KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

ruwa kawai ya sha dan bai Jin cin komai ammi tace “lafiya dai Ko ya aiki da abokan aikin naka suke ?”duk Suna lafiya sunce agisheki tace sannuku Ai kuna k’okari wannan aikin naku bakwa samu lokacin kanku gashi duk ka rame Ina fatan dai lafiya kake ?” ya gyada alamun “eh .
Tunda ya shigo gida hasera ta d’aura idanunta akanshi taji hankalinta ya sake tashi akanshi , taji komai ya sake tsaya mata, duk yadda take hasashen girmansa da haibansa da kyawunsa abun ya zarta tunaninta ita kuwa wacce irin dace tayi arayuwarta samun kyakkyawan miji ,suruka mai kyau da nagarta, dangin miji masu qaunarta wannan ma kawai sun isheta , zata zama matarsa acikin yan watani masu zuwa , am very lucky burina zai cika na samu cikar burinna tayi mgnr a kasan ranta.
irin mijin da take so shine agabanta idan Allah ya taimaketa haihuwar fari ta haifo masa da nmj mai kama dashi sak ita kuwa me zatacewa ubangiji ta ?”
Sai faman safa da marwa take tana satar kallonsa shi kuwa duk yana lura da duk zariyarta amman Ko ajikinsa duk yadda ya kai ga qaunar ubanta baya jin zai Iya rungumar qaddarar aurenta yana qaunar mahaifinta domin ya taka rawar gani arayuwarsa ta baya amman ya rasa dalilin da yaji bai qaunar yarinyar da babu abinda ta bari na mahaifinta .
shiru yayi sannan yaki cin abincin daaka kawo masa sai da ammi takurasa sannan ya gauguta cin abincin domin gaf ake da Kiran sallah magriba yana kammalawa lokaci yay ya mike ” bari naje nayi sallah na dawo “. to a dawo lfy Allah tsare inji cewar ammi .

Bayan ya idar da Sallah kai tsaye gidan ya dawo a inda ya fita ya bar ammi anan ya dawo ya sameta akan daddumar sallah babu Kowa ya sake durkuahewa agabanta dan ya fahimci akwai magana abakinta zama ammi ta gyara sannan ta maida dubanta ga jaguwa ta Kira sunansa har sau uku “Adnan !!!!
ya d’ago a hankali ya tsura mata Ido yana dubanta kamar wata sabuwar halitta a gabansa sannan ya amsa da “na’am ammi nah “.
“Adnan ta Kara kiran sunansa a hankali ya tsura mata rikitattun idanunshi yana sauraronta “ga hasera nan yaruwarka diyar kanin mahaifinka uwa daya uba daya ,hasera yarinyar kirice mai tarbiya Kamar yadda kasani nima kuma na yaba daita dari bisa dari da kaje ka auro min wacce ban san halinta ba gara ka aureta .

“nasan kai yaro ne mai biyayya ba zakaki abinda nake so ba hasera nake so ka aura bisa umarnina takarsa maganar tana numfasawa .
numfashi ya sauke sannan ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa gbdy sai yaji bazai iya kin bin umarninta ba kawai ya tsinci kanshi da cewa “ammina na amince zan aureta tunda kin amince daita nima amince ya karasa magana a raunace cike da tashin hankali “alhamdulillahi Allah yayiwa rayuwarka albarka daman nasan bazaka bani kunya ba yadda kake min biyayya Allah yasa yaranka suyi maka .
“Ameen ya furta a can kasan makoshi zuciyarsa na masa zafi da tuttukin bakinciki .

