KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Kai tsaye jaguwa gidansa ya wuce zuciyarsa cike da tunanin tanwer yayi hon mai gadinsa ya bude masa tafkeken get ya shigo tun bai karasa parking din motarsa ba ya hagi mutun uku zaune jabir kamil,da jubi suna sha tabar wiwi yayinda kwalabar explorar ke ajiye agaban kowa ya karasa yayi parking din motarsa ya fito yayi mata key ya soma tafiya har ya karaso inda suke zaune idanunsu tamkar garwashin wuta, jaguwa ya dan tsaya nesa kadan dasu yana tambayarsu “anas fa?da hannu suka nuna masa inda yake ya juya yasa kai ya nufi hanyar part dinsa na baya anan ya tarar da anas zaune yayi shiru tare da zabga tagumi yana tunani iri iri acikin zuciyarsa har ga allah baya marmarin su cigaba da wannan aikin sai dai uban gayyan yaki bashi hadin kai dan koda yace masa a abuja idan sun dawo gida zasu yi mgn bai bashi lokacinsa ba lamuran gabansa ya cigaba duk da yasan ba wai ya manta bane lokacin maganar ne bashi dashi .”
daga wannan tunani ya ajiye ya shiga ta aure “yanzu wace yarinyar zai samu ya aura da wannan rayuwar da suke yana jin tsoron faruwar wani abu akansu batare da suna da yayan da zasu nema masu sausauci agurin allah ba “? dama yana da uwa ko uba ne ko dangi da zasu dinga binsa da addua byn baya raye bashi da kowa “waye zai tallafa masa idan sun shiga hannu tunda yasan lallai idan har basu tuba sun daina ba wata rana zasu kamu tunda kwana dubu na barawo ne rana daya na mai shi ?”.
jaguwa ya dade tsaye akanshi anas bai sani ba har sai daya dafa kafadansa batare daya kira sunansa ba ya waigo a dan firgice ganin jaguwa ne ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana riko yatsun hannunsa ya zagayo dashi gabansa ya zaunar dashi akan kujera “bazaka rabu da tunanin aure ba ko? ai shine mafuta akarshenmu”
“bashine ba mafuta ba kanason mu tafi mu barwa ahlinmu abun kunya né?da wannan rayuwar fa babu abinda zamuyi da iyali wallahi ajiyesu bazai amfanemu da komai ba sai nadama shiyasa nake kaucewa auren nan bana son saka diyar kowa cikin matsala duk da ba fatanta muke ba “kai kake ganin haka amman ni sam bana gani wata matsala ni dai ina bukatar aure ya fada afusace cike da jin haushi,sai faman binka nake kana kaucewa bafa tsoronka nake ji ba zan iya tsayawa nayiwa kaina komai duk da bani da kowa a duniya ya karasa maganar cikin tsananin fushi ya tashi ya juya zai bar dakin jaguwa ya riko tsintsiyar hannunsa cak ya tsaya jikinsa na rawa hawaye sun cika masa ido jaguwa ya dawo gabansa ya tsaya anas ya sake juyawa cikin tsananin bacin rai “saboda me zaka fada min hk? me yasa zakace min baka da kowa nifa meye matsayin agurinka da zaka fada min haka ?a she daman baka daukeni danuwa ba anas ?
A she baka daukeni a yadda na daukeka ba ?
Anas ya juyo gbdy idanunshi cike da ruwan hawaye Kmr wani karami yaro “matsawar ka daukeni danuwa muje kayi min jagora gurin ammi ta nemomin matar da zan aura ya karasa maganar hawaye na zubo masa “why anas kake kuka akan wannan abu? bafa akanshi nake kuka ba ina zubar da hawaye ne saboda ka kasa fahimtata kaka supporting dina kasani ko mutuwa zanyi? .
“daman nasan karshen maganar kenan batun mutuwa né zai biyo baya shikenan but naji kace ammi ta nemo maka matar da zaka aura ina ita yarinyar dakace ka samu ?bani da kowa kawai na fada maka ne dan ka maida hankali kayi naka aure wace kimtsatsiyar ce zata aureni ai sai yar iska irina?kai ni ko karuwa ce zata aureni da wannan rayuwar na gode mata “.
Shiru yayi yana tunani ga anas na neman ko karuwa ce amman shi ya samu dama kashi da kashi amman zuciyarsa tayi masa bake bake ta hanashi amsar damarsa bai sake cewa komai ba ya riko hanunsa suka fito suka shiga motarsa da idanun jabir kamil jubi suka bisu dashi kowannensu da abinda zuciyarsa ke sakawa akansu har suka bar haraban gidan basu dauke idanunsu ba .”

A zaune suka tarar da ammi a falo tare da haseera suna kallon tv yayinda hally ke zaune agabanta tana mammatsa mata kafafafu ,a natse suka karasa shigowa bakinsu dauke da sallama ammi dake zaune ta dago hade da amasa salamarsu gbdy daga anas har jaguwa suka rusuna agabanta suka gausheta “ammi barka da yammaci,barka yarana ya kuke ya aiki ?alhmadulillah suka hada baki gurin fadar haka hally ta gaishe da jaguwa tare da anas,ya adnan ya anas ina yinku ?lafiya auta fatan kina lafiya? suka hada baki gurin amsa mata tayi murmushi tace lafiyata lau haseera kuwa ko kallo basu isheta ba ta maida hankalinta kan tv sosai dan yanzu ta fara jin haushin yadda jaguwa yake nuna mata koinkula amman hakan bai sa taji ta fasa aurensa ba ko zai mutu sai tayi rayuwar aure dashi .
