KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

sadiq yayi murmushi  yana kallon tan  wacce ta dago ta kalli jaguwa sannan  ta d’auke kanta  ita dai addua take har lokacin ,shi kuwa sadiq ya kasa hakuri hakan ya tsinci kanshi da cewa “aunty nah  ya jikin naki?” ya sake  tambayeta cike da kulawa.” da sauƙi!” ta basa amsa murya a sanyaye a natse sadiq ya soma haɗa kayan aikin da zai mata amfani dashi yana gama had’awa yace “miko hnnunki shiru tayi Taki mika masa sadiq ya    
kalli  yayansa,  jaguwa ya wani haɗe fuska yace “kiyi abinda yace mana karki batawa mutane lokaci  “
Hawayen dake makale a kwarnin idanunta suka zubo duk da kasancewarta likita amman   Allah yayita da tsananin tsoron allura muryarta na rawa tace “ni…ni banason allura a bani magani “.
“dole kiso allura  ko mutuwa zakiyi sai an Miki ” cikin sanyin  jiki  sadiq yace “, father ka bita a hankali kasan mata akwai su da mugun tsoron allura “rabu daita munafurcin ne kawai  ita kanta likita ce  mutane nawa tayiwa allura?  murmushi sadiq  ya sake yi yana cewa ” aha ai likitocin nan sun fi kowa shegen tsoron allura ganin tana ta bata musu lokaci  yasa jaguwa kamo hannunta tare da matseta gam  ajikinsa “bismillah sadiq kayi mata allura ” sadiq ya soma k’okarin tsira mata ta makale  ajikin  jaguwa sosai  tare da sakin K’ara mara sauti ,wani irin harbawa jijiyar jaguwa  tayi da  karfi  take yanayinsa ya sauya   bayan hk  wani sanyi yaji yana taso masa tarayyarsu ta shekaranjiya ce ta dawo masa a hankali tsigar jikinsa suka dinga mkewa gbdy ya nemi natsuwarsa ya rasa    ana gama  mata allurar ya saketa dan idan suka cigaba da kasancewa haka komai zai iya faruwa dan  zai iya danneta a office din.
sadiq ya had’a mata  maganunguna  har dana zazzabi ya mika mata  yana sake mata Sannu  jaguwa yayi masa sallama  suka fito kmr farkon  da zasu shiga yanzu ma hakan ce ta kasance  taji kmr ta fixge daga hannunta ta kwasa da gudu .”

suka karaso Inda sukayi parking  suka tsaya abakin mota kamar ya sani ya bude mata sai data shiga ta zauna ya kulle sannan ya zagaya ya shiga bai   zauna  ba sai daya d’auke  wayarsa
ya zauna yana danna gefenta  yayi mamakin ganin wayar a kashe  ya kunna ya ajiye a ma’ajinta  tare da yiwa motar key ko cikakken minti biyar bayi da kunna wayar ba kira shigo da sauri zuciyar  tanweer ya shiga bugawa da karfi .
ta kame guri d’aya ya d’auki wayar da hannun d’aya yana dubawa yayinda hannunsa ke kan stearing  yana tuki sunan Abubakar Hamid ya gani yana yawo akan screen din wayar  da yake yana da truculler a wayarsa  ,bai gane ko waye ba ya dai d’auki wayar yana dauka yaji saitin muryar hade da Kiran sunan tanweer …!wani wawon burki yaja a tsakiyar titi  ya waigo  yana kallonta “tanweer !!!  are you okay ? shiru cikin tsananin tashin hankali minister yace “Talk to dady  tan where are  you  ? “Inna lillahi ta furta a fili tare da  juyowa  da sauri Jin sautin muryar mahaifinta dake fita cikin tsananin tashin hankali  .
Kit jaguwa ya katse Kiran   tare da ɗauketa da barin  makauniyar  take hancinta ya balle da jini  ,wani kuka ta saki mai ban tausayi  ta bud’e baki zata yi  mgn ya sake yarfa mata wani  mari wannan karon gilmawar duhu ta gani acikin kwayar  idanunta ta sake fashewa da wani  sabon kuka tana neman d’auki tana kallonsa ya  bud’e  bayan  wayar ya cire sim din ciki  ya karya ya watsa a bakinsa  ….”
????????????????????????
KUSKUREN BAYA
     ????????????????
????????????????????????

