KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

*
bangaren  Zahra kuwa daren ranar   kasa bacci tayi  tana  zaune cikin tsananin tashin hankalin data tsinci kanta dan gbdy ta kasa runtsawa data runtse idanunta da zumar bacci jaguwa take gani tare da yarinyar da bata san ko sunanta ba , daf da asuba  bacci ya  fixgeta a matukar  firgice  ta farka ta  zauna  tana haki , jikinta ya d’auki zafi kmr garwashin  wuta  tsinuwa kuwa  ta  tsinewa yarinyar  yafi sai babu adadi  daga  karshe ta rushe  da  matsanacin  kuka “wayyohhhly  Allah   naci amanar  kaina ,  na yaudari  kaina dana d’auki  soyayyar duniya na daura ma Adnan  kuka  take sosai har da shesheka, bazan taba barinka haka ba sai na tabbatar da na kawar da hankalin  kowace mace akanka tsam ta sauko daga kan katifa ta jingina jikinta da bangon d’akin ta runtse idanunta masu zubar da zafafan hawaye masu zafin gaske tana Neman mafuta.
wata zuciyar na bata shawarar ta hakura dashi  yayinda wata zuciyar ke karfafa mata gwiwar  tabi kowace hanya dan ta mallaki jaguwa  sosai tayi zurfi cikin tsananin tunani da tashin hankali  ,babu wacce tazo mata sai  kawarta   blessing da suka had’u  a shurem  blessing yar asalin edo state  ce akwai shakuwa mai karfi a tsakaninsu blessing ta sha bata shawara ta dinga binta zuwa garinsu idan zata domin ta had’ata da manyan bokaye  dan ta qara samun d’aukaka a harka karuwanci amman taki naunayen ajiyar zuciya ta sauke na samun mafuta dan kuwa tasan blessing zata taimaka mata tun da asuban  fari  ta  kirata tana kuka ta sheida mata halin da take ciki  take blessing  tace  “ki  shirya kawai  ki zo muje garinmu na gode blessing ai muddin kika min wannan taimakon bazan taba mantawa dake ba  “karki damu zahra ai wannan ba wani abu  bane amman Ina tabbatar miki muddin na Kai ki gurin malamai sai yadda kikayi da  jaguwa  sai ya zamo tamkar  bawanki  “na gode na gode “,Kai haba Zahra ai mun zama daya tuntuni kece dai baki d’auki hakan ba ki shirya mu hadu a iyanapaja  dan  Ina royal  stream  hotel nan kwana zan k’arasa na siya mana ticket kafin kizo “okay sai nazo  cikin saurin ta soma shirinta  tana jin sanyi da natsuwar zuciya.”