hasera dake safa da marwa ta kwasa da gudu ta shige daki tayi wani irin tsalle ta fada saman katifa tana fidda numfashi da kyar , wani irin haushi yaji alokacin daya ga ta kwasa da gudu kamr wata mahaukaciya “wacce irin mace ce ita sam babu alkunya bare Kamun kai ?” yayita jan tsaki a ransa sun dauki lokaci yana tare da mahaifiyarsa a karshe ta Kira masa hasera su fahimci juna ita kuma ta tashi ta barmusu falon.
tunda ta zauna ta kasa kwakwaran motsi tamkar babu ita agurin a fusace ya kalleta zaune a gabansa ta kafeshi da Ido kmr zata cinyesa abinda yafi tsana daga mace Kenan kallo yace “ki dauke idanunki akaina sannan ki bar ruhinki ya Samu salama duk kin Wani hana kanki sukuni akaina sai Wani Jin dadi kike zaki auri mutumin da baki san kowayeshi ba “.murmshin jin dadi ta saki tana cewa “ni kuwa nasani kowaye Shi ,kai fa mutumin kirkine waje da gida Kowa yana alfahari da kai ,ni dai tunda ka amince zaka aureni na gode maka ta k’arasa maganar tana murmushin jin dadi .

“ya subhallah”!.
Ya furta a kasan ransa ” yanzu irin matar da amminsa ta zaba masa Kenan babu Kan gado, babu alkunya ina tarbiyar da tace tana dashi ?”numfashi ya fesar yana dubanta kasa Kasa , shi kallon tababbiya ma yake mata sannan wawiya wawiya shasha Kamar wacce aka kwantota daga gidan mahaukata ba wai mai tarbiya ba .
tunda ya shigo gidan take bud’e hakora har zuwa yanzu da take gabansa ta kasa control din Kanta.
ta sake bude baki da zumar sake yin mgn yace”yi min shiru anan banza shasha kawai sai wani bare baki kike “.tsit tayi kmr ruwa ya cinyeta .Falon ya dauki shiru har kusan minti talatin sannan ya sake bude bakinsa da kyar ya cigaba da mgn amman a tsawace “kin yarda zaki aureni ?”ta gyada masa Kamar zatayi kuka tare da shagwabe fuska “.
“Ina da wata mummunar dabi’a da babu wanda ya sani daita daga Allah sai abokan alqalta, Adnan da kike burin aure mashayi ne, sannan ma nemin mata ne kuma yana da mummunar sanar da nan gaba Ko a yanzu zai iya shiga hannun hukuma kuma su rikeshi riko na har abada kin yarda zaki auresa da dabiyarsa ?”
jikinta yayi sanyi jin da bakinsa ya furta abinda yake aikatawa amman ita tana sonshi Ko a Yaya yake ,shi take so ba dabiarsa ba ,ita dai tunda zai aureta ai shikenan , muryarta a hankali ta fito “na amince zan aureka saboda ina sonka, zan zauna da kai a duk yadda kake ,Allah kuma baxaisa kashiga Hannun hukuma ba inshaallahu zaka daina duk abunda ka lisafa kana……”
dogon tsakin da yaja yasa ta katse maganarta ya mike a fusace ya fice daga gidan batare da yayiwa ammin sallama ba .”
Ransa abace ya shigo gidan ya cire rigarsa yayi filinging dashi ya zauna akan kujera gbdy friend’s dinsa suka zagayesa suna tambayarsa “bai ce musu komai ba illa tsakin da yake ja akai akai gbdy gankalinsu yayi marukar tashin a karshe ya Tashi ya shige daki ya kulle kansa ya wiwi ya kunna ya fara zuga yana fitar da hayaki ta hancinsa zuciyarsa banda tafarfasa babu abinda take . “