PAID BOOK
FREE PAGE
 WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
          

WATTPAD @HAUESH

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin na kudi ne  mai bukata karanta shi  ya tura 500 ta wannan  account number din  1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686 alert  domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za’ayi  sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu  a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.

????️17

A matukar  fusace ya bawa  motar  wuta  gabansa   banda  fad’uwa  babu  abinda  yake , ita Kuwa  kuka take  sosai  kamar  ranta zai fita   .
zuciyarsa  ke  wani   irin  ciwo  da  zafi  dan  idan akwai  abinda ya  tsani  gani  shine   zubar   hawayenta    sai  dai  a halin yanzu  baya jin  zai  iya  rarrasheta  ,zai  jure Jin  zafin  saukar hawayenta .hannunta  ta Kai  kan hannunsa  ta  rike  gam hawaye  shabe  shabe  kwance  a fuskarta ,
da  sauri ya waigo   fuskarsa   ya  kalleta   yana  zabga  mata katuwar harara  ,gashi  fuskarsa  gbdy  babu  annuri  , cikin muryar   kuka ta kira sunansa  “Adnan ‘!
Yana  jin ta yayi  mata banza   tare da d’auke  kanshi   ya maida kan  tukin da yake  yana jan dogon  tsaki   “me  yasa  Adnan  ? ” me yasa  bazaka maidani   gidanmu  ba ?”
Shiru   yayi  yaki  ce mata Komai   dan ko  yace  zai yi magana muryarsa bazata  fito  ba saboda ‘bacin rai  dake  daskare  a zuciyarsa  ,zubewa  tayi ajikinsa   ta  saki  wani  sabon   kuka  me  tsuma zuciya  tana cewa “kayiwa  Allah  da manzonsa  ka maidani gidanmu   nagaji ! nagaji !!  ” .
bai ce  ta daina kukan  ba  haka  zalika  bai ce  ta  bar  jikinsa ba ya barta  tayi  kukanta , shi Kuma ya cigaba da  falfala gudu akan titi .”

Bangaren  minister  kuwa cikin   lokacin da  bai wuce minti  biyu 
 da   yaji  wayar  farko da sukayi da tanweer  ta mutu  ba   ya soma  neman   number     din  commissioner  batare  da  bata lokaci ba ya d’auka nan minister ya shiga  zayyano masa abinda  ke  faruwa .  cikin sauri  commissioner  ya  katse  Kiran  ya  kira  dcp   dake   rike da  halakin kula da  binciken  tanweer  kafin kace me  jimi’an  tsaro  sun hallara a gabansa ,cike da natsuwa ya soma magana “please  ku  maida  hankali sosai yanzu  nan  minster yace sun  gama waya da diyarsa  tana  1829 amman  ga  number data kirasa dashi  ya  turo  mana  ku tafi    kuna    tracking  din  number  ku samu location   Inda  gurin yake .
Nan   take  dcp   ya   amshi  number suka  fito  cikin  sauri suka shiga  motocinsu   suna tracking  din number   sai  dai yaki nuna musu location  saboda   number  bata shiga   gbdy  bare su  samu  location din da akayi  amfani da wayar  har  suka hau babban  titi  .
dcp  ya  kira commissioner  yana d’auka  yace “sir  layin  nan bai shiga ba bare  mu  samu locacin din Inda suke   amman zamu k’arasa 1829 plaza  dake igando  ko zamu dace a  nan  akayi amfani da layin yanzu dai    zamu cigaba da  Kiran layin har mu Isa  .”Allah  yasa  ba fahimta yayi ya kashe  wayar ba ? “Dan Allah kuyi aiki yadda ya  kamata  dan yarinyar ta kira  cikin mawuyacin hali  da  alamun tana cikin  tsaka  me  wuya, wannan  wata  dama ce me  kyau da muka samu  kada ku bari ta subuce mana  “okay  sir inshallahu zamuyi iyakacin  k’ok’arinmu “.
Commissioner  ya katse Kiran yana juyi     akan  kujera  gashi dai  shirin tafiya gida yake Kiran minister ya same shi Amman a yanzu ya zama dole  ya    fasa  tafiya  gida ya zauna zaman jiransu idan ta kama ya kwana ma a office zai yi “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button