KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48


“Nazifi   haka   mukayi  da  Kai ?a she baka  da amana ban sani ba  ? ya rufe shi da fad’a ta Inda yake shiga ba ta nan yake fita ba  cike da matsanacin firgici nazifi yace “dady me nayi  Maka  ?  bangane me kayi  min ba ? ya tambayesa yana maxurai “,ni zakawa  tambayar  rainin hakali ?  to  yau  duk  a zaune naga Ibrahim  alhalin na fad’a maka bana son ganinsa a zaune sai akwance  dan  lokacin tashinsa bai yi ba tukun  “sai lokacin nazifi  ya fahimci   rashin  amanar da  yayi  masa .   ya  shafa sumar Kansa  yana cewa  “Allah  dady  Ina  iyakacin k’okarina  Ina yin  komai yadda ya kamata  alluran  da na saba yi masa shi nake masa haka zalika maganin da  yake   sha  shi    nake kawo wa  ban canza ba  “.
“wannan karya ne nazifi  “da gaske dady baza yi maka haka ba ,ai duk abinda kace shi zanyi tunda ka zabi abarshi cikin wannan yanayin ni me zaisa naki?” ai ya  zama  dole nabi
duk wani  umarninka  bayan haka ma  duk  sati  sakokan  na shigowa account dina ,nafi tunanin yawon  magani da allurar  da ake masa  ne yasa suka daina aiki   ajikinsa Ina ganin me zai hana a canza  masa ? “. ya fad’a yana tsine masa  acikin zuciyarsa domin kuwa  mutane  masu hali  irin na alhj Tahir sam basu ya  kamata su haifi  d’a irin Ibrahim  ba. “to shikenan na d’auka kana cin amanata ne ?Ina ai bazan ta’ba cin amanarka ba  wannan ai sirri ne a tsakaninmu ” alhj Tahir yayi murmushin jin dadi  yana cewa “to yanzu kana ganin idan an canza masa  za’a samu me karfin  na farko ?”sosai  kuwa  za’a samu  zan duba  me karfi  wanda yafi na farko  zuwa gobe  sai nazo   dashi  “to shikenan na gode son Allah yayi maka albarka ya Kai hannu ya zagaye kafad’an  nazifi yana tafiya dashi  acikin falonsa” ka cigaba da bin umarninna ni Kuma bazan gaji da tura maka   sakona ba “nazifi ya gyada masa Kai tare cewa “babu komai dady ai ko baka biyani ba ya zama dole nabi duk wani umarninka nasan kana da wata munafa me kyau akan ib  shiyasa kake bukatar ganinsa akwance  ?”.

“yauwa  nazifi  a she kana da fahimta ?” shi yasa kullum  kake kara burgeni  saboda kaifin  baseerarka”  cike  da  girmamawa nazifi yayi sallama da alhj Tahir ya fito zuwa babban  falon gidan   Inda ya iske  hajiya baseera zaune kusa da Ibrahim  dake zaune akan wheelchair tana bashi  abinci a baki tausayinta dana Ibrahim ya kamashi ,mace har mace me tausayi  da biyayya  amman batayi  sa’ar miji ba  “har ka  fito nazifi ? “eh  mumy  na fito  “to sannu da kokari  Allah  yayi muku albarka  gbdy , yadda kake kula da abokinka  baka gajiya Allah ya kula da lamarinka  “Ameen mumy ai kula da ib ya zama dole ,  Ibrahim ya  dubesa  wuyansa a karye  magana yake son yiwa  amininsa   amman ya kasa furta Komai  so yake ya sheida masa Kiran daya samu daga bakin  alqali a kwanakin  da  suka  gabata  .

