KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

A matukar firgice ammi ta farka ta zauna dafe da qirjinta dake dokawa da karfi tamkar ana buga mata guduna ,ta kunna wutar daki ta waiga bayanta ido hud’u sukayi da hally dake kwance a gefenta tana fitar da numfashi sama sama da alamun ma kuka take ganin irin duban da ammi take mata yasa ta kai hannunta daya ta dafe goshinta dan karta lura da halin da take ciki .”
Bata ce mata uffan ba ta sauko daga kan gadon stil tana cigaba da jin bugun zuciyarta inda wayarta ke ajiye ta qarasa ta dauka tana dubawa a tunaninta zata ga missed call’s din jaguwa kamar kowani dare sai ya kirata ko idanunta biyu ko tana bacci sai dai idan aiki ne ya sha kansa , wani lokacin idanunta biyu wani lokacin kuma tayi bacci sai dai tabi kiransa amman yau babu tayi shiru tana jin mummunar faduwar gaba .”

Ta dawo ta zauna abakin gado tana neman layinsa sai dai kira take ana fada mata number switch off ta kira yafi sau goma amman stil abu daya ake fada mata ta daga kanta zuwa bangon dakin tana duba agogo karfe goma ta wuce da wasu mintuna tayi shiru tana tunani can tayi tunanin ta kira number anas shima abinda aka fada mata ana jaguwa shi aka fada mata jikinta yayi mugu mugun sanyi sai dai a fili tace “yanayin aiki ne .”
Ta dubi inda hally take kwance “kinci abinci kuwa .”?
“Ammi bana jin yunwa .”ta fada atakaice tana danne kukanta ammi ta girgiza kai kawai tana cewa “allah ka iya mana abinda bazamu iya ba wanda zamu iyama karka barmu da iyawarmu ka tsaya mana ,
Ammi ta kasa komawa bacci ta mike ta shiga bayinta dake hade da dakinta ta dauro alwala ta fito ta tada sallar nafila har kusantowar asuba ammi na zaune tana kaiwa allah kukanta haka zalika tana neman layinsa .”


Washegari har kusan karfe biyu na rana tanwer tana kwance tana sharar bacci hankali kwance yayinda mumy da dady ke adduar allah yasa idan ta farka ta dawo haiyacinta ,IB ma ya zo dubata yadda iyayenta basu fada masa dalilin kwanciyarta hospital ba haka shima bai tambayesu ba saboda tunaninsa ya fara zuwa wani guri dabam ,dan kafin yazo gurinta hospital daaka zarce da alqali ya fara zuwa kuma yayi masa bayanin komai wanda hakan ya kusan tarwatsa masa zuciyarsa ya tsura mata ido kawai yana kallonta .”
har ya gama zamansa bata farka ba karfe uku daidai ta farka da ihu da fixge fixge likitoci da iyayenta suka rufa akanta sai dai taki yarda kowani likita ya tabata ta bude idanunta sosai ta zauna a tsakiyar gadon marasa lafiya daya daga cikin likitocin dake duty yace “kwantar da hankalinki ki fada mana abinda kike bukata ya fadi haka ne saboda ya fahimci ta fara fita hankalinta “bana son komai wanda nake so baba ya kai shi qara gurin hukuma dan su kashesa kuma sunyi nasarar kashesa alhalin yasan ina son shi ,”na baya masa ina son shi ina son shi amman yaki barin muyi aure me yasa yayi min haka ?” bani yanci ne akan abinda ya shafi rayuwata ? ta qarasa maganar tana sauke wani irin numfashi da karfi “ku fad’a min fadawa soyayya laifi ne?.”ya girgiza mata kai cikin tsananin mamakinta domin bai ta’ba tunanin alamarin soyayya zai shafi lafiyar ta ba .”

“Please tanwer karki maida kanki mahukaciya bayan da hankalinki why are you like this”?ta bude ta qara idanunta sosai ta kalli sister sabera sannan ta dauke idanunta akanta ta dubi ruky “ruky ina jin yunwa ki kira min adnan ya bani abinci yunwa nake ji sosai ta matso kusa daita “naji tanwer zan kirasa amman kafin nan bari na baki abinci kici da hannuna .”

“Ruky ….”.!

