KUSKUREN BAYA

KUSKUREN BAYA 1 TO 48

xagi ba kalar da tanweer  bata musu  ba da hausa da turanci Amman Babu Wanda ya kulata haushi ya isheta ta bar gurin mota ta nufi bakin get nan ma babu hali dan me gadi yaki bude mata get duk Inda tasan zata bi ta fita daga gidan babu hali ta shiga maseefa tana cewa ” sai na bar gidan Kuma Babu wanda ya Isa ya hanani fita idan na bar gidan sai na sa ankamaku anyi muku hukunci me radadi,wallahi  da Kun San Koni wacece a garin nan da baku tsaya bin umarnin wannan ba Kun  hanani fita ba, ta juya ta Kalli Inda jaguwa yake tsaye jikin motarsa Idanunsa na kanta yana cigaba da kallon bakin tsiwa  “zan nuna muku ko ni wace acikin garin nan tare da juya masa baya.
“Kashi Amman na tausaya miki wannna shi ake kira da power less” juyowa tayi cikin fushi ta Kalli Inda yake idanunta ya sauka akanshi.
yana nan  tsaye sai dai zuwa wannan lokacin   ya harde  hannuwansa a qirji  yana mata murmushin mugunta fuuuu ta nufosa cikin tsananin  fushi da zuciya   tace “zan nuna maka wannnan power din kasa Ido ka gani”tayi  mgnr tana nunashi da yatsa  “me  zaki  iyayi ?ba abinda zaki iya yi min ,ki daina takama da wannan dan matsayin da mahaifinki yake dashi dan baki da wani power da zaki iya min koma” .

ba bata lokaci ta cukumi wuyansa “zaka ga abinda zanyi “.
Yaransa suka bishi da kallo haka ma abokansa me gadi kam saurin kawar idanunshi yayi kamar bai ga abinda ke faruwa ba  ran jaguwa yayi mugun ‘baci sai dai bai ce mata Komai ba har sanda ta hau fad’a da maseefa  da zaginsa da fada masa bakaken maganganun ,sai da tayi mai isarta sannan ta  sakar masa wuya ta dukurshe ta zube kasa ta  runtse idanunta  wasu hawaye masu zafi suka zubo mata .
shi kuwa ya matsa gefenta ya tsura mata Ido ransa na quna kafin daga baya ya canza kallon zuwa natsana yayi taku biyu zuwa Inda take durkushe  dafe da goshinta “sorry tanweer bazaki iya komai ba sai da kiyita ihu kina kuka kina zagina
just like a baby ,the great tanweer, kyakkyawar matashiya mai ji da
kudi  yanzu ta zamo abar tausayi  agidan nan , gidan nan fa  ba yadda kike tunani bane dan ba  haka kawai yake ba ko mahaifinki da karfin masu karfin garin nan zasu zo  basu Isa su shigo ba, Ina tabbatar miki muddin kika bar gidan to nine na fitar dake amman rashin kunyarki da ihunki bazasu fitar dake ba cikin sauki ba  .”

