KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Bai Ankara ba yaga ta soma kokarin yunkurawa tare da kai hannunta jikin murfin mota ta bude ta fara fitar da kafafunta sannan gangar jikinta, ya bita da wani irin kallo yayinda ransa yayi matukar baci zuciyarsa ta soma tafarfasa kamar ya kama da wuta,
Amman dake shi din namiji gaske kuma dauriya da jajurcewa ajininsa suke bazaka ta’ba fahimtar hakan ba atattare dashi ba , abun takaici da bakinciki agareta bai wuce murmushi daya sakar mata byn ficewarta a motar ba gabadaya batare da wata damuwa akan fuskarsa ba ya daga mata hannu alamun” bye bye wanda hakn ya kusan tarwatsa zuciyarta amamn tayi kokarin ta danne damuwarta tayi itama ta daga masa hannunta ta juya ta fara tafiya a natse cikin sanyin jiki ,Shima jikinsa a sanyaye yaja motarsa .”

ta juyo a hankali taga motarsa har ta fice da gudu ta kai hannunta daidai saitin zuciyarta dake beating very fast “allah karka bar zuciyar adnan ta samu sukuni daga wannan lokacin daya furta yana sona da bakinsa ya allah karka bar zuciyrasa ta zauna lafiya ka sake jarabftarsa da matsanancin soyayyata har sai ya amince da tsarina , tayi hanzarin barin gurin ta isa office dinta ta soma hada kayayyakinta masu mahimmanci tana kiran layin direbanta cikin kankanin lokaci ya qaraso ta dauki hand bag dinta ta rataya akafadarta ta fito zuwa haraban hospital din ta shiga bayan mota ta zauna bata san yaakayi taji digar hawaye na gangaro mata a kuncinta dirba yaja suka dauki hanyar gida.”

Direba na gama parking ta fito jiki a sanyaye batare data rufe murfin motar ba ,da kyar take daga kafafunta tamkar wacce bata da laka ajikinta har ta sanya jikinta cikin hadadden parlour’n nasu ta bude baki da kyar tayi sallama, mumy dake zaune a falon ta amsa mata cike da kulawa sai dai kallo daya tayi mata ta fahimci tana cikin damuwa “sannu da gida mumy. “sannu da zuwa tanwer ya fama da jamaa ?
ta amsa sannan ta zauna kusa da mumy tana cewa “mumy yau dai adnan ya amince da zai aureni amman ya tabbatar min sai dai na auresa da aikinsa,ni kuma ko ba d’an alkawarin dana daukar miki ba mumy ba bazan iya rayuwa aure dashi da wannan sanar ba me zanyi mumy na raba zuciyata da soyayyarsa ?”wallahi mumy na gaji da wannan azababbiyar soyayyar ,nayi tunanin zuwa yanzu zai yi tunanin canza rayuwarsa amman sai ya nuna min lallai sai dai muyi aure a haka kuma dole na auresa da aikinsa ko ina só ko bana só ta karasa maganar tana zubar da hawaye .”

“Ya isa bana son wannan kukan mumy ta tsaida
ita daga kukan da take ba musu tabi umarnin mahaifiyarta “ni kaina mahaifiyarki ina jin zafi da ciwon irin son da kikewa yaron nan daga ni har masu qaunarki babu wanda zai so kiyi rayuwa da mutun irinsa domin gibi ne rayuwarki sai dai akwai wasu abubuwa da nayi nazarinsu cikin takaitacen lokaci akansa yasa kika ga ni kaina na amince daki auresa bugu da qari idan adnan ya shiryu adalilinki bakaramin jahadi kikayi ba.”
“ yanzu abu na farko da zakiyi shine “ta fada tana daga mata dan yatsanta daya .“ tunda ya furta miki yana sonki da bakinsa kuma zai aureki ki nuna masa lallai sai dai ya zabi daya aikinsa ko aurenki zanso adnan ya shiru kafin kuyi aure tanwer“.shiru tayi tana kallon mumy kafin ta cigaba da magana “abu na biyu idan bai zabi daya acikin ba ki nuna masa zaki iya cigaba da rayuwa babu shi .”
“Abu na biyu ki rage ko ki koyi boye wannan son
da kike masa ,ki nuna masa kawai idan bazai iya canzawa ba babu shi babu ke idan har lallai yana sonki zaki karya isa da qarfin izzar da ikon da yake ji dashi sannan ki hada da addua wannan itace kawai hanyar da zaki mallakesa ki mallaki zuciyarsa a wasu lokuta dayawa nuna wa nmj zazzafan só irin wanda kike masa babu abinda yake jawowa sai nadama kima godewa allah da ya jarabi adnan da soyayyarki da baki ga katin gayyayar aurensa da wata ba .”
“d’an haka ki kwantar da hankalinki karki sake damuwa akanshi ,ki saki jikinki kiyi lamuran gabanki idan yaga kin fita rayuwarsa gbdy shine zai dawo gareki yana rokonki mumy ta qarashe maganarta tana sakar mata murmushi “wannan shawara ce da umarni idan kika bi zaki ga yadda adnan zai haukace miki wallahi sai ya dawo yana baki tausayi sai ya dawo yana bin duk abinda kike so da duk wasu shawarwarinki ,kiyi kokarin danne soyayyarsa baya ga haka babu abinda zai sauya acikin zuciyarsa kullum kece zaki qare a wahala.”
“Ki saki ranki bari akawo miki abinci kici kinji mamana mumy ta fad’a tana shafa fuskarta.”