“Karki damu zan kira miki shi kuma zai zo amman kafin nan kici abinci daga gareni “ta fad’a kamar zata yi kuka “nashi kawai nake son ci abincin hannunsa nake so, ku kira min shi nan ta runtse idanunta tana tuno adnan dinta yanayin jikinsa irin rayuwar da sukai yi yanzu ace ya mutu ya barta da tarin soyayyarsa da sauri ta bude idanunta ta mike zata fita daga dakin da sauri suka yo kanta gabadaya suka riketa har iyayenta “ku barni gida zani na hakura bana son komai yanzu bana son ganinsa shima yana da sanya hannu gurin mutuwarsa ,nace masa ya daina aikin fashi yaki ,fashi ba sana’ar bace ko sana’ace ?” ta fad’a tana kallonsu daya bayan.”

ta tsuguna tare da fashewa da kuma suma duk suka tsugunawa agabana ta suka fashi da kuka tanwer ta rasa abinda yake mata dadi , mumy ta rasa ya zatai da alamarin tanwer kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kawai take furtawa nan ta mike taje ta kawo mata abinci tare da ruwa ta kawo mata bata ‘bata lokaci ba ta hau cin abinci bata ji bata gani alamar tana tare da jin yunwa mai tsanani bayan ta gama ta kwanta agurin tana cewa “dan allah ku kiramin adnan na gansa can kuma sai ta rufe idanunta da sauri tace “karku kira shi bana son ganinsa yana bani tsoro har bacci ya dauketa cikin wannan halin .”
????????????????????????
KUSKUREN BAYA
     ????????????????
????????????????????????

PAID BOOK

WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert  domin tabbatar da an tura ko wadan nan number’s din 09136918331 or 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi  sai a tura ta wannan number 09136918331 domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

????️47

……Mumy tasa tanwer gaba tayi kuka har taji babu dadi dady kanshi ya kasa jurewa halin da tanwer take ciki  gabadaya ya daura laifin Akansa sai yana ganin kamar shine silar fad’awarta cikin wannan halin shima tsugunawa yayi a gabanta yana goge hawaye yana jin babu dadi aransa “ina ma yaron bai da wannan katoton mugun tabon a rayuwarsa?”.
“Ina ma wani hali garesa ba fashi yake ba? “.
yanzu yana shiga cikin maganar reshe ne zai juye da mujiya cewa za’a yi yana cikin wadan da suke mara masu baya ,mumy da dady sunyi kuka sosai kafin daga  bisani   likitocin suka dauketa cak tamkar wata jaririya saboda rashin nauyi suka d’aurata akan gado
sannan suka fice daya bayan daya daga dakin cike da matsanancin tausayinta .”

Hally ma rufe kanta tayi a dakin ammi ta sha kukanta ta koshi babu wanda ya sani in ta gaji sai tayi ta addua wani irin radadi son mijinta take ji yana ratsa sansar jikinta tare da jin tausayin kanta yadda abubuwa ke tafiya yana matukar bata tsoro nan ta zaro wayarta ta bude hotonsa tana kallo wanda kullum anan take samun natsuwa da karfin zuciya da sanyi rai murmushinsa na kwantar mata da hankali sai taji ta tsinci kanta da yi masa murmushin .”

Wunin ranar da wannan tashin hankali  mumy da dady sukayi shi tanwer da zarar ta farka zata fara ihu tana  fixge fixge tana fadar abu daya , hakan yasa lokitoci suka fahimci ba wai da gangan takeyin haka ba hankalinta ne ke  kokarin barin jikinta , dole kuma su tashi tsaye domin  ganin hakan bata kasance ba dan irinsu da zarar anyi sakacin barin sun fita kamar yadda take kokarin yi suke qarasa zarewa gabadaya.”

Bayan awa daya da fitar  tomy daga dakin  babu wanda ya sake shigowa  shi kuwa jaguwa sanyi sanyin asuba ne dake shigowa ta window yana shiga ilahirin jikinsa ne ya farfado dashi  ,banda  numfashi sama sama babu abinda yake fitarwa babu wanda yazo zuciyarsa kamar mahaifiyarsa da anas da tanwer ,gara ma amminsa da tanwer yasan suna guri daya kuma duk runtsi duk wuya laifinsa bazai ta’ba shafarsu ba amman halin daya baro su anas fa ba wanda zaa iya jura bane . “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button