wani mugun kallo take masa tabbas da zata samu bindiga a halin yanzu  da zata hakura da son da take masa
ta harbesa ta huta, hakan ne  ma zai zame mata sauki a rayuwarta dan tasan muddin bai duniya zata hakura dashi , “amman bari na gwada miki karfina ai kina son fita ko?tayi shiru taki cewa komai sai hawaye dake zuba “Ammar  bude mata get tuni
taga get ya bude “how dare you? ta fada tare da k’arasawa gurin me gadi ta d’aukeshi da mari “Kai har ka Isa na maka mgn Kaki bin umarnina  kasan kuwa waye ubana a garin nan?  “ubana shine minister of health na garin nan waye shi wannan daya ajiyeku ban da tantiri   ?jaguwa ya matso gabanta ya mika mata roban ruwan faro me sanyi  “,Sha ruwa sanyi  tanweer  kiyi aiki da kwakwaluwa ” me yasa mahaifinki zai d’auki mataki akansu ?”anan basu san kowa ba sai  sani , babu dokar kowa da zai yi aiki sai nawa ,gidan nan gidana ne mahaifinki bashi da wani matsayin bashi da power haka kema , shi wannan matsayin ko power  din ki bari sai kin koma gidanku dan anan babu Wanda zaiyi respect dinki babu Wanda zai ga girmanki  sannan babu Wanda zai bi umarninki sai nawa , nawa  za’a bi   kin san me yasa ?Yayi kusa kusa daita “kowa yasan matsayina, dan fashi ne  dake sata wa kasa da kasa the CEO of  armrobber’s, armrobber’s din daya yi suna da girma a fad’in Africa gbdya kowa yasan jaguwa wato Adnan amad gwoza  anan wa yasan matsayin tanweer har ta bada umarni abi har ta kafa doka abi a zauna ?ke ba kowa bace sai diyar common minister of health da iya garin nan da wasu tsirarun garuruwa  akansansa
sannan mutumin dake zaman banza
a offishinsa da suna yana aiki wa alumma mutumin da  maci   amana kasar ne  , bai San komai ba sai shaye shaye da  neman matan banza da bata rayuwar mutune  wannan shine cikakken  halin mahaifinki da kike takama dashi ,bari kiji da zai fito da boyayyen  halinsa fili babu mutun d’aya da zai ga girmansa  hatta ke kanki sai kin tsaneshi ,wallahi idan baki yi amfani da tunaninki kin kiyayeni ba kin daina  zagina ba zan nuna miki asalin waye jaguwa, zan fito miki da true colour dina, zan yaga miki rashin mutunci ,zan mayar dake baiwa a gidan amadadin bautar da nake miki  , sannan ki zamo daya daga cikin karuwaina nayi duk yadda nake so dake idan bukatata taso nayi ko sau nawa nake so yana gama fad’ar haka ya juya   abunsa .”
ran  tanweer yayi mata zafi ta dinga Jin zuciyarta kamar wuta magangunsa suka tsaya mata arai ta kasa motsi, ta bishi da Ido  kawai
tana kallonsa  ,lokaci  na farko kenan da’aka  fad’a  mata bakaken maganganun da suka daga mata hankali Km akan masoyinta data fi qauna akan komai,sosai  taji mgnr sun tokare mata zuciya Kuma ta kasa Koda motsi balle ta bud’e baki ta zagesa ko ta fad’a masa bakar mgn. shiru tayi tana mamakin abinda ya fad’a akan mahaifinta karyata hakan zuciyarta tayi sai dai Kuma ta rasa dalilin da zuciyarta ke wasi wasi akan maganarsa .”

Shi kanshi jaguwa yayi mamakinta Yana jiran yaji ta balbalesa da masifa da balai akan furuncinsa sai yaji shiru don haka byn ya dan yi nisa kad’an sai ya juyo yaga me takeyi, har yanzu tana zaune tana kallonsa yaga wani bacin rai atattare daita wanda bai ta’ba gani ba tayi sanyi sosai bazai iya karantar meye a kwakwaluwarta ba tuni yaji hankalinsa yayi matukar tashi Anya bai fadi magana dayawa ba kuwa  akan dad dinta ? “Shi kansa yasan ya fadi abinda bai dace ya fad’a ba , jikinsa ne yayi sanyi ya Isa d’akinsa yana tunani   hankalinsa ya tashi dan arayuwarsa baya qaunar ya batawa wani bare ita da yake jin duk saukar numfashinsa yana sauka da tunaninta ne ,yadda yaga yanayinta yasan ya ta’ba zuciyarta” me yasa na fadi abinda na fada “karka damu is a very good respond to her akan furucin bakinta km ya kamata   tasan kadan daga cikin halin mahaifinta .
” amman Kuma karya zamo da gaske zata shirya daukar fansa akanka ? tsaki yaja dan me zakaji tsoro ko ka manta ko kai waye ? Yayi shiru na dan tsawon lokaci sannan yace “babu abinda zata iya  ya kwanta akan kujerar kushin ya janyo pillow kujerar ya rungume a qirjinsa yace”tanweer you can’t do anything coz na zamo wani bangare na rayuwarki .”