Cikin natsuwa da rashin kuzari yake tuqinsa cikin zuciyarsa kuma yana jin tanwer bazata iya barinsa ba ,duk abinda ta fada masa matsayin wasa ya daukesa dole zata dawo garesa dan ya rigada yasan yadda karfi da tasirin qaunar da take masa wannan karfin soyayyar da take masa zai taimaka masa ya sake tsaida hankalinta kanshi amman kuma haka nan yake ji tashin hankali daga kasan zuciyarsa tare da mummunar faduwa gaba.”
wayarsa ya lalubo ya kira layin anas kira daya ya dauka “anas tanwer zan aura kamar yadda kake so ,”dan allah abokina? ya gyada masa kai kamar yana kallonsa amman …“Kai gaskiya naji dadi nasan itama zataji dadi sosai kai allah na gode maka sam yaki bari jaguwa ya karashe masa bayani halin da suke ciki dole ya katse kiran ya cigaba da tuqi Jaguwa ya shiga gida babu kowa a babban falonsa dan haka kai tsaye ya nufi dakinsa ya fad’a akan makeken gadonsa tare da dafe goshinsa da yayi wani irin rikewa ,ya kusan minti shabiyar kwance yana tunani sannan ya yunkura ya tashi ya shiga bathroom ya shiga zubawa kansa ruwa sai da yaji kan ya dan rage masa ciwo sannan ya fito jallabiya kawai ya zira tare da wucewa masjid .”

“Ranar yau anas jinsa yake dabam ,jinsa yake kamar an sake sauya shi, wani irin farinciki ke rasashi wanda ga duk wanda yasanshi yasa fuskarsa ta sake wadatuwa da farinciki fiyye da yadda fuskarsa take ,
itama hally haka nan ta tsinci kanta da farinciki dan yanzu ta maida damuwarsa nata haka farincikinsa ,
taja Karan hancinsa da take mugun so tana sakar masa murmushi ya janyota gabadaya ta zube aikinsa ya rungumeta tsam ya kai bakinsa cikin kunnenta yana sakar mata numfashi “matata yau ina cikin farinciki .”Ta juyo gbdy ta fuskancesa “naga alama nima ina tayaka farinciki amman meye abinda yasakaka farinciki haka “? murmushi yayi mata yana sake rungumeta tsam yana bata labarin soyayyar yayanta da tanwer sai dai bai bayyana mata yadda soyayyar ta samo asali ba .Ta ware masa idanunta sosai tana cewa “to ya zaiyi da aunty haseera?yayi kissing din idanunta “zaki fara ko ?”me kuma nayi daga tambaya ?a duk sanda kika bude min wadan nan idanunki ina kwadaita dake my princess
bakiji yadda naji ajikina ba yanzu dana kalli cikinsu.” ya karashe maganar yana matseta ajikinsa har tana jin yadda jijiyarsa ke zungurinta .”

“Shikenan na daina amman fa akwai daru idan aunty haseera tasani ,tanwer tafita iya daru ai sai dai kawai idan taga damar barinta ko kuma ta duba dangantar dake tsakaninku “a ajiye wannan ammi fa tana matukar son yaya ya auri aunty hasera domin itace ta hada duk abinda ammi take so ga surukarta ya riko hannunta sosai cikin nashi yana murzawa cikin wani irin salo na shauki “fada min abinda ammi take so ga suruka? “tana son farar mace doguwa kyakkyawan mai shape ,me tarin Ilima addini dana boko ,me tsafta da iya girki uwa uba kula da miji ta karasa maganar tana rufe idanunta da tafukan hannuwanta duka alamun kunya .”
ya cire hannuwanta yana cewa “kalleni !.
Ta tsura masa narkakkun idanunta dake tada masa tsumin shaawarta “dan baki taba ganin tanwer bane ta hadu iya haduwa fiyye da tunaninki idan dan kyau ne da abubuwan da kika lissafa to auntynki hasera bazata tsaya a kusa daita ba iya girki ne kawai bani da tabbaci saboda ban ta’ba cin girkinta ba amman sauran abubuwan da kuka lissafa duk tana dashi “gsky zan so na ganta nice ma zan fara sheidawa
ammi “a’a ban yarda ba ki barshi yaje ya fad’a mata da bakinsa ya fada yana shafa saman dukiyar fulaninta dama kuma dibiarsa kenan muddin suna tare hannuwansa basa rabuwa da ta basu ,yana qaunarsu da hips dinta fiyye da komai ajikinta barin yanzu da lafiyayyen sex din da take samu ya qara fito dasu sosai .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button