Mika  jaguwa yayi  had’e da salati Ya  sake  kwakumeta tsam  ajikinsa yana sauke  numfashi a hankali kmr bazai bud’e Idanunsa ba amman dole ya bud’e sakamakon wayarsa dake Kiran sallah alamun lokacin sallah  yayi  ya bud’e tsumammamun idanunshi ya kunna wutar d’akin wanda yasa ta d’an motsa tana shigewa jikinsa hade da d’aura hannunta akan chest Kuma daidai nipples dinsa sauri d’auke numfashi yayi gabansa na faduwa  yayi shiru na tsawon lokaci yana tunaninta abubuwa dayawa akan yarinyar ya d’an dade kwance idanunshi biyu sannan ya  cire hannunta a chest dinsa ya sauko a natse ya karasa Inda wayoyinsa suke ya d’auki daya yana dubawa karfe bakwai saura na safe bai so  wannan lokacin ya taddashi a hotel din ba shi daya so tun asuban fari ya bar hotel din Kai tsaye bayi ya shiga ya fara da sakarwa jikinsa ruwa sannan ya dauro alwala ya fito ya saka kayansa ya Kalli gabas ya tadda sallah byn ya idar ya mike ya Isa Inda take kwance ya Kai hannuwansa tsakiyar kafafunta yana shafawa a hankali ta bud’e idanunta sakamakon jin damshin ruwan hannunsa na ratsata idanunshi cikin nata yace “tashi kiyi sallah lokaci na tafiya ta janyo bargo ta lullu’be jikinta sosai dan babu komai ajikinta  muryarta can kasa tace “okay  ka  miko min  towel na d’aura “Dan Allah malama  ki  tashi kije dauka karki bata min lokaci  ya k’arasa maganar a fusace  shagwabe fuska tayi kmr zatayi kuka  “babu komai ajikina fa tsaki yaja ya mike ya janyo towel ajikin kofar bayi ya jefa mata  a fuska  ta d’aura ta   soma k’okarin  saukowa  “kiyi sauri please Ina da appointment ya fad’a kwayar idanunshi na kanta  bata ce Komai ba ta nufi bayi yabi bayanta da kallo yana kallon every step of her komai nata dabam  ne ta had’u sosai ilarta dai rashin kunya har ta  shige bayi idanunshi na kanta  itama sai data yi wanka sannan ta dauro alwala ta fito a lokaci da yake waya da anas “karka damu ku bani minti ashirin yanzu zaku gani murmushi yayi yace “Kai anas me yasa ka fiyye damun kanka nace maka ba abinda kake tunani bane  shikenan koma dai menene ba abinda kake zato  bane  ya katse Kiran ya kira ammina Inda yake sheida mata Yana da aiki me mahimmancin da zashi shi da abokan aikinsa yana bukatar adduarta”Allah ya tsareku yasa ayi aiki cikin nasara amman dan Allah kabi a hankali kasan Kai ne rayuwarmu sannan  da zarar ka kammala da komai kazo
naganka karka ce sai karshen sati zaka zo gbdy “karki damu ammi inshallahu bazan Kai ba me zan taho Miki dashi ?”.Shiru tayi  tana tunanin kafin daga baya tace “komai ka kawo amminka zatayi farinciki murmushi yayi yace “shikenan my happiness murmushi tayi daga bangarenta ta sake Aiko masa da addua komai dare idan na dawo zan kiraki karki yi bacci har sai Kinga kirana kinji ammina  tace “to Adnan inshallahu zan jira kiranka   sun d’auki  minti biyar suna waya har da kannensa ,sanda tanweer ta kammala shirinta taja ta tsaya tana kare masa kallon tsab  yana matukar burgeta yadda bai wasa da lamarin mahaifiyarsa  da kannensa a dan zamanta dashi ta fahimci yadda yake mugu mugun son mahaifiyarsa har sanda ya k’araso gareta ya riko tsintsiyar hannunta tana can duniyar tunani   kumatunta ya ja kadan tayi firgib  ta dawo natsuwarta tana sauke ajiyar zuciya  tsurawa juna idanu sukayi batare data ce masa komai ba
ya  nufi hanyar  fitowa daga d’akin daita tana  biye  dashi .”

Yana  fitowa haraban hotel din idanunshi suka ci karo da motar alqali  murfin motar a bude  wasu mutane na tsaye suna duba cikin motar ,sai lokacin ya tuna da yasa a tsare masa shi ,Kai  tsaye gurin motarsa ya nufa ya bude wa  tanweer gaban mota ta shiga  ta zauna ya rufe ya zagaya ya shiga bangaren direba ya shiga ya zauna ya tadda motar yana fitowa ya sawa motar wuta kamar Wanda zai tashi sama “kabi a hankali please  Ina matukar son rayuwata  domin  tana da matukar mahimmanci ga iyaye saboda nice duniyarsu  “Ina  da mahaifiya da kanne day day har guda uku  mafi soyuwa a zuciyata bazan so suyi  maraicina ba bare ki fada min  maganar banza yayi mgnr a tsawace yana dukan stearing motar shiru tayi tana zance zuci kafin daga bisani ta motsa  labbanta  a hankali  “kana son mahaifiyarka  da kannenka   sosai  ?” tayi maganar tana kallonsa da gefen Ido da kmr bazai yi mgn ba sai dai mahimmancin su ya wuce ya banzatar da  amsar  dan haka yace “kwarai  kuwa  ina matukar son mahaifiyata  da kannena  so na  gaskiya  son da bana Jin akwai wani mahalikin da yake wa ahlinsa “Amman shi ….”  maid your thought   karki  sake  furta komai akan  ahlina  ya fad’a yana  cigaba da murza stearing ,dole taja bakinta tayi shiru “.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button