Yadda haseera ta nuna koin kula ga danta da aminisa yayi mata zafi amman ta hadiye bacin ranta dan ita macece da bata fiyye nuna bacin ranta ba ,idan kuwa har ta nuna abu ya lalace ganin sunyi shiru sunki tashi daga tsuguno da sukai mata kamar masu neman gafará ta fahimci akwai abinda ya kawosu mai mahimmanci dan haka ta kalli hally da hasera tace “ku dan shiga daga ciki ku bamu guri hally ce tayi sauri ta mike ta bar gurin hasera kuwa sai data yi jim sannan ta mike ta nufi ciki tana rausaya .”

Ammi ta girgiza kai sannan ta numfasa kana tace “fatan dai lafiya naganku jiki a sanyaye ?lafiyar dai ba lau ba anas ne ya tasani gaba lallai sai nayi masa jagora zuwa gurinki “ta gyada kai sannan tace ,ku tashi ku samu guri ku zauna sai naji abinda ke tafe daku a natse suka gyara durkuso zuwa tankwashe kafafunsu suka zauna agabanta shi kam anas tun byn gaisheta da yayi bai sake dago idanunshi ba suna sunkuye akasa.”
“Ina sauraronku meke tafe daku?anas kasa magana yayi saboda wata irin kunya datai masa diran makiya gbdy ya kasa samun natsuwa ahankali jaguwa ya fara fada mata abinda anas yake bukata batayi magana ba har sai dayayi shiru “lallai anas kayi tunani mai kyau kafin wannan ta nuna jaguwa dake zaune agabanta dan shi ina tunanin har yanzu haukan kuruciya bata barshi ba bare yasan abinda ya kamata dan haka anas karkaji komai nima kamar mahaifiya ce tashi ka zauna akan kujera kaji yaron albarka inshaallahu da aurenka dana Sadiq zaa hada tunda shi wannan ya zama babban kwabo jaguwa ya kalli ammi yana wani shagwabe mata fuska “nifa ammi ni ba yaron albarka bane?tai murmushi “shine amman yayi kokari yayi abinda amminsa take bukata dashi sai taji dadin saka masa albarka.”
ya girgiza kai kawai yana kallonta ammi ta mike ta nufi uwar dakanta tana kiran jaguwa “adnan zo na dan ganka ya yunkura ya tashi alokacin da har ta karasa shigewa ciki ta samu guri ta zauna shima ya zauna akan kujera Kushan dake dakin ya tsura mata ido “kasan abinda yasa na kiraka daki?ya gigirza mata kai sannna ya tattara dukkanin natsuwarsa gareta domin yasan duk abinda yasa ta kirasa abu ne mai mahimmanci.
“Adanan nasan halin anas kamar yadda nasan naka nasan sanarsa kamar yadda nasan naka daidai gwargwado anas nada kirki lokaci yayi daya kamata mu saka masa qaunar da yake mana ina jin anas ajikina sosai kmar yadda nake jinka dan haka ni a nawa shawarar na bawa anas auren hally me kagani?
da sauri jaguwa ya zaro idanunshi waje ya zuba wa ammi yana dubanta adan rikice bai tsamaci qaunar anas har ta kai haka a zuciyar amminsa ba lallai amminsa mutun ce da bata manta alkhairi “ya kake kallona haka ko akwai damuwa né ko yana da wata matsla né dani bansani ba ?saurin girgiza masa kai yayi yana murmushin jin dadi “wannnan shawar tayi ammi nima nayi naam da hakan dan inata tunanin inda zaa nemo masa mata .
“kaga sai a hada dana Sadiq domin iyayen yarinyar da yake só sun matsa lallai ya turo iyayensa har gidan nan mahaifiyarta tazo jaguwa ya sake ware idanusnhi sosai “daman anayin haka ba dangin miji ke zuwa ba “? Ammai tayi musmushi dangi miji ke zuwa amman kuma a wasu lokutan nagarta mutun nasa haka kai yanzu me kake ciki da yarinyar nan hasera tana zaune har yanzu kaki kace komai?
“Allah ammi bawai naki cewa komai bane ina tunanin ne ammi ni ba mazauni ba sanarmu bata zama guri daya bace “ba sai kabarta anan ba duk sanda ka dawo tana nan tunda anas yayi tunanin ajiyewa kai me yasa bazakayi ba ?” Ya shafa sumar kansh anas ya sake ballo masa ruwa kenan ?
shiru tayi tana dubansa a tsnake tana nazarinsa “ganin yadda ta kafeshi da ido yasa shi yin mgn “akwai aikin dana sa gaba a halin yanzu da zarar na kamlashi zanyi magana to abari a hada auren gbdy da naka?.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button