikin haiyacinki  lokacin da abun ya faru nayi k’okarin kar hakan ya faru a tsakaninmu amman saboda bakya cikin hayacinki burinki na kusanceki alokacin shiyasa nayi .
“me Ka bani wanda ya gusar min da hankalina  ? girgiza mata Kai yayi alamun “Babu ” Karya ne ka bani wani mugun abu idan ba haka banga dalilin da zai sa na kawo maka kaina ba kayi yadda kaga dama ba ta k’arasa maganar tare da fixgo numfashi da karfi ta fesar  kmr me cutar asthma tayi shiru hawaye na xubo mata “kenan shiyasa a wacan ranar yayita matsa mata lallai sai tayi wankan tsarki ? ashe yasan mugun Abu da yayi mata ta zabura zata mike ya rikota gam ya makaleta ajikinsa yana shafa kanta zuwa  bayanta  yana jin kmr ya mutu , yana son ya fad’a mata cewar asiri akayi mata a waccen ranar yasa komai ya faru yana jin tsoron wani sabon tashin hankalin da za’a yi idan tasan da hakan.
“kiyi hakuri da abinda nayi miki nayi k’okarin gujewa hakan nasan illar abinda nayi miki tunda an ta’ba yiwa yar’uwarta
a lokacin ji nayi kamar na mutu duk yadda mutane ke bani hakuri akan nayi hakuri kasawa nayi har sai dana d’auki fansa da hannuna sannan ruhina ya samu salama ” iya radadi naji a wannan lokacin ,qunar abinda na miki ya tsaya min a zuciya kullum dashi nake kwana nake tashi na zubar da hawaye sosai naji kamar na kashe kaina a ranar ,ki ya femin tanweer domin kece mace ta farko dana amshi budurcinta , bana sonki amman budurcinki shine abinda yafi komai tsaya min arai har na mutu bazan manta cewar ni ne mutumin dana amshi budurcin tanweer ba, kuma bazan daina ganin kima da martabarki ba .”

“Zaka cigaba da ganin kima da martabata  ? ya gyada mata kanshi “amman kace bani da tarbiya ? shiru yayi kawai dan rasa abinda zai fada mata “haka kayita  maimaitawa abokinka cewar ni mara tarbiya ce kuma nasan shima zai tsaya maka arai baza ka ta’ba ganina da wannan darajar ba ? ” no karki ce haka ,kiyi hakuri da furucina na d’azu am really sorry bazan sake ba ya rike kunnuwansa da hannunwansa  , “babu ruwana da  nadamarka  ka biyani budurcina kawai dan wallahi bazan yarda  ya tafi a banza ba”.
shiru  yayi yana kallonta maganarta tayi matukar bashi dariya amman ya hadiye  ,
yarinyata  ne zalla atattare daita bancin haka taya zai biyata budurcinta  daya amsa ?
Numfashi ya fesar  kafin   a hankali ya mike ya Isa gaban wani katon akwatin me  ratsin  baki da ja ya janyo akwatin  zuwa  gabanta   ya bud’e dalolin kudin  american ne cike dashi “bani da abinda zan biyaki dashi sai  dai ….. “dakata ai kasan ni ba bakuwarsu  bace  dan zan iya baka  ninkinsu abinda nafi bukata ka  dawo min da budurcina  na koma yadda nake Kuma a yanzu “.
tsura mata tsumammun idanunshi yayi  kawai yana kallon  karamin bakinta ,ya furzar da numfashi  wanda hucinsa  ya doki  fuskarta ,a natse ya  d’auke idanunshi akanta zuciyarsa na tafarfasa “yau tazo masa da abubuwa a cukurkud’e “Ina  dcp ya samu numbersa da har ya kirasa yana masa barazana ?  sannan da wannan tashin  hankalin da furucin  bakinsa   yayi  nasarar jefashi ciki ,taku  biyu yayi ya  tsaya jikin window  d’akin tare da juya mata baya ,bayansa tabi da kallo batare  tace  uffan ba illa sheshekar  kukan da take zuciyarta na  hasko mata yadda ya dinga juyata    .
A natse ta soma jiyo  sautin muryarsa  na shiga kunnuwanta “ki  shirya  gobe zan mayar dake gidanku  nasan  zakiyi farinciki da  jin  hakan  sannan  dashi kawai zan iya biyanki budurcinki dana amsa  ya  k’arasa maganar tare da juyo ya kafeta da Idanunshi  yana ciza lip’s dinsa na kasa da karfi “.

