KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48


Zahra ,hafcy no-no ,Saira  suna  zaune a falo   sai sukaji knowking Saira ta tashi ta bud’e kofa  police men guda biyar ta gani  tsaye “muna son ganin  “Zahra !
Saira   dake tsaye tace “Zahra ! suka gyada mata Kai alamun “eh !  ta kauce ta  basu hanyar shigowa dan batayi tunanin wata matsala bace    a tunanin me gidansu ke son ganinta tunda tasan akwaita da kan masu kudi  suna shigowa  suka yi wuri wuri suna raba idanu   suna son gano fuskar hoton da’aka basu.
cikinsu babu wacce  bata tsorata ba most especially Zahra  suna gama ganota  suka tunkari Inda take  zaune “are you Zahra?  da kamar tace a’a sai Kuma tace” eh! “Okay muje me gidanmu na son ganinki tace “waye kenan me gidan naku ?”idan muje zakiga ko waye ki hanzarta please ” ta mike ta d’auki karamin   mayafi baki ta yane kanta dashi  dan a shiryenta take ta fito suka wuce har suka Isa station tunanin waye wanda yasa a d’aukota take .

Kai tsaye office din dcp aka zarce daita  suka Sara masa sannan suka ce “sir ga ta nan da hannu yayi musu alamar su  wuce  “ki zauna mana ya fad’a yana nuna mata gurin zama  ta zauna a Inda ya nuna mata tana jira daga garesa qirjinta na dokawa da karfi  byn kmr minti biyar ya dago yana cewa “Zahra ya jaguwa ? lumshe idanunta tayi sannan tace” yana gidansa “gud ko zan iya sanin halakarki dashi ?”eh to saurayina ne da na bukaci  muyi aure dashi  yaki “
ko kinsan aikinsa ?ta girgiza  Kai da sauri  ban ta’ba sanin aikinsa ba Sannan   Ban ta’ba tmbyrsa ba “ya gyada mata  Kai “,fashi da makami ne aikinsa “what ? Zahra ta furta a matukar firgice  tana zaro idanuwanta waje “impossible gsky ban yarda ba, nan take ya shiga mata bayani a karshe ya kunna mata duk maganganun da sukayi dashi tabbas muryarsa ce babu mutsu muna son mu kamashi ko kinsan  sirrinsa? tayi shiru tana nazarinsa ” idan kika bayyana mana sirrinsa  zamu baki million  goma  ”  ta sake yin  shiru tana sauraronsa  da tunanin million goma  , ya cigaba da fad’a mata duk hanyar da suka bi amman basuyi nasara ba 
“gbdy yadda  kuka shirya gurin kamashi  ba tsari bane “
” me yasa kika fad’i haka ? “tamkar kuna lalube ne cikin duhu ,   kun samu  bibiyesa  fiyye da sau  hamsin  amman bakuyi  nasara akanshi ba saboda  baku da wani Abu guda daya da zaku iya rikewa a matsayin hujja  ko tabbacin yadda zaku kamashi byn muryarsa  kunga  har yanzu akwai sauran rina akaba kenan “

“nayi yawo guraren da dama akanshi duk Inda naje ba’a nuna min waye shi   har sai da muka hadu da Kai  yanzu sannan  nasan waye jaguwa  ,abinda wani malamina  ya fad’a min jaguwa  nada mugun  asiri  ajikinsa ya fad’a min cewar muddin ana son akarya asirin jikinsa   sai an daidaici    lokacin da bai tashi a bacci ba, ma’ana a rusashi yana kwance yana bacci akan katifarsa to fa a wannan lokacin dole  asirin  jikinsa ya karye kunga ku Kuma dole ya kamu a hannunku ni Kuma dole burina ya cika akansa   amman matswar ba wannan lokacin ba asirinsa jikinsa  bazai karye   ba sannan batun diyar minister Shima malamina ya fada min ya kamu da balain sonta bazai iya  rabuwa daita ba  Ina ganin shine dalilin da yaki dawo daita .”
“yanzu me kika ganin za’a yi mu rutsashi yana bacci  ?”,dole sai munyi dogon  nazari  akan haka “Yanzu  kirawo numbersa   tunda kina daita muji ko zai dauka “wannan ma wani sabon tashin hankalin ne, yaushe rabon hakan a tsakaninmu dashi ?mutumin dake gudun haduwa dani sai dai duk every each hour Ina samu rahoto akanshi .”
 

