KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

Bayan ya gamsu ya rungumota jikinsa yana bata hakuri bata ce masa komai ba dan numfashi ma da kyar take fitarwa da kanshi ya tashi ya dora mata ruwan zafi da safe ya kuma gyara mata shimfida data baci da jini ,sabata yayi ya shigar daita bathroom “bari nayi miki wanka tunda ,ta buga masa harara bai sake yin magana ba ya fice yana murmushi jiki babu Kwarai tayi wanka ta fito a daddafe haka tayi sallah ta fito falo bata iya aikata komai ba abinci daman tun safe ya kira yayi musu order Suka zauna akan dining table “bari na kirawo adnan yau dai yazo ya tayamu zaman gida ta wani maka mishi harara”saboda ka tona min asiri ?no no my princess am sorry gani nayi yau gidan babu walwala ta kawar da kanta cikin tsiwa “to kuma sai ka kira shi to yazo yayi mana me “?
“Aa nifa bana nufin komai kodan aikace aikecen gidan ya taya ni kinga fa yadda zanin gadon ya baci ke da haka zai fahimci kina yiwa mijinki biyayya ya fada yana mata dariyar tsokana cikin wasa ta dauki pillow din jikin kujera ta cilla masa kamar zatayi kuka yana dariya yace” ashe fa laifina ne yi hakuri matata ta hade fuska sannan taki cin abinci dake gabanta ba dan bata bukatarsa ba sai dan kunyar da take dawainiya daita “ai zaka sake dawo ne zaka ….”tayi shiru ta kasa karasa mgnrta yana dariya yace “zan dawo me “?ta hararrsa bansani ba “tunda baki sani ba bari na fita zuwa anjima na dawo tayi shiru ya mike ya shirya tsaf sannan yazo kusa daita tana zaune my princess na gode Kwarai da kulawarki gareni nayi alfahari da samunki a karo na farko na kara kuma zan cigaba dayi na godewa allah daya bani ke a matsayin matata halima kin zamo wata jigo acikin bargon jikina ina sonki halima soyayyar da ban san iyakarta ba na yarda soyayyarki ta shiga jinina inshaallahu mutuwa ce zata raba mu kalamansa sun faranta ranta haka nan taji kamar ta dawo dashi kar yafita zuwa koina tayi wani yalwataccen murmushi “yanzu kuma sai ina ?”zanje gurin yayanki akwai aikin da zamuyi dashi murmushi ta sake yi”sai kuma yaushe zaka dawo ?kema Kinsan bazan jima ba zan dawo dan allah kiyi min hadi irin na jiya tayi saurin tsuke fuska cikin rashin fahimta tunaninta ko abincin data girka masa jiya taga abincin ma bawani ci yayi ba sosai qirjinta na bugawa tace “hade me fa ?
Ya dan yi murmushi har “kin manta abinda ya samarwa mijinki farinciki ta bishi da harara alokacin ya fita kai tsaye gidan jaguwa ya nufa a lokacin garin ya canza alamun zaayi ruwa sai dai ruwan bai sauka ba sai iska mai dadi dake sauka yana ratsa sansar jiki a lambun gidan ya iske jaguwa da abokansa da yaransa ya mika masu hannu suma suka mika masa suka gaisa sannna ya samu guri ya zauna a kusa da amininsa yana cewa “ina   alhj Tahir din ku fito dashi ? ya fad’a yana duban yaransu daya daga cikinsu yayi saurin juyawa cikin haka wayar jaguwa ta soma ringing ya dauka yana dubawa tanwer ya gani dan haka ya dauka ya kara wayar a kunne batare da yace komai ba har sanda aka karaso da alhj tahir gabansa waya na manne a kunnensa ya d’aura kafafunsa akan wata kujera yana girgiza kafafunsa yana sauke ajiyar zuciya yana duban Alhj Tahir  wanda gbdy ya fita haiyacinsa ya tara gemu mai yawa yayi wata irin katuwar rama   sai faman zare Ido yake .