alhj Tahir bai farka daga naunayyen baccinsa ba sai washegari da yamma , gbdy ilahirin jikinsa ya mutu da kyar yay mika haka zalika da kyar ya daddage ya mike zaune yana duban d’akin da yake jin yana jujjuya masa ,tunani ya shiga yi akan naunayyen baccinsa . yayi tunanin duniya akan baccinsa bai gano dalilin baccin ba shida baccin dare ma ba kasafai yake yinsa ba bare na safe har ya kai yamma da kyar ya Tashi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya rama salolinsa sannan ya nufi bangaren hajiya baseera yana tafiya qirjinsa na bugawa da karfin gaske wanda ya rasa faruwar haka.
cikin Wani irin Taku na sanyi jiki ya karasa shiga part din da masu aikinta ya fara Cin Karo suna kai Kawo bazakace matar gidan bata nan ba kodayake suma a tunaninsu fita tayi kuma zata dawo .
A hankali ya Samu guri ya zauna yana cigaba jin faduwar gaba ,ya kusan minti talatin bai ji motsinta ba dan haka ya mike ya shiga part dinta cike da tashin hankali yake bin d’akin da kallo Kamar ranar ya fara shigowa koina a hargitse nan take gabansa ya cigaba da bugawar da yake , zuciyar ta kaiwa kwaluwarsa sakon daya firgitashi cikin tsananin tashin hankali ya karasa bakin kofar bayi ya kwankwasa Ko tanayi wa Ibrahim wanka ne, sai dai still shiru ya Kira sunanta da karfi sannan a firgice ya tura kofar bayi wayam babu Kowa da mugun gudu ta fito Kamar Wani zautacce ya isa bakin get yana kwallawa mai gadi Kira “sabitu ! sabitu!!! Zuciyarsa na sake shiga garari “tun yaushe matar gidan nan ta fita ?”shiru yayi yana kallonsa yana tunanin amsar da zai bashi Kar ya fadi abinda zai jawo masa matsala da aikinsa bai ankara ba yaji sauka mari daga yatsun alhji Tahir “dan ubanka tunani na tambayeka Ko inda matata da dana sukaje ?
“a gigice mai gadi ya rike kuncinsa inda alhj Tahir ya zabga masa mari yana cewa “nidai tun jiya hjy ta fita amman ita kad’ai “ita kad’ai fa kace?
“da idanuna naganta ita kadai ta fita gama direban can ka tambayesa ita kad’ai ta fita acikin jar mota .
babu wanda ya shigo gidan nan cikin kawayenta Ko yanuwanta ?”ya sake masa tambayr a rude “gsky babu wanda yashigo bayan naxifi shine Kawai ya shigo bayan wani lokaci ya fita sannan itama ta fita sake tambayarsa yayi ka tabbatar da naxifi ne kawai yashigo gidan nan sannan ta fita?”
mai gadi yayi saurin gyada masa kai nan take ya juya Kamar zai Kifa ya nufi part dinsa ya soma bincike hatta camerorin gidan an tsadasu sun daina aiki bare yaga wainar daaka toya .
wani gumi ya shiga tsatsafo masa hankalinsa yayi mugun mugun tashi wayarsa ya d’auka ya shiga neman layin naxifi kira daya ya dauka cike da ladabi da biyayya ” barka da yamma dady?” Ina ka kai min matata da dana ?Tambayar da ya soma yi masa Kenan cikin tsananin tashin hankali naxifi yace “dady bangane nufinka ba ?”Ni rabona dasu tun jiya danazo duba jikin Ibrahim “Kaci nalafar ubanka da tun jiya rabonka dasu, kun kashe min camerorin gida dan kusamu damar aiwatar da nufinku ba to wallahi Kaji na rantse kwana biyu kawai na baka ka dawo min dasu ingansu agidana suna shawagi idan ba haka ba wallahi ka kuka da kanka dan sai na aikaka lahira byn nasa an daddatsa kai yana gama fadar haka ya kashe Kiran yana huci .
take gumi yashiga karyowa naxifi ta koina ajikinsa tsoro da matsanancin fargaba suka mamayesa , yasan ya tarowa kansa March dan alhji Tahir zai Iya aikata abinda ya fada mutumin da bai bar dan ckinsa ba to wazai Bari?”da sauri ya Shiga tattara kayan aikinsa ya fito cikin sauri kunnensa manne da waya ….”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button