Tanweer  ta koma d’akinta ta kwanta lamo akan kayan da tayi kaca kaca dashi  sai dai tsabar zafin zuciya ta jima tana tunani wani lokaci hawaye ya zubo mata ta tsinci kanta cikin kewa ta dinga Jin kamar bata da kowa da komai a duniya a tattare daita haka ta yini kwance agurin ta Kulla wannan ta kwance har dare jaguwa yasa aka yi order abinci kala kala wanda yasan take so, ya nufo d’akinta Yana  bud’ewa yaga wani duhu ya kunna wutar d’akin ya sameta kwance cikin yanayi mai ban tausayi ya matsa gareta ya tabata “tanweer “!
ya kira sunanta ai kamar wanda ya dana mata shoking din wuta tayi saurin  mikewa  ta buge masa hannunsa “ka kyaleni ka rabu dani kaji dadi burinka ya cika kasani cikin wani hali ,ka rabani da kowa nawa,kasani cikin damuwa  hawaye ya zubo mata “ka rabani da masoyina ka rabani da dady ka rabani da komai hatta matsayina da mutuncina ka rabani dashi kana Jin wai Kai wani
ne  shiyasa ka dauki kanka a wata  tsiya to bari na fad’a maka sai dai idan ban bar gidan nan a raye ba amman wallahi sai na ……” shiiiiii ki Daina wahalar da kanki coz you can’t do anything  “.
  dukkaninsu sukayi shiru suna kallon juna a zahirin gsky  bai so ya fad’a mata abinda ya fad’a ba amman tunda ya fad’a babu abinda zai goge hakan, muryarsa can kasa yace”ga abinci kici ki km  huce  dan nasan baki ne babu abinda zaki iya yi ya mike ya juya yana cewa “ki tabbatar kin gyara d’akin ko ki  kwana cikin datti “.  kifi abincin tayi a kasa “baza’a ci abinci ba, gbdy ta zubar dashi tabisa  da fad’a da tsawa bai kulata ba ya wuce ya tafi a wannan daren dukkaninsu babu  wanda ya runtsa kowa da abinda ke ranshi ke sakawa  jaguwa  da bacci ya gagara ya tashi ya shiga d’akin anas kusan kwana sukayi suna Hira sai dai bai yarda ya Sako mgnr tanweer ba yayinda Zahra tayita Kiran wayarsa bai  d’auka ba , wannan abu yayi mugu mugun d’aga hankalin zahra ta kwana da matsanacin fushi da bacin rai a zuciyarta  da sake d’aukar burikan mugunta  akan tanweer haka ma washegari bata hakura ba tayita kiransa bai d’auka ba shi kuwa duk kiranta  yana gani   amman yaki d’auka  dan bai ga abinda zaiyi da kiranta ba ya cigaba da harkokin gabansa .”
A daidai wannan lokacin kuwa Zahra na can cikin tsananin tashin hankali tsaye cikin bakake kaya kunneta manne da waya  cikin yanayi na tashin hankali take waya da blessing  “matsalata daya yanzu arayuwa shine Adnan .”
“Na fada miki zaki samu Adnan zaki auresa ta kowani hali duk Wanda zai shiga tsakaninki dashi karshensa mutuwa ,mutuwace makomarsa dan haka ki kwantar da hankalinki mu gama da next target dinmu ki natsu karki rusa mana plan idan aikin boka yaki akwai makirci bare zai ci zan sake kaiki wani guri Ina tabbatar miki  duk abinda yake takama dashi da asiri baya cinsa sai mun rusa, mun ruguza komai nashi yaji baya qaunar ganin kowa sai ke .”
“Shine abinda nafi qauna blessing ya zo da kanshi ko bai rokoeni soyayya ba ni dai yazo blessing  bazan iya rayuwa babu Adnan ba “ki daina kaskanrar da kanki  kina da komai da duk wani cikakken nmj zai soki akanshi kece kika fi dacewa da cancata dashi ba wacan  tsinanniyar yarinyar ba, ya soki ya qaunaceki amman saboda rashin hankali da tunani me kyau irin nasa  ya rasa Inda zai ajiye soyayyarsa sai gurin….” “excuse me  blessing don’t ever call him mad  karki sake zaginsa idan kina cewa bashi da hankali da tunani ni Kuma da nake so  shi fa ?don’t don’t try to insult him “am sorry kit  Zahra ta katse Kiran batare da ta jira taji me blassing  zata sake cewa ba .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192Next page

Leave a Reply

Back to top button