Tanwer ta busa masa iskar bakinta acikin kunnensa wani irin yar yar yaji ajikinsa “adnan baka kyauta min , me kuma nayi sarkin complain ? “Complain din me nayi kuma yanzu byn kana bani wahala baka nemana idan bani ce na nemeka ba , kusan kwana uku kenan ina nemanka a waya bana samunka “Ya lumshe rikitattun idanunshi “aiki ne wallahi .
“I love you adnan and I miss you You are so precious to me “Nima ina sonki tanwer ya fad’a a kasan ranshi “Ina son nayi maka wani albishiri “meye albishiri din fad’a min naji ?”dady  yace ka turo magabantaka ya bud’e idanusnhi dake lumshe ya zubawa yatsun hannunsa  Ido Kawai yana kallonsu batare da yace uffan ba “Kayi shiru  ?
ya numfasa  yace “ban son zolaya fa, anas yayi masa alama da alhj Tahir dake durkushe gabansa da hannu shima yayi masa alamar yayi komai kawai yana waya .
tanweer ta  ware idanunta kmr tana gabansa tace  “kana nufin baka yarda da mgnta  ba ? gsky ban yarda ba ta yaya mahaifinki zai yarda ki auri mutun Irina yasan koni waye a garin nan fa “? sau nawa zan fad’a maka ka daina fadar haka nice fa zan zauna da kai Kuma nasan zaka canza da izinin Allah Kuma wallahi sun amince da gaske nake fada maka bada wasa ba .”
jaguwa ya sake gyara zama  da wayar hannunsa yana murmushin Jin dadi anas ya juyo a lokacin daya d’aura bakin bindiga akan alhj tahir yana masa gargadi girgiza Kai kawai yayi yana ciza lip’s dinsa na kasa shi Kuwa jaguwa ko ajikinsa hankalinsa kacokan yana gurin tanweer shi kadai yasan sanyin da yake ji a sansar jikinsa adalilin jin sautinta sai ma yake ganin tamka tana gabansa yayi missing din komai nata yana jin kamar tana bisa qirjinsa ne a hankali ya fara shafa faffadan qirjinsa “adnan dina!“Yes tanwer ina tsananin qaunarka burina akoda yaushe mu kasance tare matsayin miji da mata murmushi kawai yayi batare da yace komai ba a ransa yace lokacin baki amsar tayi tanwer dan ni kaina ina ganin lokaci yayi da zan ajiye iyali kuma ba kowa bace face my tanwer.”
A hankalin ruwa ya soma sauka gbdy suka koma cikin wasu lema kamar yadda jaguwa yake ciki suka cigaba da sauraron anas.”

“Alhji tahir me ya hadaka da nazifi kake neman rayuwarsa ?”wata mummunar fad’uwar gaba ta ziyarcesa tsoro da fargaba suka mamayesa baya raba dayan biyu a hannunsu nazifi ya fad’a  tunda kuwa ya fad’a hannunsu shikenan ya shiga uku tashi ta samesa yayinda Nazifi ya tsira daga mutuwa, duk da kasanceearsu yan fashi amman  su din masu gaskiya ne da rashin son zalinci ko danne hakin wani uwa uba alkawari zakuyi aiki dasu lafiya batare da wata matsala ba .

kimanin minti uku anas na saurarensa yaji me zai ce amman shiru  yayinda jaguwa ke sake nitso cikin hira da tanweer hannunsa ya kai ya daga wajen lemar da suke zaune ciki yana wasa da ruwa fuskarsa kwance da murmushin Jin dadi kana ganinsa zaka fahimci yayi nitso cikin tafkin soyayya
Anas ya cigaba da mgn “me yasa sai ka shiga abinda babu ruwanka ?”  alhj Tahir yayi shiru yana sake shiga tashin hankali “ka dauka   kai  kad’ai kake  da karfi acikin garin nan ?” yayi mgn idanunshi akansa yana jin babu dadi a ransa “ko da yake   kai fa mugun  mai laifi ne sannan ,da kake sawa abi  yaron mutane dan daukar maka rayuwarsa   idan komai ya kwabe kafin yashafemu ta kanka zai fara , kabi  ka ta kurawa yaro,yaron nan ma a maganarsa matsayin mahaifi kake dashi agurinsa  ,kai dai wallahi mugu ne gbdy halaiyanka marasa kyau ne , wai hatta dan cikinka baka bari  ba ,gsky kai din azzalumi   ne  ,dan iskanci  shine kake amfani da damar da kake dashi kake damun mutane Idan har baka cire hannunka akan niyyarka ta son ganin baya nazifi  ba  wallahi matsaloli  zasu faru amman  matsalar kai kadai zata shafa dan mu yanzu mun rigada muyi karfin da babu Wani wanda ya Isa “. ya karasa mgnr tare da bawa sky umarmin ya zo da nazifi adaidai lokacin da jaguwa ya watso ruwa bai sauka a fuska sai a fuskar Ana’s ya waiga ya kallesa yana girgiza Kai  ko cikakken minti goma ba’a yi ba suka dawo tare nazifi  kallon kallo  suka shiga yiwa juna daga nazifi har alhj tahir .”
gbdy alhj tahir ya rasa inda zai saka Kansa dan kunya yayi bakinciki da wannan rana “ka kula da kyau ka dauki maganarmu da mahimmanci babu Kai babu shi kowa yayi harkar gabansa idan ka ….”shiru yayi batare daya k’arasa maganarsa ba sakamakon ruwan da jaguwa ya sake watso masa ya waigo ya sake kallonsa gbdy ya fahimci hankalinsa bai garesu  ana ma kawai   ya yarda  yana  son tanweer ,soyayyar ma  bazata   misaltatu  ba gbdy daga anas har su Kamal da jubi da sauransu kallon jaguwa suke ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button