“Shikenan  yanzu ki bani numbersa “Taya zan baku numbersa byn Kun Saba tautaunawa dashi ?”duk sanda zai kiramu  yana boye number ne,ki taimakawa kasarki kiyi aikin alkhairi ko sau daya arayuwarki, wannan mutumin dan ta’addane da bai dace ya cigaba da rayuwa ba  shiru tayi kawai tana tunanin ta bayar ne  ko karta bayar  byn kmr mintuna shabiyar  tace  “zan baka Amman kasa baseera sosai dan  yana da matukar hatsari “na dade da sani wannan ta Karanto masa number yayi dialing a wayarsa ya soma kira  alokacin jaguwa na d’akin Jim dinsa yana motsa jiki yaji shigowar kira wani irin tsalle yayi ya danna bluetooth din dake ajiye a gefensa ya manna a kunnensa  “hello..”  jaguwa yayi shiru sakamakon ,jin muryar dcp bai gama tunanin Inda ya samu wannan layin nasa ba ya cigaba da Jin muryarsa “muna sane  da halin da kake ciki  yanzu  amman ka sani karshenka yazo lokacin kamaka yayi.”
“Kai   ka tabbatar da hakan  jaguwa  ya fad’a tare da gyaran abun kunneshi ya kife hannuwansa duka  akasa yana  motsa jiki  ?kwarai kuwa Kuma zaka gani , “meye abun maimaita magana daya Koda yaushe yalla’bai   ?
“wai ma meye  abinda kake gadara dashi da abinda  yake baka wannna kwauri giwar da har  kake aikata wadan nan  abubuwan ?

“Ka sausauta yalla’bai wannan ba abun tada hankali bane ya fad’a yana mikewa tsaye ya kakkabe hannunsa “duk wani shirina na rigada nagama tsarawa aikatawa ce kawai ta rage min adadin mutane da zan yiwa fashi   a lisafe suke  ya fad’a tare da yin  tsalle ya rike kerfe yana sama da kasa jikinsa na budewa  ” Ku daina bincike da bin kwakwafi akaina dan babu wani abu da zai amfana muku dan  bazaku ta’ba samun komai ba sai darasin rayuwa kawai .
“ka kiyaye kanka dan randa zaka shigo hannunmu zakayi da kasani  ….
“daga murya fa ba komai bane agurinmu, masu laifi ake d’agawa murya Kuma kunsan Inda suke , dcp yayi  shiru yana furzar da iska sannan yace  “me kake bukata zamuyi maka muddin zaka dawo da yarinyar nan ?”murmushin gefen baki yayi nasan karshe abinda za’a  sake tmbyata  kenan “me yasa sai akan diyar minister zaku kasa zaune zaku kasa tsaye ?”oho a she fa ita diyar me kudi ce ko ?
“ba wannan muka tmbyeka  ba abinda kake bukata muke so jin “,ku shiga cikin gari akwai Yara irinta bila’adadin da akayi garkuwa dasu wasu sun mutu wasu suna raye zaku iya zuwa ku taimakawa  wadan da suke raye, sau daya kawai kayi aikin alkhairi idan Kuma zaka had’a Kai dani  ni din simple man ne ya karasa mgn  tare da janyo rigarsa ya saka “kayiwa Allah karka manta  kaifa Muslim ne”
“cikakke kuwa “to ka dawo da yarinyar  nan “naji kubani lokaci na kammala abinda nake a karshe ma ni ne zan nemiku ba sai Kun Sha wahalar nemana ba  yana gm fad’ar haka ya katse Kiran duk ya hada gumi tunaninsa Inda suka samu numbersa  Kai tsaye ya fito cikin tsananin damuwa d’akinsa  ya shigo  ya wuce  bayi ya tsaya cikin bathtube ya Kuna shawa a hankali ruwa ke sauka ajikinsa  sosai ya shiga kogin tunani”Ina suka samu wannan number sosai kwalkwawarsa ta shiga lissafi ya dade ruwa na sauka ajikinsa  sannan ya fito ya goge jikinsa ya zira jallabiyar  deep  blue ya fito falo ya goya hannuwansa duka abaya  yana zariya  ko cikakken minti goma bai yi ba  anas ya shigo yana murmushi “mutumina sarkin soyayya wannan yarinya  fa  tayi win … tayi galaba akanka yanzu muka hadu da  pretty take fad’a min wai wulakanci kayi musu akanta “ba’a akanta bane  kawai yanzu zinar ce bana so “
“karka wani waske  kana  fa son yarinyar nan   da zarar anyi magana ka kama wani Shan kamshi amman  kullum cike da  yi mata biyayya kake  da tattalinta  “na sha fad’a maka  babu soyayya a tsakanina daita kuma karka dameni da  wannan maganar dan a halin yanzu bashi bane  a gabana ba kwakwaluwata na bukatar tunani dan gano wani Abu me mahimmancin  ” “tunanin me zakayi ?Kuma me zaka Gano byn mun gano maka , munyi shekaru sama da goma tare taya zan kasa fahimtar abinda kake so Adnan  ?  tsaki yaja “ka daina  fad’a min haka nace ba  sonta nake ba bana  sonta kawai dai  tausayawa ce , taya za’a yi nayi soyayya daita gbdy zuciyata ta mutu babu wani  abu soyayya bayan ta ahlina ,wallahi Ina balain tausayinta ne kuma ko tabar gidan nan zan cigaba da tausaya mata saboda na amshi  budurcinta wanda yake da wuyar samu a wannan  zamani  yarinyar ta  had’u  ciki da wajenta tunda na Kusanceta na kasa cin kowace mace   ilarta  rashin kunya da  rashin  tarbiya .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button