 sai  da nazifi ya sake duba jikin  Ibrahim sannan ya fito zuwa haraban gidan ya  shiga motarsa  ya zauna ya bata wuta,  tafiya kad’an yayi ya  gangara gefen titi yayi parking ya Kasa cire hannunwansa akan stearing motar   ya  shiga  kogin tunani ta yarda alhj Tahir  yake wa  dan lelensa wanda shi kad’ai ya haifa a duniya  mugunta.ji yake kamar ya tattara ib da komai nashi ya turasa zuwa kasar    england  domin ya samu kulawa daga manya  likitoci ,  dan  allurar da mahaifinsa  yake sa shi yayi  masa bata da maraba  da  poising   me karya garkuwar jiki gashi sanadiyyar haka an tsaida komai nashi  bayan shi din mutum ne mai qulafucin  akan aikinsa”gbdy  zuwa yanzu ya soma zargin manufar alhj Tahir akan d’ansa   Ibrahim, idan kuwa haka ne babu shakka akwai  lauje cikin nadi wato akwai saka hannun alhj Tahir  cikin kidnappin  din tanweer da yan fashi suka yi  .
“haka ne ma  zuciyarsa ta tabbatar masa da hakan , wannan dalilin yasa  alhj  Tahir baya son Ibrahim ya tashi  bisa kafafunsa ya nemi tanweer da karfin da iKon da Allah ya  bashi, tabbas Ibrahim nada gogewa da  jajircewa da qulafici   akan aikinsa da  duk wasu masu laifi a kasar nan.
” idan ya gangara ta bangaren aikin sirri shine kan  gaba   saboda kwarewarsa  ya iya  binciken sirri tamkar aljani  tare da abokan aikinsa  har su  gano me laifi  yanzu abinda zai yi zai    cigaba da boyewa alhj  tahir tare da biye masa har sanda zai kammala komai  akan  abinda yake zarginsa akanshi tare da nemo  sheidu  masu   karfi  ta yadda za’a samu nasarar  kamashi a sikwane , yana da tabbacin muddin aka kamashi za’a kama ragowar  abokan sana’ar tasa dukkaninsu su girbi abunda suka shuka ya kusan awa d’aya  agurin yana  saka da warwara har hawayen tausayin Ibrahim ya zubar saboda rashin dacen mahaifi da yayi   sannan ya tada motarsa zuwa office dinsa har ya  Isa office tunanin aminisa  yake ..”


Tanweer  bata  farka ba  sai gurin  karfe d’aya  na rana ta farka cike da matsanacin azaban ciwo  dan   ta sha  wahala sosai  jikinta na rawa koina ciwo yake mata sai numfashin wahala take fitarwa  , wani abu ya hadiye  sannan ya matso kusa daita  sosai  ta  bud’e idanunta  da suka mata nauyi ta ga shine zaune a kusa daita wani marayan kuka ta fashe dashi tana shesheka, muryarsa a kasalance yace “lafiya kike kuka me ya  sameki ? ya fad’i  haka ne dan ya sake tabbatar da tana sane da abinda ya faru a daren  jiya   duk da baya   doubt   akan  gaskiyar abinda baba  ya fad’a masa .ta fashe da wani sabon kuka tana cewa  “nima bansani ba amman duk ilahirin  jikina ciwo yake  min tunda nake ban ta’ba Jin irin wannan ciwon ba dan Allah ka taimakeni ka  maidani gida …..” ta k’arasa maganar  tana sheshekar kuka  bai sake  yin  magana ba ya ɗauketa cak ya nufi bayi daita  ya had’a  mata ruwan zafi ya Kai hannu zai  riko hannunta ta goce ya bita da wani kallo.
ta zabga masa harara tana hura masa hanci ,shiru yayi yana cigaba da  kallonta yayinda  kukanta yaki tsayawa   ganin    ko ya  rarrasheta ‘bata   bakinsa zai yi yasa  a hankali ya Isa  Inda  take jingine acikin  bayin  ,batayi  expecting ba taji ya rungumeta  ajikinsa  tsam , ajiyar zuciya ta saki  ta had’e  rai sosai  .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button