Wani sanyayyayen farinciki ne  ya lullu’beta alokacin d’aya , duk cikin  kalamansa babu wanda yayi mata dadi ya sanyaya  zuciyarta kamar wannan “zani gida kace ?ta fad’a tana tsareshi da idanunta ya gyada mata Kai alamun “eh! gbdy taji raunin da yayiwa zuciyarta ya Kau hawaye  ya gangaro mata amman wannan lokacin na farinciki ne, sosai take kuka wanda ya rasa dalili a tunaninsa murna da farinciki har ma da tsalle zatayi na barin gidan  .
ta tsugunna kasa ta cusa kanta a tsakankanin cinyoyinta hawaye na cigaba da gangaro mata ya rasa ya zai yi daita abubuwa dayawa suka zo masa kukanta da rabuwar da zai yi daita rarrafowa yayi ya dawo gabanta ya kafeta da tsumammun idanunshi masu kashe mata jiki tun ba’aje koina ba ya soma Jin babu dadi a ransa ,ya bud’e baki da niyyar yin magana kenan kira ya shigo wayarsa ya janye jikinsa ya mike ya karasa Inda wayoyinsa suke ya d’auki wacce ke ruri ya duba sunan amminsa ne ke yawo a screen din wayar dan haka da hanzari ya danna Koren madanni tare da manna wayar a kunnensa ya soma tafiya yana Kiran sunanta “ammi!

bata daga Kai ta kallesa ba har ya bar d’akin  kusan minti biyar da barinsa d’akin ta d’ago kanta  ta  bin hawayen dake zuba akan tafukan hannunta da Kallo.
  a hankali ta soma  share hawayenta zuciyarta na tsinkewa  , ta tsaya shiru tana kallon d’akin har zuwa kan bed dinsa da komai ya faru sosai take tunani matsayar rayuwarta , kwakwaluwarta ta shiga tunani “shikenan ya amshi budurcinta zai   barta ? ” bana sonki amman budurcinki shine abinda yafi komai tsaya min arai har na mutu bazan manta da ni ne na amshi budurcin tanweer ba”  kwakwaluwarta ta dawo mata da maganarsa “Adnan ka cuceni amman  Kuma ka  sake mamaye zuciyata da komai nawa , ka sake samun gurbi acikin zuciyata ,ka amshi abu me daraja da tsadarsa ya wuce komai acikin fad’in duniyar nan to me yasa har yanzu zuciyarka ta kasa amsar soyayyata ?why! why !! adnan kwalkwaluwarta ta toshe kanta ya cunkushe duk abinda ya fad’a rashin sonta daya furta shi yafi komai d’aga mata hankali “nima bazan manta da Kai ba har karshen numfashina ,Kuma har yanzu ban ji na tsaneka  Ina tsananin sonka adnan nasan Allah yana da kyakkyawan nufi akan ni da Kai yasa ya had’amu , yadda nake sonka haka zalika Kai ma kana Sona duk da cewar kana boyewa , amman soyayyata ta gama fallasa kanta ajikinka tunda har abokanka suka san dashi , zan tafi na barka da dunbin qaunata daskare a zuciyarka , ba zaka gane hakan ba sai bayan bama tare idan Kuma hasashena dana  abokanka bai zamo gaskiya ba ” ya Allah ka jarabi adnan da mutuwar sona , yaji idan bai dora idanunshi akaina ba bazai iya rayuwa ba ,
ya kasa samun natsuwa ,ya kasa hutawa ,ya kasa tsaye ya kasa zaune  har sai ya tunkareni da batu na soyayya , Allah kasa na zamo silar shiryuwarsa ya dawo mutumin kirki ….” ta k’arasa maganar tana mai  runtse idanunta  tare da  jingina bayanta da abun gado tana sake zurfafa tunaninta  tun daga  farkon haduwarta dashi har zuwa wattanin da tayi a hannunsa  ta fahimci abubuwa da dama akansa illarsa dai  shan wiwi da  sanar satar  da yake   bancin hk bashi da wata makusa  ,yana qaunar ahlinsa da taimakon mutane gari yana kyautatawa duk wanda yake tare dashi gashi shi din me basera ne ta kowani bangare yana da matukar da basera akan komai .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button